chapter 4

302 35 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

04👯
Ranshi a mugun bace ya tako har zuwa wurin da take tsaye Yana kallon ta cikin Ido, tuni jikin ta ya fara kyarma don wani kwarjini yayi Mata sosai ya cika Mata Ido.
"Ban taba dukan wata ya mace ba, kada ki saka na fara a kanki wallahi ki kiyaye ni Zarah"

Saida ta tausasa murya kaman zatayi kuka tace
"To Dan Allah ka sake ni na koma gurin iyaye na, wallahi na gaji bazan iya zaman talauci ba mutuwa zanyi"

Saida yayi 'yar qaramar dariya sannan yace
"Ai auren mu na zobe ne babu saki, abunda hausawa suke cewa mutu ka raba, duk inda zanje tare dake zan tafi komi dadin wurin komi wahalan shi kabari ne kawai ba zamu shiga tare ba shima kawai zan barki ne ki kulamin da yara na.

Kin riga kin dasa min sonki a cikin zuciya ta ya zamo Miki dole kiyi haqurin zama dani, lokacin da Zaki aure ni ma ai haka kike fadamun idan babu ni mutuwa zakiyi Kuma gashi yanzu kina neman rabuwa dani dan haka idan ban sake ki bama nasan babu mutuwan da zakiyi"

Ya shafo fuskar ta cikin kula murya can qasa yace
"Bazan rabu dake ba mi alma(my soul) duk wacce ma zata shigo cikin gidan Nan haka zata same mu, bazan yada ke ba please ki qara haquri wata rana sai labari komai zai wuce kaman ba'ayi ba"

Raurau tayi da idanun ta qolla na taruwa a ciki, tana son zama da Sa'eed Kuma tana kishin sa sosai Amman ba zata iya zama dashi a cikin talauci ba
"Please kayi haquri ka sawwaqe Mun na koma gidan iyayena na zauna idan kana so ma zan iya bari maka 'ya'yan ka a Nan please set me free"

Zarah tana bashi takaici, a rayuwan ta wato ita Bata san qaddara ba bare ta rungume shi ta samu dacewa na duniya da lahira, no ita kawai aji dadin duniya shikkenan.

"Mi alma your mother is also part of the mailafiya family and kinsan Sarwa ta bace da duk wani mahadi da mabudin dukiyar mu Wanda yake wurin babanmu, har yau mamanmu Bata farka ba ballantana a samu wannan kudin su dawo garemu, so idan Kika koma gida ma ba wani amfani hakan zai Miki ba"

" Amman ai mahaifina ba 'dan zuri'an mailafiya bane ko? Kawai ka sake ni ka fita harqata"

" Bazanyi ba cariña do whatever you want"

" To wallahi Kai da zaman lafiya kunyi sallama a cikin gidan Nan tashin hankali yanzu ka fara gani"

" I don't care tunda kina da tsoro har kikan lanqwasa harshen ki zanyi manage a haka"

Yana Gama fadan haka ya wuce dakin shi ranshi yana mishi zafi, yana addu'an Allah ya bayyana Sarwa wa'innan matsalolin suzo qarshe.

**********
Salee na shiga gida taci Karo da Helen da Lateefa suna tsaye cirko_cirko ana jiran dawowar ta, damuwar da ta gani Akan fuskokin su yasa annurin fuskarta bat ya bace, hankalin ta ya tashi a tunanin ta wani Abu ne ya Sami Leesa.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now