chapter 35

208 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

35👯
Tagumi sa'ood yayi Yana jujjuya maganar Adam, ba zallan second option ba harda first option din yayi mishi wahala Dan baisan ta inda zai fara neman Mai laifin a cikin su ba, su suwa ma kenan? Shi ko Idris? Tunda ance ba Sa'eed bane, yasan cewa Idris can never stoop so low yayi Abun da zai cutar dasu irin Haka ba bazai ma yiwu bane Adam yayi misunderstanding situation din ne,

Duk cikin Mailafiya su uku ne manyan magada Kuma su uku ne suka San abubuwa dake wakana ciki da waje sauran duk yara ne Basu ma yi wani wayon da zasu iya tsara irin wannan crime din ba Dan duk cikin su Babu Wanda ma yakai shekaru 30 "to wayene?"

Ya tambayi kanshi idan Kuma ya amince da Option na biyu ko wani member na Mailafiya family babba da qarami sai ya cutu, Dan lalacewar abin yake gudu kowa zai koka yawan su yanzu ya ruba na da sau uku ta ko Ina hayayyafa akeyi idan ya saka gwamnati ciki Abu ya rincabe baisan Ina ze Kai 'daruruwan mutanen da ke qarqashin su ba and at the end harda orphanage din abin zai shafa dan sabon gwamnati zata iya sake qwace su,

Cikin damuwa da rudani da ya Shiga yace "Adam Yaya zanyi yanzu ta Ina ma zan fara binciko Wanda yayi wannan barnan? Ni ba likita bane banma San ko cikin doctors din asibitin bane wani yayi masa haka"

" Eh to Kuma hakan zai iya yiwuwa kasan mutane suna fama da cutar hassada Amman ko cikin doctors din Babu Wanda kuke zargi? Wanda Koda wani qaramin rashin fahimta ya taba Shiga tsakanin su?"

" Gaskiya babu, Babu kowa fa Sa'eed mutum ne Mai sauqin Hali sosai shiyasa ya fini mutane, barshi da neme_nemen Mata da Kuma shagala Amman bayi yarda wani rashin fahimta ya Shiga tsakanin sa da wani Dan duk abinda zai kawo ajinsa ya zube wurin Mata bayi son shi"

" To indai haka ne shawara Daya zan baka, kaje ka samu Sa'eed din ku zauna daga Kai se shi kuyi figuring Wanda kuke da shakku a kansu kada ku cire kowa Kuma kada ku yarda da kowa Koda kuwa baba alhaji ne ko uncle Ishaq ko Kuma Idris kada ku tsame kowa cikin su harda samari masu tasowa da Kuma abokan sa likitoci tabbas wannan ba aikin mace bane Dan hatsarin da yake ciki Mata ba zasu iya yin shi ba Amman ka jarraba hakan insha Allah zamu ci nasara"

Girgiza Kai Sa'ood yayi cikin rashin son gaskata maganar Adam yace "inaa abinda ka fada ba Mai yiwuwa bane, tayaya zaka ce mu hada Kai mu biyu muyi bincike ba tare da sauran ba?

Baba alhaji fa shi da sauran qannen shi ne masu gaba Daya wannan dukiyar, Bayan ya Bata lokaci wurin Tarawa sannan yanzu da yazo gangara sai ya lalata? Magana ma yanzu da qyar yakeyi Dan ma Allah yayi shi Mai tsawon rai ne Amman mutumin da yake nema kusan shekaru 100 yayi irin wannan abun? Kaga hankali bazai dauka ba,

Shi Kuma uncle Ishaq Yana da nashi companyn babba a Mexico Wanda ribar dake cikinta yayi rabin ribar da ake samu a hospital Banga dalilin da zaisa yayi haka ba, and idan Idris ne Kuma...just forget it 'dan uwana bazai taba aikata wannan laifin ba I trust him so much"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now