chapter 7

228 37 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Wannan shafin naku ne*
*Fatima isma'il (fatyn amadulle) Aunty Sadiya vice, maman Adnan, Aisha babayo, hapseey, Mrs naseer, maman fatima, maman sadik, maman shareep, Mrs prince, miss danzango,momyn twince, rabi'at Muhammad, husna m Kora,*.......Wanda basuji sunan su ba a jira ni a coming pages🤩
*Kuma Ina godiya da sharhi Allah ya barmu tare*😍😘

07👯
'''Please ga amanar yaran nan da iyayen su ba shegu bane muna cikin wani matsala ne Amman zamu zo mu dauke su nan da dan wani lokaci, mai tabo a qirji itace babba Haleesa dayan kuma itace qarama Saleeha'''

Cikin tsananin firgici, tsoro da Kuma mamaki yake kallon takardan da abinda ke rubuce a jiki, tabbas wannan RUBUTUN SHI NE, shi ya rubuta abinda ke jikin wannan papern da hannun shi a office dinshi, gaba daya ya shiga rudani ' does that mean sune.... Innalillahi wa inna ilaihirraji'un' shine kawai abinda yake maimatawa a zuciyar shi.

A take zufa ya fara tsatstsafo Masa ta ko Ina shikam kwanakin shi na rayuwan duniya ya qare dan idan har Sa'ood yasan Sarwa ne ta tashi a gidan KARUWAI saboda sakacin shi sunan shi gawa.

Sarwa da MAILAFIYA FAMILY suka Dade suna Mata tanadi, Sarwa da mamanmu take kwance a gadon asibiti saboda rashinta tsawon shekaru kusan 17, Sarwa da itane sanadin gaba tsakanin shi da 'dan uwana shi, Sarwa da itace silar da aka rufe MAILAFIYA HOSPITAL aka kwace takardun shi gaba Daya Wanda ke nuna shaidar shi likita ne aka tura shi prison ga matsala da ya samu da iyalinshi, Ashe da Sarwa yake rayuwa Bai sani ba.

Dago rinannun idanun shi yayi ya daura ma Salee, batare da ta lura da yanayin shi ba ta miqa mishi necklace dinta na gold, ya karba Yana tabbatar da wannan sarqan Sarwa ne Wanda babanmu ya saka aka qera na musamman saboda ita.
"Kaga sarqan da aka tsince mu da ita, Leesa ma tana da irin shi Amman shape din pendant din ya banbanta, shugaba ta fada Mana Mai tsada ne sosai Kuma ta bar Mana shi ne Dan musan asalin mu Amman akwai alqawari tsakanin mu da ita na duk ranar da muka samu iyayen mu zamu sayar da necklace din mu Bata kudin shi".

Gaba Daya Sa'eed ya rasa Mai yake Masa 'dadi, he can't believe that Sarwa da suka rasa a Kano ne ta dawo jigawa, how? When? Why?.

Ganin idan ya cigaba da zama zata iya gano halin da yake ciki yasa ya miqe Yana qoqarin daidaita kanshi yace
"Yanzu ki shiga gida, Bari naje na dawo" ya juya ya tafi.

Leesa dake labe tana kallon su tayi saurin juyawa ciki kuka na cin qarfin ta, bin bayan shi Salee tayi da kallo tana tunanin tausayin su ne ya saka Sa'eed tafiya yanzu Dan ta lura da canzawa yanayin shi.

Shiyasa take qara son shi komai nashi daban ne, murmushi tayi tana rungume takardan a qirjin ta
"Ohh I love you malam Sa'eed, insha Allah nothing in this world can separate us, I'm meant to be yours" ta sake wani murmushi tana rufe fuskar ta da tafin hannun ta wani shauqin so na taso mata.

Shiga gidan tayi tana rero waqar soyayya, tana shiga dakin su ta hango Leesa kwance a dandamarin qasa tayi rigingine hawaye na bin gefen fuskar ta.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now