chapter 14

243 32 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

14👯

Sa'ood na Shiga gida ya wuce bedroom dinshi ya fara duba shirt dinshi da ta dawo dashi ta bama abubakar a qofar gidan da suka hadu dashi, Dan ya fada Masa akwai wani takarda da ta saka cikin aljihun rigan, a lokacin Bai damu ya duba ba don a ganin shi babu wani abu a tsakanin su da zata ajiye mishi wani takarda.

a cikin laundry basket ya tsinto rigan dukda a wanke a goge yake amman tunda wata mace tayi amfani dashi yaji bazai sake maidashi jikin shi ba shiyasa ya ajiye a wurin don yayi kyauta dashi wa Mai guga,

_Sa'eed please Kai waye? Mai kake yi a Kano? Ina 'yar uwata? Dan allah kada ka cutar min da ita na roqe ka_

Ninke takardan yayi ta mayar ya ajiye, to meye tsakanin 'yar uwarta da Sa'eed dole ya binciko koma menene Amman kafin Nan he have to handle her kada ta Bata Masa aiki,

**********

Washe gari tun da safe Leesa ta sanar da madam zata bar aiki, taso ta Hana ta tafiya da qarfi Amman ta matsa ita zata tafi Dan yau ko me zai faru sai ta kubuce wa alhaji Kuma ta samu ta koma jigawa duba 'yar uwarta kada Sa'eed ya cutar da ita Dan tun jiya take cikin tashin hankali,

9:15am madam ta Kira Leesa, babu Bata lokaci tazo ta dauka sallamar ta zatayi, da Dan murmushin ta tace "madam gani"

"Yauwa ki hada breakfast ki Kai ma alhaji bedroom dinshi bayi jin dadi ne, ki hanzarta"

A rikice Leesa ta dago tasan tabbas wannan plan din alhaji ne don dazu ya fada Mata yau Bata Isa ta tsallake tarkon shi ba,

"Amman madam ai na ajiye aiki"

"Nasan da hakan ai nace ki Kai mishi, saikace ba aikin kudi kike Mana ba as stupid as you are Wai kina da bakin musu dani, zakiyi abinda na saki ne ko Kuma kin haqura da kudin aikin naki?"

Girgiza Kai Leesa tayi tace
" A'a zanyi"

"Matsiyaciya kawai bace min da gani"
Kitchen Leesa ta wuce ta hada tray kaman Yanda madam ta umarce ta don Bata son ta su Sami sabani har alhaji yasan da maganar tafiyan ta gwara su qare lafiya ta karbi kudin ta tabar mishi gida,

Tafi 10 minutes tsaye tana tunanin Yanda zata Kare kanta idan alhaji ya kawo Mata farmaki ta dauko qaramin wuqa ta soke a jikin skirt din uniform dinta sannan ta dauki tray din tayi part dinshi,

A wangale ta hangi qofar dakin ta Shiga tana karanto addu'oi cikin ranta, wani qaramin table ta nufa zata ajiye ta fita tunda Bata ganshi a dakin ba, sai ji tayi kiriff ya rufe qofa ya zare key ya jefa cikin aljihun wandon shi sannan ya fara nufota Yana dariyan mugunta,

Cike da tsoro Leesa ta fara baya_baya ita taga abinda ya isheta Bai ishi Allah ba wannan wani irin jarababben mutum ne kaman maye? Saida suka Kai dungun dakin tana tafiya da baya, yayi saurin saka hannuwan shi biyu ya tare gefe da gefe ya sanyata a tsakiya, qirjin Leesa sai dukan uku_uku yake yi,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now