Page ....52....End

215 7 0
                                    

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

 END

🏵🏵🏵

...52....

"Hmm inna inkin ganta bazaki ganeta ba yanzu,saboda halin dasuje ciki ne yasa dole na dawo garin.

Shema'u tayi aure ta auri mai kudi,saidai karshe takare da ganin ha ulai.

Dan dan kungiyar shan jinine,haka ya kulleta a gidansa na tsawon wani lokaci,daga baya ya yanke mata dukka nononta yayi tsafi dasu,ita kanta dakyar tafito daga gidan.

Tana nan kirjina danata babu maraba,sai wahala datake sha,dan jijiyoyin wajen har yanxu in ciwon yatashi kaman zata mutu.

Shikuwa mutari ya hau Motar kwadayi an saukeshi shima a tashar walakanci,wata hajiya ya aura ma kudi,sunata yawon kasashe,ashe ciwon kanjamau ne da ita dakuma ciwon sanyi,yana nan a gida yana fama da ciwo.

Kwananna ma yayi rigister na karbar magani.

Dukkansu idan kika gansu yanzu bazaki ganesu ba,abinda sukayi ya koma kansu,gidan da mijin shema'u ya siya wa innna shi aka sayar akayi kudin maganin shema'u"

Dan tasabar girgiza da zancen dauda sumayyah batasan lokacinda ta tashi tsayeba.

Sun dad'e suna magana tana bashi baki da kuma cewa ya dage da kuladasu yan uwansane.sannan ta ciro check ta rubuta masa na taimako,tareda cewa yafara zuwa aiki gobe.

Ba karamin godiya dauda yayu mata ba,dan kam bazai manta da wannan taimakon ba har karshen rayuwarsa.

Watanni sun tafi cikin sumayyah ya tsufah sosai,dakyar take turashi,duk wanda yaganta sai ya sake ganinta,yanzu dolenta ta daina zuwa aiki.

Hajiiya mama taturo mata mai yimata dan aikace aikace,dan anyi mata warning a asibiti kan ta daina aiki mai yawa,sannan haihuwa tana zuwa suyi gaggawar komawa asibiti.

Hakan kuwa akayi,nakuda tana kamata suka tafi asibitin,Allah ya taimaketa Ahmad yana gida,dan tun akan maryam yanzu yayi hankali,ba barinta a gida ita kadai,musamman da itama tanda matsalar.

Dakin labour aka shiga da ita,tun suna saka ran zata haihu da kanta abu amma yagagara,har saida daga karshe suka bawa Ahmad takarda yayi sign nayi mata aiki,hannunsa yana rawa kasa yin sign din yayi,dan gani yake kaman itama zai rasata idan suka shiga da ita,saida aka dan karfafa masa gwiwa tukunna ya karba yayi.

Yana rubutawa kuwa yabisu cikin dakin tiyatar,a cewarsa yafison da dunga ganin mai suke,kyaleshi dr yayu shima yasaka kaya aka shiga dashi..

Akan idonsa tsaga cikin aka fito da jaririya ta farko,dayarma tana motsi a cikinta,kafin itama aka fito da ita,lafiyayyayu dasu sai kuka suke,murna da farinciki Ahmad sai murmushi yake,nuna masa cikin mahaifarta sukayi wamda yayi baki da alamar ciwo,

"Zamu cire mahaifarta idam bazaka damuba,saboda barinta a cikin jikinta zai iya jawomata camcer nan gaba,domim kwayoyim da'aka bata da farko dunyi tasiri sosai"

Shuru Ahmad yayi kafin daga baya yace su cire kawai,abune daya yariga ya faru,wannan din ma allah yayi musu albarka.

Duk abinda akeyi sumayyah bata saniba,saidai yanada tabbacin bazata fushi da zabinsa ba

KAICO NAHWhere stories live. Discover now