chapter 10

285 39 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
   *And aunty Fenarh matar Soja*

10👯

Sa'eed na shigowa cikin gidan matan tayi wa Zarah sallama ta tattari takalman ta tayi waje, tun daga nesa take hararan shi ta rasa wani rashin mutunci zatayi Masa ta huce, tsaban wulaqanci Wai ita ne Sa'eed zai hada ta kishi da karuwa?

"Wato Sa'eed baka dauki tozarta ni a bakin komai ba ko? Da na nuna banji dadin kasancewar ka da karuwa ba shine zaka auro ta Dan ka gwada min ka Isa ka jawo min zagin mutane ko? To Naga isar taka bazan Hana ka aure ba gida ne gashi Nan koma wacece ta shigo babu abin da zata tsinta ciki Banda tsiya da baqin talauci ni banga abun kishi a Nan ba"
taja dogon ta fice ta bar mishi dakin.

Sauqe ajiyan zuciya yayi don baiyi tsammanin abun daizo Masa da sauqi haka ba a tunanin shi Zarah Zata tada hankalin ta ta daga mishi hankali, Amman yanzu ya tabbatar da Abu Daya cewa da gaske ne Zarah Bata sonshi abun hannun shi take so shima zai roqi Allah ya cire mishi sonta ya huta.

Dakin shi ya wuce yayi wanka ya saka jallabiya sannan ya zauna ya dauki wayarshi yayi dialling numbern Sa'ood har ya fara ringing yayi saurin kashewa Yana tunanin to me ma zaice mishi idan ya dauka? Har yanzu Bai samo Sarwa ba ko Kuma ya samu daya Daya ta gudu?

Bai ajiye wayar ba Kiran Sa'ood ya shigo Saida gaban shi ya fadi Dan yasan tambaya daya zaiyi Masa 'ina Sarwa?'

Picking yayi jikin shi a sanyaye ya saka a kunnen shi, muryan Dan uwan shi da yayi shekara da shekaru Bai ji ba ya doki kunnen shi
"Sa'eed Sarwa tana Ina? Ka same ta ne?"

Jan numfashi yayi sannan yace "har yanzu ban same su ba brother....."

"Shhhh don't ever call me your brother again until you find Sarwa, wato da kaga ban waiwaye ka bane shine Bari ka Tuna min ko? Shirin qarasa Garba TK nake yi Ina gamawa dashi zan dawo gare ka, so ka shirya dawo min da Sarwa idan ba haka ba hankalin kowa ya tashi"

" Please Sa'ood ka daina irin wannan maganar nayi maka alqawarin insha Allah zan dawo maka da Sarwa Amman ka taimaka min wajen yin hakan ka dawo gareni mu hada Kai wajen Nemo Sarwa na tabbata zamuyi nasara, let's act like the old Sa'ood and Sa'eed the loving twins ko wani yanayi nake ciki kana tare dani kana Taya ni farin ciki ko baqin ciki Dan Allah ka dawo Ina buqatar ka kusa dani"

Murmushin takaici Sa'ood yayi yace "hakan zai faru ne kawai idan da Sarwa tsakanin mu, babban kuskuren da nayi shine da na zamo Mai maka fatan alkhairi kuma Mai maka kukan baqin ciki tunda gashi ni Ina cikin wannan yanayin ka kasa cire ni, kasan adadin hawayen da nake zubarwa duk lokacin da wani Abu ya Sami Sarwa ko mamanmu but still kayi sake har muka rasa su duka, yanzu ko a Ina suke? Suna Tare da wasu irin mutane ne? Tunda suka tashi sunci abinci kuwa? Inama ace Saleeha tana tare dani da na fara nuna Mata irin son da nake Mata da yanzu saura qiris na zamo angon ta Amman ina! Sakacin ka ya jawo na rasa wannan Daman Kan mailafiya family gaba Daya ya rabu saboda Kai da babanmu"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now