page ....1....

512 34 2
                                    

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

🏵🏵🏵
...1...2....

"Wlh kinji na rantse ki cikata min kudina,haka kawai kufah matannan shegen san banza ne daku,an fadamiki kyauta nake saka man keke napep din ni?"
Karyar da kai tayi cikin halin tausayi,yayinda take miki masa kudi daya kuma hannunnata tana tafe da cikin dayake jikinta,sai haki takeyi muryarta tana fita da kyar.
"Dan allah bawan allah kayi hakuri,wlh kam nasani kacemin naira dari uku ne,amma dan allah ka taimaka mini,kaga naira dari biyarce dani,zuwa naira dari biyu da hamsin,komawa ma haka,wlh dan babu yadda zanyi ne shiyasa nake neman ragi "
"Ba wani nan aikin banza,zaki nuna kaman wata a bar tausayi,to ina mijinnaki da ya kawoki asibitin mana ko ni namiki cikin dazan ji tausayinki,tsabar son banzane yasa kuke fakewa da abin tausayu kuna cutarmu,ga zoben zinare a hannunki amma kuma kina neman ragin naira hamsin"
Suna cikin ja'injane duk sun cika bakin asibitin da surutu,gashi dama said masifa yake kan gari ya gari akan naira hamsin din sa.
Sunkuyar dakai Sumayyah tayi abin duniya ya isheta,babu abinda takeyi sai kokarin mayar da hawayen dayake cikin idonta,muryar wata mata ce ta saka ta dagowa dan kaman tagane muryar.
"Salmah!!"
Shine sunan data fada cikin firgici,itama a nata bangaren cewa tayi "sumayyah".
Ganin sun tsaya suna kallon juna tundaga fadin suna babu wacce tayi magana ne yasa mai keke napep yin gyaran murya yana kara burka keken.
"Malama yadai ko ke zaki biya mata naira hamsin din,dan naga kaman kin san ta koh"
Kallonsa salam tayi tareda cirowa naira dari biyar a cikin jakarta ta mika masa.
Karba yayi babu ko kunya yayi gaba yana washe baki jin ance ya rike sauran sanjin.
Bayan ya bacewa ganin sune salma ta maida idonta kan salma,fuskarta dauke tabb da alamar tambaya,suna hada idon sumayyah tayi saurin sunkuyar da kai tana mai hafiye wani karamin yawu daya tsaya mata a makogaro.
Saurin wucewa tayi zata shiga asibitin salma ta riko tsohon hijabin dayake jikinta,juyowa tayi tana kallon salman domin sauraron wace irin tambaya zata iyo mata,kaman kuwa tashiga cikin zuciyar salman,jitayi tambayar ta dokin dodon kunnen ta bammm.
"Mai nake gani haka "golden girl" ohh yanzu kam ma ai kawai nace sumayyah,dan babu wani gopden a tare da ke,sumayyah mai nake gani haka a rayuwarki iyeee mai nene haka,yaushe haka ta faru banda masaniya iyeeh?"
Ihuuu sumayyah ta fasawa salma mai tsu ma zuciya,wanda dama ta dade tana tarashi a cikin ranta na tsawon lokaci,kakarewa muryarta take tareda fara haki tana rike cikin dayake jikinta.
Saurin kamata salma tayi tareda nufar hanyar wajen da motarta take,dakyar ta samu ta sakata a gidan baya tareda jan motar zuwa cikin asibitin ta nufi hanyar maternity ward.
Tana zuwa wasu nurse suka zo kawo mata agaji zuwa cikin ward din da sauri.
Cike ciken fike aka fara ,yayinda masu shigar da report suka ce said mijinta yazo kafin zasu tabata,dan jini take bukata da gaggawa kasancewar bata cin abun gina jiki jinin ta yayi kasa sosai.
Saida salma tayi musu jan ido kafin suka je inda gadonta yake,hakan ma saida ta bada kudi bayan na jinin data bayar a saka mata.
A zaune take a gaban sumayyah wacce take kwance jini yana bin hanya zuwa cikin jikinta,tafi kusan awa biyu a zaune kafin jinin yakare har sannan bacci takeyi kaman ta mutu,daga gani kaman ta dade bata samu bacci mai nutsuwa ba irin na lokacin.
Hannun sumayyah dayake hannunta ne taji ya motsa alamar ta farka,bude idonta tayi akan fuskar salman wadda itama kallonnata takeyi.
Yunkurin tashi take kokarin yi salma ta dagatar da ita,
"Ahh ki kwanta sumayyah kinga jikinki babu karfi sosai"
Jijjiga kai sumayyah tayi tareda cewa,
"Ahah salma babu komai,ai inaga rabon da naji karfin jikina irin na yau ma har na manta,nagode da abinda kikamin allah ya saka miki"
"Haba sumayyah menene na yimin wannan godiyar kaman ban sanki ba,babu komai ,kiyi hakuri da tambayar danayi miki,dan nasan ita ta sakaki shiga wannan halin"
"Ahah salma ba tambayar ki ce ta sakani wannan halin ba,hasalima ke taimakona kikayi,koda banaso amma baki labarin abinda yafaru dama zan baki,dan kin cancanta ki sani din,wanda bai cancanta bama babu abinda bai saniba,hatta ga cikin gari labarina ya zaga ko ina,wlh salma da badon dan dayake cikina ba wanda nake tunanin shikadai yaragemin da tuni na hallaka kaina a lokacin da babu wanda yasani,kullum idan rana ta futo kafin zuwa ta fadi saina girbi abinda na shuka yafi cikin kwando,hakika abubuwa da dama sun faru bayan rabuwarmu salma.
Ke kam kinji dadi da kikayi amafani da damarki da lokacinki yadda ya dace,ki tafi karatunki yadda iyayenki suka ce bayan mungama secondary,nikuwa fah ga inda na tsinci kaina salma,cikin halin kaico da kuma nadama,hmmmm yanzu dai kafin muje ko ina kiji abinda yafaru,dan bani ruwa na sha tukunna"
Tashi salam tayi cikin sanyin jikin ta mikomata ruwan da ta bukata,tana cikin shan ruwanne wata nurse ta shigo tana rubuce rubuce,
"Madam mun duba ba haihuwa zakiyi ba da dan saura tukunna,saidai gaskiya kina bukatar kulawa,domin daga ke har dan cikinki kuna cikin hadari,yakamata ki dunga kula sosai,leda biyu samu saka miki na jini,inshaallah gobe idan zamu saka miki dayar da safe,dan haka dole said kin kwana tukunna,akwai allurar dazaki karba zuwa nan da shabiyun dare"
Na'am sukayi mata da bayanin nata,tareda yimata Godiya ta fita.
Kallon agogon hannunta salma tayi tareda cewa,
"Toh ga shi Har la'asar ta kusa amma babu wanda yazo sumayyah,mijinnaki ya tafi aikine?,yakamata zuwa yanzu wanj yazo daga gidan,ko baki fada musu bane?"
Murmushin takaici sumayyah tayi tareda jijjiga kai,daga nan bata sake cewa komai ba.
Kallon salma tayi tareda cewa,
"Karki ta kura kanki salma yakamata ki koma gida dan za'a iya nemanki,ohhh ni na manta ban tambayrki bama,mai kika zoyi a asibiti,har yanzu kina gidane ko kinyi aure?"
Dariya salma tayi tareda cewa,
"Ohh sorry Ni ban fadamiki bama,wlh na mantane saboda ganin halin da kike ciki,yau shekarata daya da dawowa daga Egypt,muka hadu da wani engineer sunansa Emran,yanzu haka ma gwajin genotype nazoyi saura wata daya auren inshaallah"
Murmushi sumayyah tayi tareda cewa,
"Gaskiya nayi miki murna salma sosai,allah yasa gidan zamanki ne,ubangiji allah yabada zaman lafiya"
"Ameen sumayyah nagode sosai da addu'a rki,ke ma allah yasa kifi haka jin dadi a gidan da kike"
"Uhm salma karki ce haka,ki tsaya kiji abinda na aikata tukunna,dan nasan kinajin abinda nayi bazaki kara jin tausayina ba,guduna zakiyi kaman yanda sauran sukemin,hmmmm ina cikin tsaka mai wuyah sosai,nazama tamkar muziya a cikin alummah,abinda nayi allah kadai nake fata ya dubeni,ya jarabceni koya kankaremin zunubina a nan gaba"
"Kai sumayyah kidaina fadan haka,komai yayi tsanani maganin sa allah ,inshaallah watarana said labari,babu abinda allah baya yafewa saidai idan baka rokeshi ba".
"Haka ne kam salma"
"Ahh kaman inada number hajiya mama a wayana bari na kirata na fada mata halin da ake ciki,koma mai nene bai kamata ki zauna ke kadai a cikin wannan halin ba sumayyah"
Saurin cafke wayar sumayyah tayi tareda mayar da ita bayanta tana jijjiga wa salma kai,idonta tabb cike da kwallah wacce take xuba a hankali,cikin rawar murya ta fara cewa,
"Ahah salma karki fada kowa halin danake ciki,idan kika fada ma ba iya raina ne kadai zai baciba harda naki salma,bakisan halin da ake ciki bane shiyasa,amma abin ya wuce yanda kike tunani sosai,banu wanda zai kalleki bare amsa miki a kaff cikin a halina matukar sunana kika kira,koda kuwa cewa kikayi na mutu babu wanda zai kalleki,salma na dade da zama gawa a ciikin a halina tun ranar da aka dauramin aure,dan haka a wajensu zancen matacciya zaki yi musu bawai wata yar adam mai raiba,ki manta da wannan taimakon da kike kokarin yimin na kiran dangina,dangin mijina ma idan kika tambayesu,su sunsan ni rayayyiyace amma ko karuwa bankaita bakin jini a wajen suba.
Idan kina bukatar tafiya gida yakamata ki tafi salma,taimakon dakikayimini ma bansan da wanne baki zan godemiki ba,saidai bace allah yakara miki wadata a zuciya dakuma na duniya mafi alkhairi"
Zuwa lokacin salma tafara kaduwa da halin da sumayyah take ciki,dan yamzu ta fara ganin abin yafi karfin wasa,ya wuce yanda take tsammani.
Karar wayarta ne yakatse sumayyah da yin magamarta,mikowa salma wayarta tayi domin ta amsa kiran daya shigo,sunan mahaifiyar ta ne ya fito akan screen din ,ta shi tayi ta fita waje domin amsa kiran.
Batafi mintuna shida ba sai gata ta dawo,kallon sumayyah tayi kafin tace,
"Na fadawa ummah cewar zan kwana a nan,in anjima zata aiko driver da bargo da abinci da kuma sauran abin amafani,duk da ma gobe sukace zasu sallameki,amma duk da haka zamu bukaci wani abun"
Har sumayyah tabude baki zatace wani abu salma tayi saurin katseta tareda cewa,
"Karki ce komai sumayyah babu komai zaman taren da akayine ya zawo haka,allah yakara yimana muwafaqah a rayuwa."
Suna zaune suna tadi wanda mamar salma ta aiko da kaya ya shigo,gaishesu yayi tareda ajiye kayan ya tafi,harda flask da ruwan zafi dakuma kayan shayi ta aiko musu,tashi salma tayi ta hada mata shayi mai kauri ta bata,hannunta har rawa yake ta karba ta kafa kai kwatt kwatt sai kofin ta ajiye tana maida numfashi.
Abinci ma da aka zuba saida ta shanye cikin plate,tana gama wa sai gata ta shi tana zagayawa a tsakar dakin,duk abinda takeyi salma kallon ta takeyi da mamaki da kuma tausayi,wai sumayyah da tasani ce ta zama haka,lallai duniya abar tsoroce.
Gyaran murya salma tayi bayan sun gama sallahr la'asar tace,
"Sumayyah in a so ki bani labarin abinda ya faru bayan bana nan indai hakan bazai dameki ba,dan abubuwa da dama sun daure min kai sosai"
"Uhmm duk abin akwai nauyi amma inshaallah yanzu zan sanar dake abinda nasani a takaice wanda ya faru tun rabuwarmu dake sanda mukayi candy"
...........komai yafarane a shekarar 2016 lokacin da muka gama makarantar secondary lokacin nake kan tashena na tauraruwar zamani lokacin dana shiga jami'a lokacin da nake ganin kowa ba kowa ba lokacin danake bin zuciyata fiyeda bin iyayena lokacin danake ganin babu abinda yagagareni ko bazan samuba,saidai kash abinda ban sani ba shine..........komai na lokacinne,sannan idan ya tafi baya dawowa,tafiya yake yabar wawa da cizon yatsa kaman yanda ya barni a ciki........kaico nah!!!!!!!!!

KAICO NAHWhere stories live. Discover now