chapter 46

199 34 5
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

46👯
Leqo da kanta tayi ta saita dutsen dai_dai qeyar mutumin, Sannan ta qwala mishi tayi saurin komawa cikin lungun ta buya tana dariya Sa'ood dai kallon ikon Allah kawai yakeyi,

Ihu mutumin ya saka Yana Sosa wurin da Leesa ta jefe shi dan Babu laifi ta qware wajan saiti, Lateefa na ganin abinda ya faru cikin murna ta qwala Kiran sunan "Haleesa!! Kina Ina ne 'yar uwa ki fito dan Allah"

Mutumin dai na tsaye yaga ta Ina Haleesan zata fito yaci ubanta Amman ganin ta tare da Sa'ood yasa yasha jinin jikin shi yayi qwafa kawai ya juya ya tafi, ya saka ma ranshi sai balaraben Nan ya tafi zai dawo ya ci qaniyar ta,

Rugowa da gudu Lateefa tayi ta rungume Haleesa tana dariya, sai Kuma ta sake ta taja da baya kadan tana qare Mata kallo,
"Leesa kece wannan? Innalillahi kin ganki kuwa? Kin dawo Kaman 'yar turawa, mijin Salee ne wannan ko?"

Murmushi Mai sauti tayi ta riqe hannun lateefa tana jijjigawa cikin Jin dadi tace "yayana ne wannan, yayan mijin Salee ne sunan shi ya Sa'ood, shi 'dan yayan mahaifi na ne yanzu nasamu dangi na Lateefa"

Tsalle ta daka ta qanqame Haleesa tana dariyan farin ciki "nayi Muku murna sosai Haleesa Allah ya saka mu a madamacin ku kema shi din Zaki aura?" Ta fada cikin zolaya tana kashe Mata Ido daya,

Rausayar da Kai Leesa tayi ta Ciro IV daga cikin handbag dinta ta miqa Mata "gashi naki katin gayyatar ta musamman, tun sauran sati nake so kije gidan mu ki tare asha hidima tare dake na saka ki a cikin qawaye"

Sake runguman Leesa latifa tayi tana Jin kaman tayi Mata kuka saboda farin ciki Sannan ta dago tacewa Sa'ood dake make a gefe Yana lallatsa wayar shi "sannu angon mu"

Ya saurari hirar su tun daga farko Kuma yaji sannun da Lateefa tayi mishi Amman batayi mishi da ya amsa ba, tun daga Kan shigar ta tasha mini skirt da gashin doki da kuma kwalliyar ta da yayi kaman na shedanun aljanu bai cancanci da ya amsa ba,

Fisge wayar hannun shi Haleesa tayi tana hararar shi, ya dago zaiyi masifa yaga Wanda ke cikin idon ta yafi nashi sai ya sassauta murya "novio please give my phone back I'm doing some official work and it's very important"

Dan saboda kada Lateefa taji sun sauya harce tayi tunanin wani Abu yasa tace "yau ba ranar aiki bane ya Sa'ood, aunty na tana gaidaka baka amsa ba"

Wayancewa yayi yace " ohh yaya kike"

Kan Lateefa a qasa tayi mishi proper gaisuwa sannan taja hannun Leesa suka Shiga gidan shugaba, Sa'ood ya bisu da Ido Wai a wannan gidan magajiyar karuwan qannen shi Sarwa suka tashi, Yana jin Yanda gidan ya dauki ihu da shewa na muryan maza da Mata kowa Yana oyoyo Salee Babu Wanda yayi tunanin Leesa ce saboda Yanda ta sake tana ma kowa da kowa murmushi,

Shugaba na Jin ana Kiran sunan Salee ta fito dan tabbatar ma kanta da gaske yaran da suka yaudare ta suka tsere ne yau suka dawo, kallo tabi Haleesa dashi tun daga sama har qasa sai Kuma ta juya ta koma dakin ta, jiki a sanyaye Haleesa ta buta ciki ta hange ta zaune ta kawar da kanta gefe sai taunar chewing gum takeyi qaras..qararas...,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now