chapter 31

228 40 5
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

31👯
Matso da cameran wayar shi yayi daidai fuskar ta Yana dariya yace "kici a hankali Mana sister, abincin ba guduwa zaiyi ba idan ma ya qare zan saka a qaro Miki wani kiyi ta dirka"

Tsayawa da cin abincin tayi ta dago tana kallon shi
"Meye haka ya Sa'ood? Yaya zaka dinga shooting dina Ina cin abinci"

" Because you are eating like a horse, hakan kuma ya dace dake kina wasu abubuwan kamar Mai tabin hankali Amman daga baya kizo kinayi wa mutane iyayi"

" Koma Yaya ne Kai ka jawo, gashi saboda Kai tun safiya ni ba azumi nakeyi ba Amman babu abinda naci"

" Wannan kuma laifin ki ne saboda rashin hankali da na sauqe ki a hanya sai ki tafi wani wurin?"

" To Yaya kake so nayi?"

" Ki nemi abin Hawa ki koma gida mana! Raina ya baci ne a lokacin shiyasa nayi Miki haka"

" Na koma gida saboda ka qara Mara zuciya a Kan zagin mahaukaciya da Mara tarbiyya da kake min? Bani da wani wuri da zan Kira da gida Bayan inda na fito, ni ban Saba da rikici ba ko a gidan karuwai ba'a rikicin da kukeyi, I always have freedom sai abinda naso zanci sai abinda naso zan saka Kuma wurin da nayi niyya kawai nake zuwa babu wanda ya taba min dole da katsalandan cikin al'amura na bayan Kai, ka gama Isa ta inaso nayi nesaa dakai sosai ya Sa'ood I don't like you"

Shiru Sa'ood yayi Yana kallon Leesa gaba daya jikin shi yayi sanyi, baiyi tunanin akwai ranar da wata zata Budi Baki tace ta washe shi ba musamman ma daga cikin Sarwa, Yana tuna lokacin da suke jarirai Yana kula da su burin Shi bai wuce su Sami kusanci dashi kaman Yanda ya samu da mahaifiyar su ba, he loved and cherished the girls so much Amman bayi hango Koda shaquwa ne tsakanin su, ba'a maganar Saleeha ma don ko kallon shi na mintuna 5 Bata taba tsayawa tayi ba ko yaushe tana manne jikin Sa'eed,

Daukan tissue tayi ta goge hannun ta sannan ta koma cin abincin da spoon tana diban kadan_kadan tana ci a hankali, Bata qara yafi spoon biyar ba ta tashi tace su tafi ta qoshi, kallon plate din abincin yayi yaga da saita da yawa a Yanda ta fara ci yayi tunanin zata iya cinyewa har ta nemi qari,

"Baki Gama cin abincin kin ba fa Haleesa, ki zauna ki qarasa zan jira ki"

" No thanks, I'm full I don't want to continue eating like a horse"

Kallon ta yayi a kaikaice hade da lanqwasa murya yace "ke shirmammiya I was just joking, ki zauna Dan Allah ki qarasa cin abincin ki, I'm sorry Kinga ma zan goge videon"

" Babu buqatar hakan ya Sa'ood kawai mu tafi" taje ta wanke hannun ta yayi settling bills din suka tafi,

Cikin mota kuwa shirun da Leesa tayi ya dami Sa'ood yafi so yaji ko yaushe tana jero tambayoyin ta da Basu qarewa dan hakan ne kawai yake tabbatar Masa Bata cikin wata damuwa,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now