chapter 17

231 38 19
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Wannan shafin naku ne 'yan uwana not related by blood but by a strong bond that cannot be separated 💞

*Fatima batula(Mrs balarabe)*
*Yar Umma*
*Fatima shu'aib*
*Matar Soja*
*Nimcy sarauta*
Jinjina gareku marubutan qwarai 👍🏼

17👯
"Me zakayi dashi?"
Ta tambaya tana binshi da wani irin kallo,

"Na roqe ki Haleesa dan Allah ki bani na gani, dan Allah ki taimake ni ki taimaki rayuwa ta please"

Ganin Yanda ya marairaice yasa tasan akwai wani Abu a qasa, a iya saninta Sa'ood dan fashi ne Kuma shugaba ta fada Mata sarqan su gold ne mai tsada, ta yuyu Yana so ya qwace ya siyar ne kaman Yanda yake yi ma sauran mutane Kuma wannan necklace din shi kadai ne abin da ya rage Mata Wanda zai iya sada ta da iyayen ta na gaskiya,

Cire sarqan tayi daga wuyan ta, ta zare pendant din jiki ta dunqule a hannun ta na hagu sannan ta miqa mishi zallan chain din yayi saurin karba Yana qare Masa kallo,
" Haka sarqan yake babu wani Abu a jikin sa?"

Gyada Kai tayi tace " eh haka uwar goyo na ta bani shi"

Sauqe numfashi yayi ya miqa Mata chain din ta karba sannan ya wuce cikin daki Yana Jin ana kiraye kirayen sallah, ya dauko first aid box ya zauna Yana tunani, Yaya ma za'ayi wannan yarinyar ta kasance Sarwa?

Ya yarda tana Kama da dady aliyyu tun ranar da ya fara ganin ta Kuma shekarun ta daya da Sarwa sannan sunan ta daya da Haleesa, Amman Ai su biyu ne ita Kuma ita daya Kuma bata taba ambatan tana da twin sister ba saidai qanwa, a iya sanin shi mamanmu Bata sake aifan wata yarinya ba Bayan su,

Yana zaune Yana tunani ta shigo ta zauna dan nesa dashi sannan ta dauki cotton wool ta zuba spirit a kai Dan taga haka Mai chemist yake yi idan mutane sunji ciwo, ta Kai hannun ta saitin fuskar shi zata fara goge Masa a dan firgice ya dago Yana kallon ta,

Wai qoqarin taba shi fa take da sauri ya ja baya, ai shi dazu bisa kuskure ya kusan taba ta shine ita kuma zatayi Masa na gangan?
"Ki bari kawai zan iya da kaina" ya fada hade da karban audugan hannun ta Yana goge jinin fuskar shi,

Kaman daga sama yaji muryar ta tana tambayar "Mai yasa dazu ka damu da kaga sarqan wuya na?"

Bai dago ba yace "saboda na dauka na Sarwa ne"

"Wacece Kuma sarwa? Yaya za'ayi sarqan ta yazo wuya na?"

" Qanwata ce da Kuma matata"
" Ban gane ba itan guda nawa ne Haka da har take da matsayi biyu a wurin ka?"

Dan dagowa yayi cikin gajiya da tambayoyin ta yace
"Ai kuwa ba Zaki taba ganewa ba Dan ba abinda ya shafe ki bane, na riga na fada Miki Sarwa qanne na ne twins da Haleesa da Saleeha amman ke ba a cikin Mailafiya family kike ba shiyasa baki San abin da ya faru da su ba kuma ba Zaki sani ba"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now