chapter 5

280 28 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Wannan shafin naku ne masoyan gaskiya, members din *REAL KAMA DA WANE FANS*
Special thanks to
*My Umma sulaiman, Aisha Hamza (sweetheart), maman hafeez, maman saudat, Aisha Lameengel (namesy), maman sadeeq, my pinky(ruqy), antimee,zee dauda, hadiza mustapaha, ummu al'amin, hadiza aminu Ali, Maryam gambo, Mrs Abdullahi, sis pha'ixer, sis hussy, maman Shaheed, maman ammar*......... *Wanda ma basuji sunan su ba ma su jira coming pages sharhin ku na qayatar Dani matuqa, love you so much ❤️❤️❤️*

05👯
Tsayawa tayi a qofar gidan su tana karanto addu'oi kafin ta tattaro qwarin gwiwar ta na tunkaran Leesa ta shiga cikin gidan, Bata tsaya ko Ina ba sai dakin su lokacin na Shirin islamiyya.

Ta saka uniform tana qoqarin saka socks ta dago tana kallon Salee da ta rakube a jikin qofa tace
"Wato ke idan Kika fita sai an ganki ko? Tun kafin na debo ruwa Kika fita siyo sweet gashi har na shirya kina tsaye a wurin, kinsan dai ba jiran ki zanyi ba wallahi Ina gamawa tafiya ta zanyi"

Qarasowa kusa da ita tayi ta zauna tare da sunna Kai qasa tana faman murza laidan hannun ta da kaganta kaga marar gaskiya, a hankali ta Kira sunan ta.

Saida ta leqa fuskar ta kafin ta dago kanta tana Mata kallo Mai alaman tambaya tace "meye?"

Gyara zama Salee tayi ta fara bayani
" Kinga dai kyautatawa Yana da kyau ko? Kuma idan ka fitar da wani daga qunci kaima Allah zai fitar dakai, Kuma kin tuna malam yace Mana sadaka na maganin baqin ciki Yana yaye masifa Kuma kema kullum sai kinyi sadaka da safe saboda burin mu ya cika ko ba haka ba?"

Daure fuska Leesa tayi tace " eh haka ne, sai akayi Yaya"

"Umm... Am...Daman inaaso ne na taimaki wani bawan Allah wallahi Baki ganshi ba abun tausayi, matar shi bata bashi abinci wani lokaci kwana yake da yunwa shine nakeso ki amince Mun na....."

" Na amince Miki ki ciyar dashi ko? Gaki 'yar gidan qaruna"

" Aa da kudin shi fa, ya roqeni ne yanaso Yana bada kudin shi a dinga dafa mishi abinci daga gidan Nan ana Kai mishi"

Miqewa tayi ta jawo hijabin ta tana qoqarin sakawa tace
"Waye shi?"

Da sauri Salee take
"Malam Sa'eed dinnan ne na school dinmu wanda nace Miki yaran shi kyawawaa"

" To ban yarda ba, akwai restaurant bila adadin a garin Nan idan bayi da kudin da zai iya ci a wurin yaje maciya ya siya Amman baza a dinga Kai Masa abinci daga gidan Nan ba kinji na fada Miki, idan kin Gama ki same ni a makaranta Kuma kiyi sauri"

Tana Gama fadan haka ta fita, dama Salee tasan da'a rina Kuma tayi alqawarin ko Leesa Bata so sai ta dinga kaiwa malam Sa'eed abinci Koda kuwa a boye ne.

Da suke dawowa daga islamiyya ma haka Salee ta matsa tana Mata Magiya Amman turmushishi taqi, itama daga Nan tahau dokin zuciya bataga dalilin da zaisa Leesa tana mulkanta tana juya ta Yanda taga dama ba Bayan tsakanin su ma babu wani rata.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now