Page.....21......

182 22 3
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

🏵🏵🏵
...21....

Safa da marwa ta fara a tsakar dakin tana sakar zuci,tunda tadawo gida bata taba tunanin ahmad ba,amma yanzu daga fadar sunansa har taji wani abu a ranta,mai hakan yake nufi toh,mai yasa takejin hakan a ranta,abinda tunda take bata taba jiba,duk da tasan ba so bane amma kuma wani abune daban,kodan kiyayyar data nuna masa ne takejin rashin dadin hakan.
Inna Ramma ce mahaifiyar Ahmad ta fado mata a ranta,yanda matar ta nuna mata so lokacin datake karama,dakuma irin hallaccinta gareta,kwata kwata baza'a hadata da inna mahaifiyar mutari ba,gaskiya ta zalunci kanta dayawa,a ina zata samu Ahmad har ta nemi gafarar abinda tayi masa kuwa.
Haka sumayyah ta wuni ranar Ahmad yana fado mata a rai,kaman wanda aka sakata tunashi koyaushe,gashi kuma tana son zuwa gidan inna ramma kodan taga ya take.
Washagari bayan ta gama abincin safe ta gyara sashen harda dakin hajiyah mama,wanda ta hana Muhibba gyaramata yanzu ita takeyi.
Dakinta ta koma tayi wanka,bata dade a bandakin ba ta fito,dan yanzu bata wankan ruwan zafin sosai tunda kwarin jikinta ya dawo,saidai ciwon mara wani lokacin yakan tashi mata idan tayi aiki ko kuma motsa jiki dayawa.
Atampa ta dauka daga cikin kayanta da kuma hijabi tasaka ko mai bata shafa ba,dan tun watanta uku a gidan mutari man shafawarta ya kare,shikuwa bai siya mata ba.
Yanzu ko gyale ta daina sakawa ballantana kayan ado,dan yanzu bahu su kokadan a ranta kaman am cire mata su tass.
Dakin hajiyah mama ta nufa bayan ta gama shiryawa,domin tayi mata sallama zataje gidan su inna Ramma da iya.
Abin mamaki yabawa hajiyah mama ,ganin da ko zuwa gidan tayi saitaga dama ta gaisheta,amma wai itace mai zuwa gidanta yanzu,wanda rabonta da gidan har ta manta.
Bata nuna mata komai ba saima cewa da tayi ta gaisheta.
Amsawa sumayyah tayi tareda nufar gidan.
Har driver ya taso zai rakata ta dakatar dashi tareda cewa zata tafi da kafarta,tunda basu da dan nisa sosai.
Tafiya take a hankali tana karewa anguwar tasu kallo har ta zo kofar gidan,gabanta ne yafadi rass,sai a sannan ma tafara tunanin to mai tazoyi,tunda bata zo gidan ba sai yanzu da taki dansu,gaskiya hakan da kunya,babu yanda ta iya dai haka ta bankada kofar gidan ta shiga bakinta dauke da sallama.
Iyah ce ta amsa wacce ta fito daga bandaki.
Koda bata nuna sosai ba amma daga ganinta kasan tayi Mamakin ganin sumayyah a gidannsu,duk da labari yazo musu na mutuwar aurennata.bata sake cewa komai ba sai idonta data daga tana karewa gidan kallo,ko ba a fadaba tasan Ahmad ne yagyara gidan,yasha tiles dakuma femti mai kyau,kasancewar babu yara a gidan sai su kadai ko ina fess dashi.
Inna Ramma ce ta fito daga daki tareda kallon sumayyah.
"Lahh Mai Sunan uwata kece a gidan,yah su hajiyan toh"
"Lafiya kalau inna ,ina wuni ya gidan"
"Gida alhamdulillah,zoki zauna mana toh ko ruwa kisha,sannumki dazuwa,da tsiya zan miki amma tunda an tuna dani shikenan"
Kunya ce takama sumayyan ganin innah ramma bata riketa a zuciyarta ba duk da kiyyayyar data nunawa jininta,lallai inna ramma mutumce wacce samunta sai am shirya,Maryam tayi sa'ar suruka ba kadan ba.
Zama tayi a dan tsugunne taki sakin jikinta,musamman da iyah tun daga gaisuwa bata sake kukala ba,inna ramma ce ta dawo da jug a hannunta da kofi ta tsiyanya mata ruwan juice.
Kin daukar kofin sumayyah tayi,gashi taki cewa komai sai sunkuyar dakai da tayi.
"Ahh yanzu Uwata ni kike kunya kuma yau ko iya,mufah ba baki bane kinsani,kisaki jikinki kinji kaman kina gida,indan dan abinda yafarune ai ya riga ya wuce da dadewa"
Kaman dama sumayyah jira take tafashe da kuka harda toshe baki.
Kukanta tasha ta koshi,tun inna ramma tana rarrashinta har ta tayi shiru itama iyah tafara saka baki.
"Haba yannan banzata abin har ya kai haka a wajenki ba,kidaina kuka haka yariga ya wuce kinji"
"Ahah iya koda ya wuce a wajen kowa bazai taba wucewa a wajena ba,abin ya riga yazama wani tabo wanda ya mannu a kan zuciyata,sanann bazai taba gogewa ba,dan allah na rokeku ku yafemin abinda nayi a muku a iya sanina dakuma wanda ban saniba,hakika nasan nayi kuskure dayawa a rayuwata,har iyayena ban bariba bare wasu,nasan nimai bakin jinice da kuma bakin fenti a fuskar mutane da dama"
"Yi shuru ya isa haka kidaina fadan haka kinji,komai yawuce bamu rikeki da komai ba kinji"
"Nasan bazaku rikeni ba inna,saboda hakan halinkune da dattaku da kirki,amma ni dole zan riki kaina,koda naso bawa kaina farinciki bazan iya ba,horona ne zama cikin wanann halin har na koma ga ubangijina,nasan hallayata basu da kyau ko kadan,takaicina daya shine yanda nakasa sanij hakan sai lokacin da lokaci ya kuremin...."
"Kidaina fadan haka sumayyah,kidana hakkin bawa kanki farinciki anan gaba koda ba yanzu ba,sannan shawarar dazan baki wajen gyara mai kikayi shine,"_ta inda aka hau a komai tanan ake sauka,sannan ta inda matsala ta fara dole sai anje inda tafara kafin a gyarata_
Wannan shine shawarar dazan baki kije kiyi nazari akai sosai,idan harkika samo amsar duk wuyarta to nikuma a sanann nasan kin gane laifinki,kuma sai inda karfina yakare wajen taimakonki sumayyah"
Rarrafawa sumayyah tayi tareda rugume iyah kaman zata maidata cikin ta,dariya abin yabawa inna ramma sosai.
Dago da fuskar sumayyah iyah tayi tareda yin murmushi irinna dattako,
"Iyeee to wannan hawayen fah,so kike ki bata fuskar nunawar"
Murmushi sumayyah tayi tana share hawayen idonta tace,
"Iya kenan,fuska kam yanzu ai tazama dameji,lokacin baya yariga ya wuce,yanzu wanann fuskar sumayyah bazawara ce ba fuskar summy golden girl ba"
Duk da tana magana tana murmushi amma daga muryarta zaka san maganar ta doki zuciyarta sosai.
"Kakice haka uwata,mace bata kwantai sannan bata daina yayi saidai idan ita taso hakan,dan haka ki rugumi sabuwar sumayyan dakika tsinci kanki a ciki kuma ki koyi sonta da kuma zama da ita kafin kowa yasota yakuma ji sha'awar zama da ita "
Jijjiga kai tayi tareda nutsuwa tana daukar darasin dasuke nata daya bayan daya,tabbbas ziwanta wajennnasu bakaramin dadi tajiba,musamman yanda suka sake da ita kaman babu abinda ya faru.
Sumayyah ta dade a gidan kamar karta tafi,dan sai wasa da dariya akeyi,sai bayan tayi sallahr azahar ne kafin ta dau hijabinta yafa tareda yimusu sallama.
Har ta kai bakin kofa inna ramma ta biyota tareda bata sabulai dakuma turaruka masu kamshin dadi,da farko kin karba tayi saida inna ramma taji haushi tukunna ta karba tana godiya.
"Nagode Inna Allah yasaka da alkhairi,sannan dan Allah inna kutayani bawa Ahmad hakurin abinda yafaru,duk nasan naso kaina idan nace a fada masa,saboda ba alkhairi ne a gareshi ya tuna dawata halitta mai kama dani ba amma dan Allah kuce yayafemin domin Allah,ina bukatar yafiyar wanda na zalunta domin nasamu sassauci sannan na koyi rungumar sabuwar rayuwata kuma........"
"Yi Shiru haka na fahimceki,kuma zan miki iya kokarina,kedai ki dunga kwantar da hankalin ki kinji,inshaallah komai zai wuce"
"Nagode inna Allah yayiwa rayuwa albarka"
Daga haka sumayyah tafita daga gidam ta nufi nasu gidan kamar kada ta tafi.
Tana isa tun daga bakin kofar falon ta jiyo muryar Anty Maimuna itada yah mu'azzam suna magana,tsayawa tayi domin jin mai za'a ce sosai,kuma da alama dukakansu ne a cikin falon harda hajiyah mama.
"Lallai mu'azzam yanzu babu ko kunya kake cewa an baka mata zu je godiya koh?"
"Haba anty Maimuna wace Kunya kuma yanzu ai andena irin wanann kunyar,ai kawai ku baje kafa kusha biki,kuma baki gantaba kyakykyawa da ita,duk cikin si yah naseer nafisu dacen kyakykyawar mata"
Duka anty Maimuna takai masa da pillow tareda cewa,
"Muhibba kinajin wanann yayannaki yana zagemu koh,kuma dan cin fuska a gaban idona,to kaman kayi da Hafsa sai na fada mata karta zo bikinka tayi zamanta ta huta"
"Ahah aunty Maimuna karkiyi min haka,idan anty hafsa bata zo ba ai biki bazayyi armashi ba,kinsam kuwa ita na ce ta iyomini kayan lefe daga can?"
"Iyee Wai Har haka abin ya matsone mu'azzam,kace biki dai ya kusa kawai"
"Hmm ki tsaya kallon ruwa mana,jiya fah takirani take cewa abbanta yace naturo manyana ni aka bawa,sanann yace bikin bazai wuce wata daya da kadan ba ,dan yagaji da ganinta a gida a zaune."
"Tab gwanda mufara shiri kenan,yau dinnan zan kira hafsa da su Nafi da Anty hajara akan maganar,ina kuwa Abokinnaka naga kwananan shiru baya lekowa tunda yaji sumayyah ta dawo gida"
Gaban sumayyah ne yafadi wacce take jin abinda suke cewa daga bayan kofa bayan taji an ambaci sunanta.
"Yana nan mana,ai shine gaba a kan hidimar shida maryam,dan tace ma ita zata shirya bangaren dinner a bar mata shi"
"Allah sarki maryam tana da kirki,kwanaki ai sukajemin da daddare mukayi fira suka tafi"
Muhibba ce tayi magana wanda tunda aka fara batace komai ba,
"Yah mu'azzam ya batun ankonmu nida amty sumayya kasan muna wuyanka fah "
"Eh naji,amma iya wanda zai je zanyiwa,nasan ita bazuwa zatayi ba koda nayi mata"
"Kobazata je ba yakamata kayi mata"
"Toh naji karki dameni kema"
Maganar ce ta isheta daji hakan yasa tasaka kai cikin falon,dukkan su daga kai sukayi suna kallomta bayan tayi sallama.
Daga sallamar bata sake kallonsu ba ta wuce inda hajiyah mama take zaune tana karanta Ahalari da glass a idonta,
"Ahh harkin dawo"
"Eh nadawo sunce suna gaisheki sosai"
Yah mu'azzam ne yafara tambayar ina taje,amma ko amsa masa batayi ba ta wuce sama dakinta.
......uhm miskilancin a jini yake,musamman da'aka fara samun kai.
Team din sumayyah......YASRIBA saiki fara comment su maman najwa da su maman husna yan ko ina ne.  Page din gaba za'a tsakuro gidan su mutari,koya kukace toh???
Ina yinku lodi lodi mutanena 😍😘😘😘😍😍😍😍



🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now