chapter 20

255 33 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Wannan shafin naku ne manazartan *proficient*
*Ay indabo*
*Sadeeq* and
*Sarauniya beelat*

Jinjina gareku 👍🏼 Kuna namijin qoqari👌🏼 Allah ya qara ma rayuwa albarka🤲🏼

20👯
"Bata sukayi ba sace su akayi ba"

A zabure Leesa tace "what? Yaya za'ayi yarinya ta Bata a cikin asibitin gidan su? Kuma ba Daya ba har biyu? Kai da ka kaisu asibitin kana inane har hakan ta faru or maybe daman son hallakar dasu kake son yi tun farko?"

" Ko kusa kada ki sake saka wannan tunanin cikin ranki, Yaya za'ayi naso hallakar da farin cikin Wanda ta ceci rayuwa ta? I'm not that bad guy, infact fansa nake son dauka Mata mamanmu deserves justice, Sa'eed ne ya jawo komai shine silar batansu Bayan yasan bazai iya kula dasu ba ya karbe su ya batar dasu har yanzu yaqi dawo Mana dasu and I believe yasan inda suke"

Daram Leesa taji qirjin ta ya buga, hakan na nufin Sa'eed yasan sune Sarwa tunda ya karanta takardan da aka tsince su dashi kuma tana da yaqinin Salee ba zata gaza nuna mishi sarqan ta ba,

Ya Rabb!! Daman tun farkon ganin ta dashi taji be kwanta Mata a Rai ba gashi yanzu ya aure 'yar uwar ta Yana so ya hallakar da ita tunda har ya riga ya gane ta be maido ta cikin familyn su ko ya kawota ma Sa'ood ba, dole kawai tasan Yanda zatayi ta fita daga wannan gidan taje ta ceci Salee daga hannun Sa'eed su tafi wani wuri can nesa da Mailafiya family Yanda HAR ABADA ba zasu same su ba,

" To baka fadamin Wanda ya kashe mahaifin Sarwa ba, kuma mahaifiyar sun tana Ina? Ko ita ma ta mutu ne?"

Qura Mata Ido yayi cikin tagumin da yayi Yana kallon cikin idanun ta he can see something else in it, he can feel the hatred in her words, meye connection dinta da familyn su da take son Jin komai game dashi?"

"Mahaifiyar su tana da Rai Amman tun daga wannan ranar ta dawo kamar gawa, tana kwance a wuri daya tsawon shekaru 17 maybe ba zata tashi ba har sai daya daga cikin abin da ta rasa sun dawo gare ta, nasan dady Aliyyu bazai taba dawowa ba Amman Ina da tabbacin Sarwa zasu dawo"
" How?"

" I don't know Amman na tabbatar Miki zasu dawo Kaman Yanda nake da tabbacin zan kashe Wanda ya kashe dady Aliyyu, zuciya ta zata iya bugawa idan na sake ambatan sunan shi ba tare da jinin shi a jikin makami na ba, kiyi haquri da tambayoyin ki abunda Zaki iya sani Kenan daga cikin labarin mu maybe idan kina da rabo Bayan na Gama cika burika na idan Allah ya hada fuskokin mu wata rana na Baki sauran labarin familyn mu wataqila a wannan lokacin ba zakiyi min kallon 'dan ta'adda ba,

Ki kwanta ki huta ko zazzabin ki zai sauqa idan Kuma bakiji sauqi ba gobe sai muje asibiti, Saida safe"

Girgiza Masa Kai kawai tayi, ya juya zai Shiga ciki har ya Kai qofar bedroom dinshi ya jiyo muryar ta
"Umm please kada ka manta ka duba gidan su Ameeran gobe zan baka address dinsu da safe"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now