chapter 28

244 34 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

28👯
Qoqarin bude qofar motan tayi taji shi a rufe, ta juya tana kallon Sa'ood dake kwance jikin seat idanuwan sa a lumshe, kwabe fuska tayi kaman zatayi kuka tace
"Ka bude min na fita Dan Allah"

Still idanun sa a rufe yace "idan Kika fita Ina zakije?"
"Nima ban sani ba kawai ka bude min na fita"

"shhhh please sleep bani son hayaniya'

" Ni wallahi bazan iya kwana a mota ba, yanzu idan safiya tayi mutane suka zo suka ganmu a haka fa"

Tashi yayi ya zauna yace "ok yanzu kin yarda mu tafi Kenan"

Gyada mishi Kai tayi, ya gyara seat dinshi hade da kunna motan yayi reverse suka ci gaba da tafiya, har sun danyi nisa tace "nifa bazan koma wancan gidan ba"

Baice da ita komai ba ya sake reverse ya juya Kan motan suka koma hanyar hotel,
"Wallahi fa ni bazan kwana a hotel ba ka barni na tafi kawai"

A hasale Sa'ood yaja wani wawan burki ya yunquro kaman zai shaqe ta Yana zare Mata manyan idanuwan shi,
"Kinsan Allah zanci Miki mutunci niba bawan ki bane da Zaki dinga juyani Yanda Kika so, ki kalli lokaci 12 harda 'yan kai Amman kin Hana ni barci kin saka ni galantoyi a Kan titi wallahi ki Shiga hankalin ki dani"

Ya sake zugan motan da 'dan iskan gudu suka Kama hanyar gida duk da haka bakin Leesa bai mutu ba sai qananun maganganu takeyi Yana Jin ta Amman Bai ce Mata komai ba, da abun ya ishe shi ne ya dauki kwalin tissue paper ya wurge ta dashi,

"Kai,kai,Kai! Me na maka da zaka ci Zali na?"

"So nakeyi kina maganar da qarfi saboda Ina Jin abinda kike fada"

" Amman ai ban Kira sunan ka ba ko?"
" Kima Kira ki ga Yanda zan dagargaza Miki baki"

Yamutsa fuska tayi cikin qunquni tace "wa ma zai Kira sunan ka, suna babu fasali Wai sakhh...sakhod Allah da nine aka saka min wannan sunan sai na yanka rago na canza"

Girgiza Kai kawai Sa'ood yayi ya fita harqan ta idan ba haka ba yasan Haleesa zata iya maidashi qaramin mahaukaci idan ya biye Mata, suna Shiga cikin gidan ya bada umarni wa Mai gadi ya rufe gate kada ya Bari kowa ya fita sannan yayi parking motan ya fita ya barta a ciki,

**********

Yana zaune a saman gadon ita Kuma ta kifa kanta da jikin gadon tana kuka Mai tsuma zuciya, dago jajeyen idanun ta Nabeela tayi ta kalli Idris shima gaba Daya a dame yake,

"Amor ba na fada maka ba? Duk abinda aka saka Masa Rana indai da Rai sai yazo, gashi yanzu lokacin alqawarin da ka dauka yayi dole ka cika shi, idan wani abun ya same ka ni da yara na bamusan Yaya zamuyi ba, idan ka miqa kanka ga hukuma zamuyi rayuwan qunci da kadaici cikin Mailafiya family,"

KAMA DA WANE....(Completed)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu