chapter 37

225 37 10
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

37👯
"Me yasa ko na lokaci 'daya ba zatayi amfani da qwaqwalwar ta tayi tunani Mai kyau ba kamar Wanda kare ya lashe ma zuciya? Ki kalli fa Yanda mijin ta yaci ma 'dan uwanta mutunci a gaban idonta Amman Bata nuna damuwa ba ko kadan instead saima wani lallaba shi takeyi tana bashi haquri,

Wallahi takaicin ta ne ya Hana ni aikata komai ya saka na bar parlorn ma gaba daya saboda nasan idan naci gaba da zama I might do something crazy, na rantse da Allah bazan taba gani ana wulaqanta 'dan uwana na Bari ba ko wayene kuwa"

" Tashi ki zauna"
Mamanmu ta fada tana riqo hannun leesa daya, zama tayi tana facing dinta
"Yayanki yayi laifi Haleesa Dan haka ya zamo Dole a hukunta shi, kuma ni Banga laifin Sa'eed ba da ya dauki hukunci a kanshi, yanzu misali kisa kanki a matsayin Sa'eed mutumin da ya tashi cikin daula da Jin dadin rayuwa Amman rana 'daya 'dan uwan ki da Kika yarda dashi ya ha'ince ki saboda shi kiyi rayuwa gidan kurkuku na shekaru 1-1 har 8 Yaya zakiji?"

" Babu Dadi Mana mama Amman  shima ya Sa'eed din yayi Mana laifi Kuma Mun yafe mishi, ai ni da Salee muma cikin daulan aka aife mu amma sanadin shi Mun tashi a gidan karuwai tsawon shekaru 17 Kinga ya ruba nashi sau biyu harda qarin shekara daya, shi meyasa ba zai yafe ma namu 'dan uwan ba?"

Murmushi tayi irin nasu na manya ta lura Haleesa tana da kaifin baseera Babu Yanda za'ayi ta rudata ta gwada Mata cewa abinda Sa'eed yayi daidai ne, ita kanta tasan bai kyauta ba Amman ta wani fuska gwanda da yayi hakan maybe tozarta Idris da yayi shi zaisa ya gane kuskuren shi

"Ajizancin Dan Adam Kenan Haleesa mutum Mai yawan mantuwa ne Kuma mai aikata kuskure, dukkan mu Nan wani lokaci mukan aikata wasu abubuwa ba tare da sanin mu ba, Kuma dama haka ake son mace ta gari ta zamo Mai biyayya a wurin mijinta ya zamto duk lokacin da yake baqin ciki ko tashin hankali a wurin ta zai samu salama da nutsuwa Ina alfahari da Saleeha sosai nasan ko Bayan raina na ajiye 'yar da zata zamo abin koyi ma 'ya'yan ta, kema kada ki qullace shi dan Allah he is your brother after all"

" To yanzu idan ya Sa'eed baiyi niyan yafe ma ya Idris ba fa? Haka Zaki bar masa 'yar ki a wurin shi yaci gaba da zama da ita?"

" Bani da ikon raba abinda Allah ya hada, Kuma Ina roqon Allah ya kunyatar da duk Wanda yake son ganin wannan alaqan ta yanke, Saleeha tayi matuqar Dace da samun miji wanda nake da tabbacin zai Kare Mata dukkan haqqin ta, fadan dake tsakanin 'yan uwa bazai jawo matsala a tsakanin Mata da Miji ba dan Allah ki fitar da kanki a cikin maganar Nan"

" You are impossible" Leesa ta fada cikin kaushin murya ta tashi ranta a bace ta Shiga bathroom tare da banko qofar, girgiza Kai kawai tayi ta danna wheelchairn ta tayi gaba Saida Leesa taji qaran rufe qofa sannan ta fito ta kwanta,

**********
7:11am

Sauqowa yake yi daga stairs fuskar shi Babu walwala dan tun Jiya ranshi a bace yake kwata_kwata Bai samu ya runtsa ba, tun daga wurin yake jiyo muryar Haleesa cikin daga murya take magana that too da mahaifiyar ta, qara hade fuska yayi ya qarasa wurin Yana tambayar ta abinda ke faruwa, Dan sararawa tayi da ta ganshi tukunna tace

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now