chapter 29

243 33 3
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

29👯
"Fortune?" Haleesa ta maimaita cikin sigar tambaya, "Amman Mai yasa suka saka Mana makullin a jikin mu kasancewar mu qananan yara a lokacin?"

Murmushi tayi tace
" Because they have faith in me Haleesa, sun yarda cewa wani cutarwa bazai taba samun dukiyar su ba indai Yana tare dani shiyasa suka danqa min shi, babu abinda yafi daga min hankali lokacin da kuka bata kaman salwancewar dukiyar Mailafiya family I somehow believe wata rana Zaku dawo gareni Amman bani da tabbacin Zaku dawo tare da sarqan ku, shiyasa kwata_kwata ba'a son ku rabu Dan Rabin makullin bazai taba amfani ba saida daya bangaren"

Maida duban ta wurin Sa'ood tayi tace "Chéri please take your brothers along, inaso kayi qoqari ka kawo qarshen qiyayyan dake tsakanin ka da 'dan uwanka yanzu komai ya gyaru kaje ka sameshi kuyi sulhu Dan a irin wannan lokacin Kuna buqatar juna"

Juyar da kanshi gefe yayi cikin bacin rai yace " ba zan iya ba cariño Sa'eed yaci Amana ta ya yaudare ni, ya cutar Dani da yawa bani Jin zan iya yafe mishi idan Bai rabu da Saleeha ba, kawai ya saketa sai a zauna lafiya"

"Ashe akwai ranar da zata zo na roqi alfarma a wurinka kaqi min Sa'ood? Banyi tunanin canzawar da kayi har ya taba tarbiyyan ka ba, inda haka rayuwa take baka yafe was na kusa da Kai da ban yafe maka kisan Garba TK da kayi da sunan daukan fansa ma kawun KU ba Dan ban buqaci hakan daga gareka ba, da tuntuni na miqa ka ma hukuma kaman Yanda kayi ma 'dan uwan ka"

Baice da ita komai ba ya juya zai fita yana jin zuciyar shi yayi mishi nauyi, tabbas Yana son Sa'eed kasancewar shi jinin shi Amman Yana son Salee ma tun Bata tare dasu yayi qoqarin Gina zuciyar shi a Kan soyayyar ta, ta Yaya lokaci Daya Sa'eed zai kwace Masa ita Haka nan Kuma ya haqura?"

Sanin halin shi yasa ta Kira sunan shi ganin zai tafi Kuma alamu sun nuna Bai dauki maganar ta ba, Juyowa yayi Yana kallon ta

"Dan Allah Chéri reconcile with Sa'eed ba Dan ni ba sai Dan qalubalen da Zaku fiskanta wurin maido Mana da kadarorin mu, har yanzu case din hospital Bai qare ba sun kulle Sa'eed na shekaru da yawa Amman nayi Imani ba shi ya shigo da banned drugs da yayi amfani dashi mutane suka jigata ba it was all a setup, ka ceci martaban zuri'an mu dan Allah ka bankado sirrin Wanda ya Bata Mana suna"

" Insha Allah cariño nayi Miki alqawari duk Wanda ya aikata wannan danyen aikin sai na gurfanar dashi a gaban kotu, sai ya wulaqanta kaman Yanda ya wulaqanta 'dan uwana bazan Baki kunya ba, Amman idan komai ya qare sai ya rabu da matata Dan wallahi bazan bar Masa Saleeha ba"

Yana kaiwa Nan ya bude qofar ya fita dan bayison ma a sake tada maganar tunda yace yanaso to sai ya samu ko ta halin yaya ne, da gudu Leesa ta bishi a baya ba tare da tayi wa mamanta sallama ba,

Shan gaban shi tayi tana haki ta dago tana kallon shi ya zuba Mata Ido yaji yanzu Kuma da me tazo,
"Tafiya zakayi ka barni Bayan kasan bani da Wanda zai maida ni gida?"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now