chapter 34

219 39 10
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Musmayya, Ummi Zariya, Aisha bello, Hussaina Maijama'a and Fatima Muhammad*
*Wannan shafin naku ne Kuna sharhi Yanda ya Kamata💞 GRACIAS🙏🏼❤️*

34👯
I..I mean a matsayin 'dan uwan ki kaman Yanda kike son Idris Nima kina so na haka?"

Murmushi tayi ta qara jaddada mishi " I don't like you ya Sa'ood"

Wani Abu kaman mashi yaji ya cakke shi a zuciyar sa, a wannan matsayin ma Haleesa ta qishi Ina ace ya bude Mata sirrin zuciyar shi? Bazai iya jure rejection daga wurin ta ba he better hide his feelings kada sabon dake tsakanin su ma ya rasa shi,

"Amman daga jiya zuwa yau na fara canza ra'ayi na a kanka, maybe idan na ci gaba da zama tare dakai zan tantance whether to like you or not, Amman bani da tabbacin hakan gaskiya"

Ya bude Baki zaiyi magana waiter ya qaraso da abincin su ya jere musu shi, ganin kaman Yana bata mishi lokaci Kuma ya lura rabin attention dinshi na wurin Leesa yasa shi saurin bata rai a kausashe yace

"Kai malam kayi sauri ka Gama abinda ke gaban ka ka bamu wuri" kafin ya bar wurin har Leesa ta saka spoon ta fara cin abincin ta,

Wannan lokacin a nitse take ci Dan Bata son abinda zai Bata kwalliyan ta, a tsanake Sa'ood yake qare Mata kallo she is eating like a queen today, dukda kiciniyar tattare hannun rigan ta da takeyi Amman Saida ya samu Daman Shiga cikin bowl din porridge din da take sha,

"Ya Rabb!! Duk iya qoqarina Saida wannan abun ya Bata min Kaya gashi ni bazan ci ba"

Miqa Mata nashi plate din yayi Wanda yake dauke da kalan abinci daban harda plate din da suke side duk ya tura Mata gaban ta yace "ga wa'innan kici" Yana gyara zama hade da tallafe fuskar shi da tafukan hannayen shi biyu, kallo kawai yake bin ta dashi ta zamo mishi kamar TV komai na Haleesa birgeshi yakeyi sai faman daddage Baki takeyi tana saka abincin saman harshen ta kada ya Bata Mata Jan baki,

A haka ta Gama cin abincin ta Sa'ood baici komai ba Bayan kallon ta ya saka ta wanke hannun rigan ta da ya baci a sink sannan suka bar restaurant din suka sake komawa mall din da suka fito lokacin an Gama packaging kayan su ya bada card dinshi suka cire kudin su sannan aka saka musu a mota sukayi gaba,

Nan ma wani hanya daban suka sake daukan ba Wanda zai maida su asibiti ba, cikin NASARAWA GRA suka Isa gate din wani qaton gida ganin haduwan shi yasa shakku ya darsu a zuciyar Leesa sosai 'kode da gaska sayar dani zaiyi?' ta tambayi kanta tana duba reaction din Sa'ood,

Fuskar shi a sake take Yana marmarin haduwa da abokin shi ya tura a sanar ma maigidan zuwan sa, Leesa kuwa a tunanin ta murnar zai Saida ita yakeyi a take cikin ta ya fara kuka ta tsorata sosai ta rasa qoqarin guduwa zatayi ne ko Kuma tambayar sad abinda ya kawo su zatayi? A haka har mutumin ya fito da kansa kafin ya qaraso Sa'ood ya fita daga cikin motar suna dariyan farinciki sukayi buddy's hug,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now