chapter 36

217 39 7
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Double post*💃🏻💃🏻

*Wannan shafin naku ne*
*Ummu abee, maman medo, mUzEE, zee merhdi, Maryam milo, teema & maman Yusrah*
*Thanks for the love* 💞💞💞

36👯
8:05

Suna zazzaune a babban parlon baba alhaji daga iyaye zuwa Kan su Haleesa kowa Saida aka Tara harda wa'inda Basu rayuwa cikin Mailafiya mansion, Bayan an Gama jawabai da gabatar da juna, baba alhaji ya sake fashin baqi Akan qaddarar da ta afku musu tun daga farko sannan duk Wanda yake da wani magana jawabi ko Jan kunne aka Basu dama sukayi, daga qarshe ya zamo turn din mamanmu ne saboda abubuwan da suka faru ma ita sukafi illa

" Babu abinda zance yanzu tunda komai ya daidaita alhamdulillah, saidai tabbas ba wani Abu ne ya jawo duk wanna tashin hankali da hatsaniyar ba Bayan laifukan Sa'eed da Kuma ya Aliyyu tabbas Rai ba qaramin Abu bane wurin ubangiji, shi ya halitta shi Kuma ya kiyaye shi yayi Hani da salwantar dashi idan ba a Kan hakki na Sharia ba,

bani da kokwanto Akan abortion din suka dinga yi ne ya jefa mu cikin bala'i ya jawo rarrabuwan kawunan mu Kuma ya jefa mu cikin wahala qiyayya ya 'darsu cikin zuqatan mu, yanzu dai tunda komai ya wuce Ina fatan abinda ya faru a baya zai zamo izna a gare mu da masu tasowa Nan gaba Yanda bama cikin mu ba ko wani Wanda muka sani ne muka ga ya kauce ma Sharia ya dauki hanyar Saba ma Allah zamu dakatar dashi sannan mu nusar dashi, ubangiji Allah ya qara Mana hadin Kai Yanda ya hada fuskokin mu a Nan ya sake hada fuskokin mu haka a gidan aljannah" kalmar "ameen" ne ya dauki sauti parlon daga Nan Kuma kowa yayi shiru baba alhaji yaci gaba da cewa

"To Mun gode ma Allah yanzu gashi Mun dawo cikin gidan mu zamuci gaba da rayuwa a matsayin iyali guda daya fatan zamu ci gaba da samun hadin Kai da fahimtan juna kaman lokacin baya, yaran da kwanan nan suka Gama makaranta suna buqatar aiki za'a bawa kowanne matsayin da ya dace cikin companies dinmu,

yanzu asibiti da gidan marayu ne kawai suka rage a hannun hukuma Kuma insha Allah Suma Nan ba da jimawa ba Allah zai tona asirin Wanda yayi wa Sa'eedu insha Allah sai ya tozarta a idon duniya kaman Yanda ya tozarta shi ya tozarta mu gaba daya Allah ya isar Mana yabi Mana kadin mu ya qasqantar da wannan azzalumin"

Tunda baba alhaji ya fara magana Nabeela ta saka kuka tana tayi ma Idris alamu Dan bazata jure wannan kwashe albarkan da suke ma mijinta ba da wuya dandazon mutanen Nan suce ameen Kuma Bai karbu ba,

Idris kuwa tsoro ya Hana shi magana Yana so ya fada musu shine Mai wannan laifin Amman Yana Jin nauyin su da tsoro harda kunya ma kuwa, kallon mamanmu yakeyi hankalin ta a kwance yake Yana tunanin Yanda zaiyi breaking heart dinta idan ya fadi wannan abun,

Ganin mutane zasu fara watsewa yasa Nabeela tayi zubur ta miqe da qarfi tace "idan ba zaka fada musu ba wallahi ni Zan fada"

A take gaba Daya attention din mutane ya dawo kanta kowa Yana so yaji menene take cewa zata fada, shima Idris din tashi yayi ya tsaya Yana rarraba Ido ganin duk cikin su Babu Wanda yayi magana yasa baba alhaji yace "wani Abu ne Zaki fada 'yar Nan"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now