chapter 25

220 35 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Bonus page*💃🏻💃🏻

_fans na gode qwarai da addu'oin ku, da masu SMS da masu kira da masu Bina PC naji dadi sosai da Kuka nuna kulawa, I never knew I was that popular😜🤩 ciwon bai yi tsanani kaman yanda nayi tunani ba and it can be corrected easily, very soon my vision will be clear again insha Allah_

*Thank you so much*💖
*Ummu najma loves you*😘

25👯
Kafin su fita ya Shiga office din shi saboda yasan irin rudewa na baba rabi da Kuma tsufa da ya Kamata za'a iya kaisu tace Bata Gane wacece Hafsat da Aliyyu ba shiyasa ya dauki takarda yayi rubutu Yanda zata iya riqe su har muje mu dauke su ba tare da ta nemi sanin iyayen su ba,

Da takardan a hannun shi ya dawo ya tattare su na fada mishi motar da nazo da ita zai saka driver na ya tafi dasu, Sa'eed Bai Dade da fita ba na sake Jin qaran harbi,

a wannan lokacin nayi saurin fita bugun zuciya na Yana dada qaruwa a Kan Ido na ka qarasa hallaka shi Kuma lokacin babu abinda zan iya a kai, da bullet uku ka kashe Daddy Aliyyu lokaci daya, haka na qaraso na samu gawan shi a wulaqance cikin jini lokacin Kai Kuma ka ja gawar mahaifin ka kayi gaba dashi,

Tunani na daya Yanda zan maida shi ma iyalin shi Yaya zasuji? Wani irin baqin ciki zasu shiga? Wani laifi za'a ce musu ta aikata da ya cancanci wannan kisan wulaqancin? Haka muka dauke shi jiki a muce muka kaishi gida don ayi Masa Shirin tafiya gidan shi na gaskiya,

Tunda matar shi Hafsat ta daura Ido a Kan gawar shi ko magana ta kasa yi, saboda tashin hankali da baqin ciki ko bakinta ta kasa budewa ballantana ta Sanu damar kuka, duk Yanda ta tursasa zuciyar ta yabar idanuwan ta su zubar da hawaye ko Dan ta rage Jin radadin abinda ke cikin ta kasawa tayi,"

Lokaci daya idanun shi sunyii jaa jijiyoyin gaban kanshi sun tashi, Cikin qaraji yace
"Garba bamu Shiga tashin hankali ba har Saida driver na yazo ya shaida Mana ba'a cikin motar shi aka saka Sarwa ba, Sa'eed ba a baqar Corolla x da naje dashi ya saka su ba wani mota daban ya jefa su Kuma ba'a San daga Ina motar ta fito ba ba'asan inda taje ba,

kasan me mahaifiyar su tayi kuwa?? She just collapse Kuma har yanzu Bata tashi ba, ba zata iya jure rashin miji da yara biyu a Rana Daya Kuma lokaci daya ba and all this happened because of you and Sa'eed's foolishness, Ka Raba Mana Kan family Ka saka qiyayya a zuqatan mu kana ganin zaka ci banza ne? No!!!

Dole kaima na 'dan'dana maka azabar da kake 'dan'dana ma bayin Allah ko babu komai nasan nayi jihadi Kuma Allah zai bani ladan hakan dan tabbas zan kubutar da Wanda zaka halaka jibi ta hanyar raba ka da doron duniya,"

Bai Bata lokaci ba ya jawo pillown da yake kwance a Kai ya Danna mishi a fuska, tun Yana wutsul_wutsul da kafa har ya cika sannan ya gyara ma gawan shi kwanciya ya rufe shi da blanket ya dai_daita kanshi sannan ya fita daga dakin, sauran yaran Garba suna tare shi a waje yace musu barci yake yi Amman ya fada mishi a sanar musu ko meye ya faru dashi zasu tsayar da operation dinsu,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now