chapter 8

247 36 1
                                    


(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad karim*
          And Fenarh matar Soja

08👯
4:00am
Ta farka saboda kiraye kirayen sallah da akeyi, har yanzu wuri da duhu sai dan hasken wutan lantarki dake can gefe kusa da masallacin Tasha.

tsoro ne ya Kama ta sosai da taga mutanen dake kwace Akan benches suna barci ga kwalaben giya da sigari barbaje ta ko Ina, tasan motsi kadan zatayi su farka hakan yasa ta koma wurin da take kwance ta rungume jakar ta a qirjin zuciyar ta cike da fargaba.

Kaman a cikin kunnen ta ake Kiran sallan haka take ji, ta Saba hudu nayi ita da Salee zasu farka suyi sallah kafin su fara tilawan Al-qur'ani har a shiga sallan asuba.

Ko a wani Hali Salee take yanzu? Tana cikin kwanciyar hankali Koko Aa? Kodayake tasan ba zata damu da rashin ta ba tunda ta iya fitar da ita daga zuciyar ta, a ko wani Hali Salee take tana Mata fatan alkhairi, Allah yasa Sa'eed ya Bata kulawa.

Har gari ya fara haske mutanen Nan Basu farka ba itama Bata fito daga wurin da take labe ba, saiq 6:30 na safiya kafin drivers da sauran ma'aikatan tashar harda passengers suka fara shigowa.

Hamdala tayi da taga wurin ya fara cika da sauri ta fito rungume da Jakarta tana bin mutanen wurin da kallo, taje wurin toilet din Mata ta zaro 1k daga cikin 27k dake Jakarta ta bada kudin shiga.

Kallon ta kudin tayi tace Bata da canji saidai take wurin 'yan talla ta Nemo, Leesa batayi musu ba ta sake kinkimar jakar ta take wurin da take tunanin zata samu canji tana ankare da idon mutanen dake kanta, tunda ta Ciro kudin Nan suke binta da kallo.

Qosai na 100 ta siya da pure water na 20 ta zuba a cikin jakar kayan ta ta koma wurin public toilet din ta biya kudin shiga naira 50, ta cika ruwa a buta zata shige matar tace
"Baiwar Allah ki bar jakan a Nan wurin Mana a kula Miki da ita kafin ki fito"

Murmushin Yaqe tayi tace
" Aa hakan ma yayi " Bata jira cewar ta ba ta shige toilet din, bada jimawa ba ta fito tayi alwala, sannan ta ciro zani ta shimfida tayi sallah jakar ta na gaban ta tana kallon shi.

Tana idarwa ko addu'a batayi ba ta tashi daga wurin Dan ta lura da mutanen dake zagaye da ita son rabata da sauran abun da ya rage Mata sukeyi ta nufi wurin da ake shiga motoci.

Kaduna taso zuwa wurin wata aunty Helen, saidai motan kaduna babba ce kuma namiji Daya ne a ciki, ga wa'innan mutanen har yanzu suna biye da ita Bata da zabin da ya wuce ta shiga motan KANO Wanda ya kusan cikawa, tana shiga daya daga cikin su yabi ta cikin motan baifi da minti 30 ba aka karbi kudan mota suka dau hanya.

Tunani take yi ita yanzu Ina zataje a Kano Bata San kowa ba Bata San ko Ina ba gashi abinda ta guje mawa ya biyo ta.

Saida suka kusan Isa sannan ta tuna da gidan su qawar ta Ameerah dake DUKAWA saidai fatan ta Daya Allah yasa Basu tashi ba don rabon ta da Ameerah tun primary school, baban ta drivern babban mota ne da yake tafiyar da Kaya gari zuwa gari.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now