🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER
Wattpad:SAKHNA03
🏵🏵🏵
...19....Samun waje sumayyah tayi ta zauna a gefen gadon Muhibba tana karewa dakin kallo.
Ganin sa take tamkar yau ta fara shiga cikinsa,nata dakinne ya fado mata yanda ta kawata shi komai black da golden,saidai abin mamaki gidan aurenta kuma tamkar kurkuku haka yazo mata,kawar da tunanin gidan mutarin dayi a ranta,dan a yanzu babu abinda ta tsana kaman tuno rayuwar da tayi a gidan.
Muhibba ce ta fito daga bandaki tun dazu tana kallon sumayyah wacce ta lula cikin duniyar tunani.
Tafa hannunta tayi a gefen fuskarta wanda ya yasa sumayyah tayi firgit tana kallon muhibban.
"Hmm Wai yaushe zaki daina tunaninnan anty sumayya? Anyware ki tashi ki yi wankan kafin ruwan yah huce,dan da zafinsa sosai na hada miki"
Daga sumayyah tayi tareda yunkurawa ta tashi,bandakin ta nufa cikin tafiya a hankali kaman mai tsroron taka kasa har ta shige.
Sauke ajiyar zuciya Muhibba tayi ganin ta shige bandakin,a ranta tana mata addu'ar samun saukin lamarinta.
Fito mata da kayan bacci tayi daga cikin nata ta ajiye akan gadon tareda fita kitchen domin nemo mata abinda zata ci.
Dan Kay anta kam can aka barsu a falo tun sanda ta suma aka debeta zuwa asibiti babu wanda yabi ta kansu.
Lokacin da Muhibba ta dawo rike da tea mai zafi a hannunta sumayyah har ta gama wankan ta saka kayan da ta ciro mata.
Karbar shayin tayi tareda yiwa Muhibba godiya,har sanann muryarta tana dauke da kunyar muhibban,idan ta tuna abinda tayi mata a baya,kwata kwata bazata tuna lokacin da ta yiwa Muhibba wani abun kirki ba,daga hantara sai kuma zagi da kyara.
Amma yanzu ita tadauke ta a karkashinta take kulada ita,lallai tayi abubuwa da dama wanda tasan bazasu gogu a tarihi ba.
Tana cikin tunanin tana shan tea din Har ta games ta ajiye kofin,zuwa lokacin har gumi ya rufeta na dumin daya ratsata,gana wanka ga kuma na tea din .
Tabbas Muhibba ta taimaketa soaai,dan wannan tsamin jikin da take ji har ragu,ji takeyi kaman an dauke mata wani nauyi akan jikinta.
Murmushi Muhibba tayi na jin dadi ganin yar uwarta ta tana dawo hayyacinta ba kaman lokacin data zo gidan ba.
Daukar kofin tayi domin kaiwa kitchen,kafin ta dawo ma har sumayyah tayi bacci,dan har sannan maganin data sha a asibiti bai sauta ba.
.............sai kuma gobe.
Da safe buga pillown da muhibba takene ya tayar da sumayyah daga baccin da takeyi,dan kwata Kwata ta manta cakwakiyar da take ciki da kuma wacce take jiranta.
Firgit tayi ta tashi tana dube dube,dan har ta bude ido gani take kamar mafarki takeyi,da kadan kadan abinda ya faru jiya ya dawo cikin kanta.
Kallon Muhibba tayi kana tace,
"Muhibba karfe nawane yanzu,dan kamar hasken rana nake gani ta window"
"Eh hasken rana ne karfe sha dayane da minti arba'in"
"Iyee Har azahar ta kusa amma ina bacci?,ina abbah mai yace a wajen cin abinci,dan nasan yanada masaniyar cewar ina gidannan,lahh na manta yau weekend su yah mu'azzam da yah naseer har yanzu suna zuwa gidanann kuwa?"
"Kai aunty sumayyah wannan tambaya haka,ko gajiya bakya yi,dukkansu suan nan,kuma naji aban yana cewa wai family meeting yake kira kowa da kowa har da su baffah Usman,dan shima ma tun jiya da daddare suke waya dashi,kuma nasan bazai wuce akanki bane,dan jiya yah mu'azzam yafadaasa halin da'ake ciki"
Cikin sumayya ne yakara durar ruwa jin abinda yake aukuwa daga bakim Muhibba,dam hauka ita kuma tasau baki take ta bacci.
Saurin sakkowa tayi daga gadon tareda nufar bandaki da sauri.
Ruwa ta surka mai zafi kaman wanda Muhibba ta hada mata jiya ta shiga ciki,bayyi wani sanyi sosai ba ta fito saboda mazarin da jikinta yakeyi.
Kayan Muhibba ta dauka ta saka don nata bata dauko suba.
Doguwar rugace buba,dan a halin da take ciki tafi saurin sakawa,dan kwalin ta yafa tafice daga dakin zuwa kasa dakin hajiya mama.
Daga bakin kofar dakin tayi sallama kaman munafuka tana dan lekawa dakai a sunkuye,matar Yah naseer ce Anty Maimuna a zaune ita da Anty Nafi a kasan carfet din dakin,ita kuma hajiya mama tana bandaki.
Shigewa tayi ta zauna a gefensu tareda gaishesu daya bayan daya,abinda bata taba kenan ko a tarihi,dan tsakaninta dasu idan suka zo gidan kallone kawai,shidim bana arzikiba.
Da mamaki Antu Maimuna ta amsa gaisuwar,ita kuwa anty Nafi lokacin data amsa batayi mamaki ba,dan tafi kowa sanin gyaruwar sumayyan.
Tun daga gaisuwar bata sake cemusu komai ba,sai wasa da take da hannun rigar jikinta,Anty Nafi ce ma tayi mata ya jiki ta amsa a hankali,ita kuwa anty Maimuna shakkar yi mata magana ma takeyi.
Hajiyah mama ce ta fito daga bandaki tana share ruwan alwalar data iyo a fuskarta,dan wani wajen har sun fara kiran sallah.
"Lah bakin anguwar Sarakuna ne a gidan namu"
"Eh wlh hajiya mama"
Aunty Maimuna ta fada tana sunkuyar dakai na kunya.
"Toh yah gida da su farouq,yanzu kam sun dauke mana kafa an shiga makaranta koh?"
"Eh hajiyah,sai kuma muka ji abinda ya faru,Allah ya tsare na gaba"
"Ameen ya Allah,Ina maigidan naki ko bai isoba shidin"
"Ahah tare muka zo yana wajen su abbah da baffah usman"
"Ahh to madallah sannunku da zuwa,barina fara sallah"
Daga haka hajiyah mama tafara sallahr ta tareda juya musu baya,tana kallon sumayyah a zaune ta sunkuyar dakai amma bata kukata ba,sai ma yi tayi kaman bata san da ita a dakinba.
Abinne ya girgiza sumayyah,a zatonta zata samu sassauci a wajen hajiyah mama ashe ba haka bane.
Dan dama tasan hajiya mama tana da sanyin rai ,amma idan ta rike mutum a zuciya to fah sai anyi da gaske kafin da koma yanda take dashi.
Zuciyar sumayyah ce ta karye tareda sanyin jiki lokaci daya,ganin irin tsanar da aka mata jitake kaman kasa ta bude ta fada ciki ta huta kowama ya huta.
Tana nan zaune a wajen har su anty nafi suka tashi suka fita zuwa bagaren yaran gidan,hajiyah mama ma tagama sallahr ta tanafila har ta shiga ta farillah ta idar sumayyah bata ko motsa daga inda take ba.
Ta sunkiyar dakai tana aikin kukan zuci kaman wata mabaraciyah.
Hajiyah mama ce ta juyo ta kalleta tareda yin magana,
"Har yanzu baki tafi ba mai kike ana wajen tun dazu,ko yau dakinne yayi miki dadi har kikayi awa daya a cikinsa,ko jinya nake a gidanann bakya minti goma a inda nake kike tafiyarki,yau kuma babu wanda yace ki zauna har kikayi awa guda?"
Dagowa sumayyah tayi daga kukan da take tareda rarrafawa zuwa inda hajiya maman take zaune akan sallaya.
"Ma mm mm a..........."
"Kinga dakata,nasan mai zaki ce,cewa zaki ce kin tuba kinyi nadama,kuma nasan da kinyi nadamar,dan ga tanan akan fuskarki dakuma yanayinki,abinda baki samiba shine: abinda kike yi da ko zawo ayita zakinki ana aibata zafi nakeji,idan kika aibata wani ma zafi nakeji,dakikayi zabin kanki baki ko kula da halin dazan shiga ba,na tunanin banida ikon sanin wane hali zaki shiga shima zafi nakeji,lokacin dakika zo naga yanda kika koma na wahalar rayuwa shima zafi naji,sannan kallon da kowa yake miki a yanzu dakuma hukuncin da abbah yazartar akan ki shima nafiki jin zafinsa,ke iya na jiki zaki ji dakuma wamda zaki ji a zuciya,amma ni abin yana sukana sosai,yana min ciwo sosai,yanda bakowa yasan halin danake cikiba.
Saidai amma baby yanda zamyi sumayyah,kece kika siya da kudinki,kece kika saya mana nidake muke jin wannan zafin zuciyar,kece kika jawo mana duk abinda muke ji nidake.
Abinda nake so kisani shine bake kadai kike cikin kuncin nan ba harda ni a ciki,idan kinyi abinda zaki cire mu a ciki nidake to kin kyauta,idan kuma kikayi abinda zamu cigaba da jin wanann ukubar nan ma kekika saya mana.
Dukkan ku rabin jikinane hardake ban ware ba ,wannan abune daya zartu daga Allah na sosayyar danake muku,kuma bazan iya cirewa kaina ba.
Zan hankalina gaeki shine,nasan abbanku zai baki zabi nazama da kuma tafiya,sanann kowanne nada sharadi,fatana shine karki zabi sakeyin nesa dani daga wanda kikayi a baya,idan kuma bahaka ba duk abinda yasameni kiyi ta zargar kanki har karshen rayuwarki,dan banajin zan sake jure hukuncinku keda abbanku a karo na biyu.
Dan yafewa kuma nadade da yafemiki,koda ma ban rikeki ba,dana rikeki da abin sai yafi haka a rayuwarki,saidai hakan bashi yake saka na yarda dake ba,bazan shiga al'amuranki ba har sai naga yanayin rayuwarki tukunna,kuma sai naga shiryawarki da mahaifinki"
Zuwa lokacin muryar hajiyah mama ta fara rawa,da alama zuciyarta tafara karaya,da alama abinda take fitarwa sumayyan ya dade a zuciyarta tana kunce dashi a cikin zuciyarta,sai yanxu da ta samu dama take fitarmata dashi,
Duk maganar da hajiyah mama takeyi sumayyah kyam ta zuba mata ido tana nade abinda take fada a cikin kanta,mamaki danasani da kuma rashin sanin aninda yake faruwa da mahaifiyar tata tsawon rashin mutuncin datayi a rayuwarta su suka nuna akan fuskarta.
Fashewa tayi da kuka tareda kamkame mahifiyar tata lokacin da hajiya mama ta gama jawabinnata.
Tsawon lokaci da ta shiga cikin halin kunci take tunanin ita kadai ce ashe ba ita kadai ce ba,akwai mahaifiyarta wacce tafita jin abinda take jinma,tabbas wanda ya ha'inci uwarsa ku kirashi da marar arziki duniya da lahira,domin bai biyo ta hanyar neman raboba.
"Mammmaaaaaa wlh koda idan abbah yace zai amince na zauna a gidannan amma hukuncina shine kisa,wlh zan amince hajiya mama,zan amince kodan ki ga gawata ki yi mata bankwana cikin salama,da na tafi duniya na cigaba da ruguza zuciyarki,daga yanzu bana fatan nazamo mai sakaki hawaye a rayuwata,wanda zai sakaki ma sai inda karfina yakare"
"Shikenan Allah ya sassauta miki jarabawar rayuwarki"
"Ameen hajiyah mama,yanxu inajin koma miye zam jure sabodake wallahi a duniyar nan,koda kuwa rayuwa da mahaukacine zanyi indai shi kika zaba"
"Bana fatan hakan,da sannu Allah zai haskaka miki kema a rayuwa wata rana"
Shiru sumayyah tayi tana ajiyar zuciya,dan a yanzu jitake kashi tamanin na kuncinta an cireshi,tabbas samun fahimtar iyaye tafi komai bayan imani.
Daga haka suka share hawayen dayake hawayensu kowa yana mayar da zuciya.
Murmushi sumayyan ta yi wanda har cikin zuciyarta ya shiga,rabonta dayin irinsa har ta manta.
Muhibba ce ta shigo dakin bayan sumayyah ta mike zata kama hamyar wajen,
"Yawwa aunty sumayyah wai kuzo keda hajiyah mama ana kiranku a falon abbah"
Daga haka ta juya ta koma inda ta fito.
Waigawa sumayyah tayi ta kalli hajiyah mama wanda itama ita take kallo.
Daga mata kai hajiyah mama tayi alamar babu komai.
Tashi daya taji har cikin zuciyarta babu komai din kuwa,dan akwai wanda yamzu takejin ya tsaya mata a yakinnata,koda kuwa menene zai faru.
Ita jijjiga kan tayi tareda bin bayan Muhibba zuwa cikin falon abban,wanda ita dama tun dazu ta tafi.
.......Jinjina ga iyayen mu🙏🏼🙏🏼🙏🏼❤❤❤❤❤❤🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵

YOU ARE READING
KAICO NAH
ActionShin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bare na fada musu cewa duniya tayimin zafi..........?😓😓😓 Ina ganin na fita a wannan chakwakiyar ashe...