chapter 19

232 32 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

19👯

Shigewar ta dakin shi tayi ta dudduba har cikin toilet wayam babu shi babu alamun shi ta fito sai faman tura Baki takeyi, ta qarasa wurin momy taja kujera ta zauna tayi shiruu dan tana 'danjin nauyin tambayar ta inda Sa'ood yake,

Murmushi momy tayi tace 'yammata babu gaisuwa ne? Ko dan baki samu mutumin naki bane kike fushi damu?

Murmushin Yaqe tayi tace "good morning momy"

"Morning my dear kin tashi lafiya"

A taqaice ta amsa da " Qlau, Dan Allah Ina ya Sa'ood ya Shiga ne? Na Shiga wurin shi ban same ba"

"Yanzun Nan ya fita ki duba wurin mamanku ko Zaki same shi"

Ai ko 2 minutes Bata qara ba ta fita ta saka a ranta yau idan ba kabari ya Shiga ba sai ya tsaya ya saurare ta dan tun shekaran Jiya yake Mata wasa da hankali sai yace ta jira shi Bari yana zuwa, to haka zata qaraci zamanta har ta gaji Bai zo din ba,

Saida Sa'eed yayi wanka ya shirya fess cikin army green suit sannan suka fito tare da Zarah Yana baza qamshi, parlor suka fita momy tayi Masa Allah ya Sanya albarka tayi Masa addu'an NASARA Akan aikin da zai fara dan yau zai fara Shiga office dinshi a asibiti,

Har mota Zarah ta mishi rakiya da kayan barcin ta ba tare da lullubi ba, ya Shiga passenger seat ya zauna Yana jiran zuwan Sa'ood su tafi,

Da qyar ya samu Sumayya ta rabu dashi ya fito, ya barta a part din mamanmu sai kuka takeyi Dan Kai tsaye Bayan ta Gama zazzage masa sirrin cikin ta yace shi bayi ciki,

Yana hango Zarah a jikin motar ya daure fuska kaman tunda yake a duniya Bai taba dariya ba, ya qarasa wurin da take tsaye suna magana da Sa'eed yace "Kee"

Da sauri ta juyo tana kallon shi
"Good morning ya Sa'ood" ta fada cikin sanyin murya,

" Kin wuce ciki ne ko saina tattaka ki a Nan wurin!"

Sidin_sidin Zarah ta wuce ciki don mugun tsoron shi takeyi, ta rasa Yaya akayi halinsu ya banbanta da Sa'eed dinta gashi kaman su daya Amman yanayi da halin kowa daban daban, tabbas KAMA DA WANE BATA WANE don tsauri irin na Sa'ood kaman wani qanin mala'ika,

ta kusan shigewa ya daga murya yace "Kuma na dawo na same ki da shigan arna kiga Yanda zanyi dake"

Zagawa yayi ya Shiga driver seat sannan ya tada motan aka wangale musu tangamemen gate din ya zugi motan da gudu, sunyi nisa da tafiya Sa'eed ya juyo Yana kallon kayan jikin shi,

Yana sanye da v neck shirt da jeans ya sha facing cap kunnen shi toshe da earpiece, zare daya Sa'eed yayi Yanda zai jishi da kyau yayi saurin mayarwa, bayi son Jin mitan Sa'eed yasan maganar Daya ce he doesn't look presentable,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now