chapter 33

219 38 8
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

33👯
"Da raina da lafiya ta da wayo na Banga Wanda ya Isa ya sayar dani ba wallahi, Allah idan baka maidani asibiti ba zan..."

" Me Zaki iya? Uhmm? Nace me Zaki iya?"

Shagwabe fuska tayi kaman zatayi kuka tace "koma menene nidai ka maidani inda ka dauko ni ko Kuma na nuna maka ka gani"

"Duka na Zaki yi?"

" Aa Harbin ka zanyi"

"toh Allah ya Baki sa'a Haleesa, idan na mutu sai ki fadamin zuwa lokacin inaga Mun Isa wurin da zan saida ki"

Shiru tayi ganin Yana qoqarin parking a gaban wani shopping mall, ta tsaya tana kallon shi har ya fita ya zaga ta windown seat dinta yace "mu tafi ko?" hade da bude Mata qofa,

"Me zamuyi a Nan ya Sa'ood"

"Wai Dan Allah in tambaye ki, Baki gajiya da tambaya ne Kam? Kizo mu Shiga Kaya nake so in siya na chanza Mana furnitures dan bazan koma gidan mu da tsoffin Kaya ba that's all"

Fitowa tayi suka jera tare har ciki, furnitures ya fara zaba Wanda nashi da na Haleesa da na momy da na mamanmu aka wuce musu dashi gida sannan suka wuce ya siya akwatuna manya guda hudu duk size Daya Amman collection din kaloli daban_daban suke zuwa,

side din da ake sayar da kayan sakawa na mata suka je ya fara zaba Mata, ko wanne yaga yayi mishi kyau sai ya dauka ba tare da ya tambayi ra'ayin ta ba Leesa kuwa ta gilma duniyar kalle_kalle dan Bata taba zuwa wuri irin Haka ba,

Saida Sa'ood ya gama tarkasan tarukucen shi sannan ya dibe ta suka koma wani side daban Wanda ake siyar da jewelries, takalma, jakakkuna, da Kuma kayan kwalliya,

Tagumi ya zuba Yana kallon wurin shi Bai taba tunanin haka Mata suke da Tara tarkace ba dan yanzu ma wata staff din wajan ne take guiding dinsu Kuma tace mishi sayan wa'innan kaman dole ne dan su suke qawata ado,

"Yanzu ke me kike so a cikin wannan kayan haukan?" juyawar da zaiyi ya hango Leesa can fereren duniya ta tsaya ta saki Baki tana kallon irin statues (gumaka) da ake saka musu Kaya ana displaying dinsu, ta riqe qugu sai zuba ma statue zance takeyi,

Dariya staff din tayi ta tambayi Sa'ood "wancan Amman 'yar aikin ku ce"

"Ta Ina tayi miki Kama da 'yar aiki? She is my sister"

Kallon shi tayi a kaikaice tace "gaskiya Baku Kama, ta Yaya ta zamo sistern ka? Or is she a cousin or a distant relative? Ko ma daga qauye tazo?"

Lokaci daya Sa'ood ya Bata Rai Jin tana neman zagin Leesa "look, bani son shishshigi koma menene kawai kiyi abin da take gaban ki, she is my fiance kada ki kuskura ki zage ta"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now