chapter 45

212 37 4
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

45👯
"Kan uba!!, dama yaudara ta kakeyi ya Sa'ood? Wata 'yar iskan zaka aura ba tare da sani na ba?"

Cikin salon tsokana ya toshe bakin bakin sa da tafin hannun shi Yana fadin "a'uzu billahi, haba Haleesa me amarya ta tayi Miki Zaki Kira ta 'yar iska? Kuma fa ke Kika ce mama tace ba zata bani ke ba nayi haquri, shiyasa da Naga bazan iya jure zama haka Babu aure ba kawai naje muka daidaita da wata Mata ta yarda zata rufa min asiri ta aure ni"

" Ni wallahi mama Bata ce ba zata baka ni ba Bata ma San da wani Abu a tsakanin mu ba"

Gyara tsayuwar shi yayi tare da zabga tagumi kamar da gaske yace "to yanzu Yaya zamuyi Kenan princesa? Tunda na riga nayi alqawari ma wata idan naje nace tayi haquri ba zata ji Dadi ba"

" Saidai kada taji din, Amman na rantse da Allah ba zaka aure ta ba, ba zai yiwu ka hada Dani da ita lokaci daya ba, kawai tayi haquri ai ita ba jinin ka bace ni qanwar ka ce ni zaka aura ya Sa'ood, kace min kana Sona ai ko? Kullum kana fada min kana Sona Kuma shine zaka je ka auri wata?"

Haka tayi ta sumbatu shiko ya zuba Mata Ido cike da mamaki Bai taba tunanin Leesa tana son shi da har zatayi kishin sa ba, ganin hawaye na zuba a Idon ta yasa cikin tsoro ya bude Baki zaiyi magana tayi saurin juyawa ta koma part din mamanmu ba tare da ta saurari abinda zai fada ba,

A rude yabi bayanta Yana Kiran sunan ta, mamanmu ma tana ganin Yanda ta shigo a birkice tana kuka yasa tayi saurin kunna kekenta ta nufeta Amman kafin ta Isa Leesa ta qule cikin daki ta rufo qofa, juyawa tayi tana kallon tuhuma ma Sa'ood sai kame_kame ya fara
"Umm..mama.fa..kawai... wallahi wasa nayi Mata Bata fahimceni bane tayi fushi"

Tabe Baki tayi ta juya Kan kekenta tayi gaba tana fadin " can Muku"

Haleesa na Shiga daki ta fada Kan gadonta hade da sakin kuka Mai tsuma zuciya Wai Sa'ood ne zaiyi aure da wata ba ita ba? Saida ya Gama dasa mata sonshi a cikin zuciyar ta kafin zaice zaiyi aure ya barta? Ba zata jure rashin shi ba Kuma ba zata juri ganin wata kusa dashi ba tana matuqar sonshi da kishin sa shine jigon rayuwar ta a yanzu,

Tashi tayi ta Shiga bathroom ta kunna famfon sink ta wanke fuskar ta sannan ta dago tana kallon fuskar ta a mirror, "wallahi, wallahi ko wacece wannan sai ta rabu da Miji na, Sa'ood ni yake so Kuma ni zai aura Banga dalilin da wata zata zo ta qwace min shi ba,
Tun a lokacin baya duk abinda nasa a gaba sai na samu wannan karon ma haka ne Dan bazan taba bari shegiyar Nan ta auri ya Sa'ood ba INA SON SHI SOSAI"

Fitowa tayi ta canza hijab din jikinta dan wancan ruwa ya jiqa wuyan, ta dauki wayarta missed calls din Sa'ood kusan guda 15 ta gani a lokacin ma wani Kiran ya sake shigowa, batayi picking ba ta dauko takalmi ta saka ta Suri wayarta da qaramar side bag ta fita,

A parlo ta hangi Sa'ood sai jeka ka dawo yake da waya kunnen said gaba daya ya Shiga damuwa, Jin ringing din wayarta a kusa dashi yasa ya dago Yana kallonta Tasha murr Bata lura da Idris da wani matashi 'dan gidan da Nabeela dake shigowa ba tace "muje"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now