Page...30...

207 17 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...30....


"Hakane abbah abinda sumayyah ta fada gaskiya ne,zan aureta a karo na biyu tunda ban samu aurenta a karo na farko ba,na amince da aurenta"
"Ahmad dagaske kake abinda kace na ka shirya auren sumayyah?"
"Eh abbah da gaske nake yi,na shirya"
Duk da yanda muryarsa da jikinsa yake rawa amma yana iya kokarinsa ganin abbah bai fahimci halin daya ke cikiba.
Ganin abin zai kai ga abbah ya ganene yasashi saurin yi masa sallama ya fito daga dakim da sauri,sauke ajiyar zuciya yayi ganim ya bar wajen shashen abban.
"Tabbas sumayyah kinci galaba akan kudurinki,kinsaka iyayena tursasani saboda kimsan ni ba irin ki bane mai bin zabin zuciyarsa,amma babu komai shigarki gidan bashine yake nuna cewar zan miki abinda kike so ba,ina nan akan bakana na kintata miki matukar kika nuna dani zaki zauna a inuwa daya"
Duk maganar dayake cikin cije baki da bacin rai yake yinta,ko hajiya mama bayyi wa sallama ba ya fice daga gidan,dan ji yake duk gidan ya ishashi saboda sumayyah tana cikin gidan.
Bayan fitarsa daga gidanne abbah ya nufi sashen hajiya mama dan shaida mata abinda yake faruwa.
"Maman yara ganin abinnan nake kaman wasa"
"Kaman ya kenan"
"Nakira garinnan Ahmad akan zancen yanda sumayyah take cewa shita zaba a matsayin miji,abin mamaki said cemin yayi wai ya san zancen kuma shima ya amince"
"Oh to kasan sha'anin yara,inaga sun hadu har sunyi maganar bamu saniba mana"
"Umuhm Ni ban yarda ba,daga yanda yake bada amsar kaman tursasashi akayi,wanda nasan bazai wuce aikin ramma,inkuwa haka ne zan sake bincika lamarin,bai kamata duk abinda yafa nan kuma a sake yiwa yaro auren doleba gaskiya"
"To kardai kace haka,in har da dagaske itace ta tursasashi bai kamata ka hanashi yimata biyayya ba,a garin gyara kar a je a bata kuma koh,muda muke neman wannan ma tasan menene biyayya bai kamata shi mu hanashi yi ba,kawai muyi fatan Allah yasa hakane mafi alkhairi"
"Hmm shikenan amma tunda ba sonta yake ba,ina nan akan bakana na hukuncinta,idan ta kuskura tayi wani abin tashin hankalin zata gamu da fushina batacce "
"A samu wasu suje su fadawa su ramma cewar na bashi ita,tunda sun dage sai sun kuntatawa yaro ai shikenan,kuma nasaka nan da sati biyu za'a daura auren inshaallah sannan ban yarda da wani taroba,suje can yaya Usman ya daura musu auren,dan nikam bazan daura ba gaskiya"
"Haba abban yara miyasa kake hakane,nikam wannan rikonnaka yana damuna wlh,karfah a garin wannan abin dakake watarana kaje kayi abinda zai dameka fah"
"Kinga banni,indai akan sha'anin yarinyar nan ne to kibar ma bata wani yawun bakinki akai"
"To shikenan Allah ya shige mana gaba,zan fadawa su hajara itada matar yaya Usman yah Hajjah suje su fada musu inshaallah"
Daga haka abbah yabar dakin hajiya maman cikin bacin rai.
Duk abinda ake tattaunawa sumayyah tanajin su daga bandakin hajiya maman,dan taahiga gyara mata kenan bayan tagama abinci tana sauri kar magriba tayi saiga abbah ya shigo dakin.
Dafe bakinta tayi dan kartayi wani numfashi da abban zai jiyo,abinne yake tayi mata yawo akai,tabbas zancen abbah gaskiyane,tursasa Ahmad akayi akan ya aureta,kuma tasan aikin iyah ne da inna ramma,wai metake shirin jawowa kamtane,gashi abbah yagane turasasashi akayi,tasam bazai daina fushi ta ita yanzu nan kusaba.
Maganar hajiya mama ce ta katseta da tunanin datakeyi,
"Kekuma bazaki fito daga bandakinba anan zaki kwana,nasan ai kinji dai mai yace da kunneki koh,babu batun a maimaitamiki,nikaina nasan kina da dalili na aurensa,amma rashin dacewar hakan a wajen mutane tafi yawa,wani sabon abin maganar zaki sake debowa idam bakiyi taka tsantsan,Allah dai ya gyara kawai.
I'm baki gyaramin ba ma ki barshi kawai,dan yanzu zan shiga bandakin nayi alwala,gobema ai ranace.
Haka sumayyah ta nufi nata dakin jikinta kaman babu laka,da tana daukan abin kadan amma da alama yana shirin fin karfinta gaskiya.
Bayan fitar Ahmad daga gidan su sumayyah masallaci ya wuce dan har an fara kiran sallah,daga nan kuma ya wuce gidansa.
Tun kafin yasaka kafarsa a cikin gidan gabansa yafara bugawa,shin mai zai cewa maryam,duk da tanada hakuri amma abin ba karami bane,gashi dole ya sanar da ita gudun karta ji a wani wake daban,haushin sumayyah ne yasake kamashi ganij duk a dalilintane komai yake faruwa ai.
A wajen dining ya hangota tana shirya abinci dare,jikinta sanye da wani farin yadi anyi masa ado da zare marron,bakaramin kyau tayi masa daga wajen ba,mace mai tsafta biyayya da kuma saukin kai,tunanin hakanne ya fice a cikin ransa daya tuna kwana nan sumayyah zata shigo gidan ta maidashi duhu kirin.
Isa yayi wajen ta a hankali duk bata kula daahi ba har ya jagaye hannuwansa a kunkuminta,murmushi tayi amma har sannan bata dago da kalleshi ba,
"Mekika dafane naji har yanzu kitchen bai daina kamshi ba uhm"
"Abune mai dadi,ba'a fada saikaci kaji menene"
"Okay to zauna muci,idan mun gama akwai maganar da nake so muyi dake"
"To"
Daga haka babu wanda yasake cewa komai a cikin su har maryam ta zuba musu abincin suka fara ci.
Tunda suke cin abincin ta kulada da Ahmad ba sosai yake kaiwa abincin bakinsa ba kaman ma hankalin sa gabadaya baya wajen sa yana can wata uwa duniya,itadai maryam batace dashi komai ba duk da tana kulada abinda yakeyi,.
Bayan sun gama cim abincin takai kwanukan kitchen ne ta dawo da zauna a kusada shi a falon,jawota yayi jikinsa yana cusa hancinsa cikin gashinta wanda ta iyo gyaransa da rana.
Ita dai tayi shuru tana jinsa har ya gama abinda yake kafin ya dago idonsa yana kallonta,itama kallon nasa idon take tana karance abinda ke cikin idanuwan nansa,koma menene tasan ba karamine ba.
Hannunta takai kan fuskarsa gefen kumatunsa,wanda jin hakan yasa yasake narkewa akan hanunna ta,
"Menene yafaru kake boyeminne,har yasaka cikin wanann halin?"
"Maryam ina so ki fahimceni idan kika ji abinda zance dan Allah,inna tasakani akan na auri sumayyah,wanda nan da sati biyu za'a daura auren,banaso nayi shuru harkiji a bakin wasu kiji haushi,sanann banaso nayi ta wata hanya hanya akan zancen,ke kanki kinsan mai ya faru tsakanina da sumayyah kuma kinsan mai yake faruwa yanzu,banason zama inuwa daya da ita saidai babu yanda zanyi,dan haka banason kiyi wani abun dazaki shiga harkarta a gidannan,kibarta ta zauna har ta gaji ta tafi"
Duk da abin ya doki maryam a cikin zuciyarta amma hakan bai hana ta danne ba tace masa Allah ya sanya alkhairi.
Tashi tayi zata bar wajen zuwa dakinta,dan duk abinda zai fada a yanzu kunnuwanta bazasu juri ji ba ko kadan.
Kama hannunta yayi lokacim data mike zata tashi a wajen
"Maryam yanaga kim tashi,shin baki yarda dani bane da kuma abinda na fada?"
"Bawai ban yarda dakai bane,saidai a yanzu ina matukar bukatar na kansance ni kadai,kabani lokaci nikadai a yanzu,karka hanani"
Kallon idonta yayi sai a yanxu ya kulada da damuwar dake kwance a idonta,wanda da bai kulaba lokacin dayake mata bayani.
Sakin hannunta yayi a hankali kafim yace,
"Shikenan zan barki ke kadai kiyi tunanin,amma please karki saka Tunani a ranki sosai har ya dameki"
Daga masa kai kawai tayi,dan maganar ma yanzu idan tace zatayi bazata iya ba.
Yana kallon ta har ta shige dakinta ta jawo kofar ta saka mata key.
Bandaki ta nufah da gudu,tana zuwa ta rushe da kukan datayi ta kokarin rikewa a wajen Ahmad lokacin daya fada mata auren da zayyi.
"Shikenan mai waje yazo,nasan sumayyah zaki karbi Ahmad dinki a wajena,tunda dama kaman riko na karba,duk zamana a auciyarsa bazai kai yamda kike zuciyarsa ba,mai nayiwa su inna ramma zasu min haka,shin na tab a gazawa ne,kokuma kulawar danake bawa Ahmad ne tayi karanci da har zaku sakashi kara aure,hakanma kawata wacce take masoyiya a gareshi da farko........"
Daga haka maryam tacigaba da kukan ta tana surutai na zafin kishi.
Washagari da maryam ta fito har ta huce da zancen da Ahmad yayi mata,dan da wuri ta gama breakfast dinta ta koma daki,duk da har sannan bata son ganin Ahmad din .
Ana sauran sati daya bikin sumayyan amma babu alamar za'ayi biki,kowa harkar gabansa yake,matan yayunta kuwa babu wanda ta leko,dan haushinta sukeji zata je ta takurawa maryam,kowa abin yake fada kenan,dan ko kusa maryam tafi karbuwa a ransu fiyeda ita,dan dama ita tun kafin hakan ya faru ba shiga shirginsu take ba.
Maryam ta wartsake daga fushin datakeyi dan musamman su anty Maimuna da humaira suka je mata yini suka fada mata abinda yake faruwa,da wanda aka yi harda wanda ba ayi bama,dan dama haushin sumayyan sukeji,musamman ma humaira datake taya mijinta yaki,dan tun kafin ta shigo gidan tasan mai yake faruwa.
"Ke maryam wlh ki fitar da wani bakin ciki aranki,dan sumayyah yanda take a wajen Ahmad ko karya ma tafita daraja,ni bansan ma mai yasaka ta nacewa sai ta aureshiba,nasan duk bai wuce na ta wargaza farincikinku ba,to wlh ki kulada mijinki hannun bibbiyu,kinuna mata kedashi mutu ka raba ne,nan gari nan bari"
"Kai anty Maimuna nasan sumayyah bazatayi nufin wani mungun abuba,inaga akwai wani dalili dai"
"Hmm zaki ce haka mana,ni dama yarinyar nan bataiminba,tun zuwana gidansu fah dama nagane batada kirki,dan kinga wani kallo data bini dashi lokacin dana je gidan karon farko?,hmm kiyi wasa to kizama abin tausayi a hannunta,dan kekanki kinsan a rashinta Ahmad ya aureki,abu kadan zatayi ta kwaceshi a wajenki"
"Wlh kam anty maryam,niduk da bansan ta ba amma inajin labarim ta wajen mu'azzam da irin tsiyar datakeyi Koyaushe,ni nan ina bayanki karki yadda ta kwacemiki miji,bamuce kiyi wani mungun abuba amma ki mallakeshi da kissah,yanda bazata taba samun damar karbarsa ba,zan kawomiki wasu magunguna ki jarrabasu sosai da sosai sai yakara macewa a kanki dan so "
"To duk naji abinda kuka ce,magunguna kam dama ina amfani dasu saidai nakara,zan yi kokarin ganin na mallakeshi bai fada tarkonta ba,danni kaina nasan sumayyah ba saukakkar mutum bace"
"Hmm dama duk wanda zai santa ai a bayanki yake,badai saura sati daya auren ba ,saima tazo ta shiga wannan kurkukun dakin,kekuma tana ganinki a tamfatsetsen daki hmmm ,wlh zanso naga yanda zatayi a gidanann.
"Naji mu'azzam ma yana cewa wai Ahmad yace bazai kama mata wani gidan ba kam,yace a dakin yara zao sakata idan bazata zauna ba ita tasani"
"Hmm zamu gani ai wanda bai ji bari ba zai ji hoho,humairah ai maganinta kenan,ba ita sarkin girman kai ba zata san an fita iyawa,wlh nidama dan hajiyah mama ne shiyasa nake raga mata,amma da gangan zan dunga zuwa gidanann nayi baje mata rashin mutunci yanda naga dama,babu mamar tata ai bare ta gani"
Daga haka suka saka dari ya suka tafa,basu suka bar gidan maryam din ba sai yamma,suna ta koya mata yanda zata rike gidanta a hannunta ita kadai.

Toh fah.

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now