Page...41...

187 29 10
                                    

     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...41....





Haka sumayyah tayi zamanta ita kadai a gidan bayan su Ahmad sun tafi checkup din maryam.
Lokacin da hutunsu ya kare ta tattara ta koma makaranta.
Saidai inda aiki yake shine wajen biyan kudin makarantar ta na semester,kudin wajenta sunyi katt gashi batasan ma wazata fadawa damuwarta ba.
Koda wasa bazata bari salma ta saniba,dan jiya ma da sukayi waya da ita cewa tace mata ta biya kudin,Ahmad ne ya biyamata,abin yabawa salma mamaki amma ta danne,dan tsakanin mata da miji sai Allah.
Zirga zirga take a dakinnata tana kai kawo,ta ciji ya ttsa kokuma ta say ajiyar numfashi,gashi gobe za'a rufe biyan kudin,batada yanda zatayi,dan second semester ba wasa wajen biyan kudin.
Dabara ce ta fado mata da sauri ta suri hijabinta ta bar gidan,saida ta kulle kafin ta tafi,dan itace kadai a gidan daga ita sai mai gadi.
Anguwar yayarta anty nafi ta nufah,babu bata lokaci,kayanta na daki da basu shigaba zata sayar,dan bataga amfanin dazasu mata ba suna zaune.
Da sallama ta shiga gidan ta samu yarinyarta karama sultana tana wasa da kekenta.
Shafa kanta tayi tana murmushi,dan ita ina ga saninta da yarinyar bai fi sau biyuba.
"Ina mamanki sultana"
"Tana cici bacci takeyi"
Dariya maganar yarinya yabata kafin ta shigeta ta shiga falon.
A kan kujera ta samu anty nafin tana bacci yayinda dan ta karami mai sunan abbansu yana shan nono bata ma saniba.
Yaron sumayyah ta sure daga kanta aikuwa ya zuba uban ihu kaman ta sakashi a wutah

Zabura anty nafi tayi ta tashi dan ganin mai yake faruwa,kallon sumayyah tayi akan ta da yaron a hannunta yana ta ihu.
"Kefah bazaki sanjaba,daga zuwanki har kin zaburarmin da yaro,kuma bashida lafiya zazzabin hakori yakeyi"
"Wannna kuma shiyasani,yaro ya mannne sai shan nono yakeyi,kekuma kinata bacci,kun koyawa yara jarabar nono"
"Bari in kin haifi naki karki bashi kibarshi ya mutu"
Mikamata dan ta sumayyah tayi tareda zama akan kujerar gefenta.
"Anty nafi kinsan mai ya kawoni,zuwa nayi na saida kayana dayake wajenki,ina bukatar kudin"
"Sayarwa kuma sumayyah,kedah aka ajiye idan ya sanja miki gida ki debi kayanki,shine zaki sayar"
"Ni daya sanja min gida daya barnj bai dameni ba,hasalima nafison dakin danake yanzu,saboda yafi gefe ba mutane,nidai sayar dasu zanyi kuma yau,banga mai zasuyimin ba bayan ina bukatar kudin,in Allah yayi wataran nayi wanda suka fisuma,amma yanzu bana bukatarsu"
Ganin bazata yarda ba yasa anty nafi kyaleta tareda cewa za'a sayar da kayan to.
A ranar sumayyah ta matsa wutah saida aka nemo dillaliya aka yi ciniki tazo ta dauki kayan,itama da rawar jikinta ta siya kujerun ganin masu kyaune sosai,dayar ma ta dakin cewa tayi tazo ta karba a gida,dan sun fi daraja idan a cike suke.
Ita ba baki take ba bare tace zasuje su zauna akan ta,itakuwa zaman gado ma ya wadatar mata.
Ganin tsabar kudi cass a hannunta yasa anty nafi dafata tace,
"To an siyar da kaya mai kike ganin zakiyi dasu to,karki sasu a gaba ki kashe kizo kina cewa zaki saida na dakinki ma,hakan bai dace ga mace ba daga wani abu tasiyar kafin ta samu kudi"
Shuru sumayyah tayi kuma fah hakane abinda anty nafin ta fada.
"To mekike gani zanyi anty nafi"
"Ahh to ki zauna kiyi nazari dai koh".
Haka sumayyah ta dawo gida da niyyar gobe taje ta biya kudin makarantar ta,sannan kuma ta san abinda zatayi da kudin.

Bayan an fito daga aji suna zaune da kawarta take tambayarta shawarar sana'ar dazata fara.
"Uhm tunda dama course dinki yana da hadi da computer mai zai hana ki fara graphic da wasu abubuwan"
"Graphic kuma zai kace namiji"
"Hhhh lallai bakisan irin abubuwan nan ba iya mazane suke yin aikin,bakida labarin women organization center,kenan kuma macece ma mai wajen.
"Babu kalar kamfanonin da basayiwa aiki,kuma naji ma zata dwbi dalibai kwannan,harda irin su zanen atmpa sukeyi,decorations modeling,kwangilar gyaran gida na kayan daki,jewelries da abubuwa da yawa,duk bangaren dakike so zaki iya shiga.
Register kawai zakiyi,a matsayin mai koyo kokuma a matsayin mai'akaciyah,duk wanda kike so,wajen matane zallah"
"Yi Shiru na samu wajen zuwa kawai,a matsayi biyu zan shiga,akwai wani certificate danake dashi na koyon graphic danayi,makaranta nayi na shekara biyu duk da ban maida hankali ba amma nasan abubuwa dayawa,saboda aiki da computer hobby dina ne dama"
Idan nashiga kinga saina jona training ma'aikatansu nakara ganewa,hakan za'ayi kawai"
Suna gama lecture ranar sumayyah ta matsa mata sai ta rakata wajen,ta gida suka biya ta dauko takardunta suka wuce wajen.
Tun daga bakin wajen take karewa gun kallo,babu laifi ya tsaru kam,block block ne kowanne da abinda sukeyi,office din Ceo din suka shiga.
Office din mai kyaune sosai,duk am masa decoration,masu abu da abunsu.
Wata matace ta matso inda suke tareda cewa,
"Sannuku yan uwa damai zan taimaka muku"
"Munzo ganin CEO dinne"
"Tana meeting da wani kamfani,ku fadi abinda ya kawoku"
"Ahah wajen ta muka zo,zamu jirata idan ba damuwa"
Basu yi awa guda ba suna jiranta sai gata fito daga wajen meeting din.
Yar babbar matane tana dan kiba kadan,daga ganijta dama kaga marar zaman banza.
Wucewa office din tayi su sumayyah suka bita a baya,
"Sannunku da zuwa,mai yake tafe daku"
"Sunana sumayyah Abudulkadir Gobir,an fadamin labarin wajennan ne akan idan mutum yayi wani karatu akan sana'a za'a iya dauakrsa aiki koda basaida taakrdun gama makaranta ba.
Idan za'a taimaka inaso na nemi aikinne ma fara  kafin na gama makaranta saboda ina matse da bukatarsa"
Karbar file diin hannun sumayyan tayi ta duba sosai.
"Uhm kaman na san ki koh? Uhm golden girl koh"
Mamaki ne yakama sumayyah a ina ta santa to,saikuma taji wani iri tada ambaci sunan yanzu.
Yar dariya matar tayi tareda cewa,
"Karki damu,nasankine a makarantar dakika koyi wannan din,lokacin kina zuwa da motoci kala,sunana Hajiyah Aisha,bayan yayekune na bar wajen nima nazo na bude wannan wajen,dayake na samu tallafi dayawa kinga har inda nakai a cikin shakaru shida"
Sunkuyar dakai sumayyah tayi,dan ita kadai ta tuno tijarar datayi a wajen,na rashin mutunci dayiwa masu koyarwar rashin kunya,duk da bata tuno hajiya aisha n ba amma tunda taji bata manta ta ba tasan itama hadda ita a cikin wanda taciwa mutunci.
"Yana ga kinyi shiru,karki damu,duk da a lokacin kinada rawar kai amma kokarinki a wajen ya burgeni,musamman da kika tsaya saida kika zarce kowa a competition badan komai ba dan kar kowa ya fiki,kuma hakan ya taimakeki sosai.
"Uhm duk da haka hajiya amma abinda nayi ai ban kyautaba,tunda gani nake a sannan idan wani ya wiceni darajata tayi kasa,musamman danayi alwashi,kiyi hakuri hajiya wlh yanzu ba haka nakeba kuma....
"Shiit ya isa haka,ni waccer sumayyan ma da san samu nake son daukar aiki,wacce zata jajirce dan fito da darajarta,sannan bata wasa wajen bangaren abinda tasaka a gaba,amma duk da haka karki damu,nikaina nasan kin sauya,babu komai kizo gobe zamu miki interview,inta kama ma zan dauki nauyin ki sake koyon aikin,dan nima hadda karuwata,dama ina neman ma'aikata ta bangaren computer da graphic din,yanzu ma wani aiki aka bani na design din wani company,da za'a yi musu na advertising"
"Nagode nagode sosai hajiya inshaallah zanzo goben,kuma zaki samenj mai jajircewa"
"Uhm ba komai,yanzu zan baki paper da duk abubuwan  da ake bukata zaki mallaka,saboda kinsan wajennan mu sai a hankali,bai bunkasa sosai ba"
"Bakomai zan siya duk abinda ake bukata inshaallah"
Daga haka sumayyah suka fito daga wajen sai murnar nasarar da tayi takeyi
Paper tafara dubawa tun a hanya,dole sai ta siya computer sannan dakuma wasu sample din pen da wasu abubuwan daban daban.
"Duk wannan ba matsala bane bazasu gagara ba,aiki gani nan gareka "
Washagari kaman yanda ta fada kuwa taje interview,batasha wahalar amsawa ba,dan kwana tayi tana nazari akan abubuwan sosai,yanzu babu abinda tasaka a gaba daga karatunta sai kuma aikin dabatayi tunanin samu ba sai gashi ta samu.
Ana gobe su maryam zasu dawo,aiki sosai yayiwa sumayyah yawa,ga gyaran gidan dazatayi ga kuma aikinta sannan ga karatu.
Duk da yanxu ta saba da jirga jirga amma saida taji a jikinta.
Washagari dayake juma'ace bata je makata ba,iya wajen aikin taje,shima basuda wasu Abubuwa sosai,musamman nasu block din aikinsu zuwa zuwa ne.
Saidai ita kanta sumayyah takan karbar wani dan aiki yanzu ba dole saina aikinsu ba tayi.
Tana dawowa karfe sha biyu,ta,shiga kitchen tayi musu girki,inzasu ci to,in bazasu ciba ma su suka sani.
Sai yamma likis kafin suka shigo gidan,tana zaune a tsakar gidan da computer a gabanta,tayi wankanta,gefe kuma da cup na lemo tana sha.
Dama irin rayuwar data keso kenan,yanzu tafarajin tana dawo hayyacinta,babu yan gulma babu tunanin yazatayi ta samu abu kaxa,karatunta yana tafiya normal yayinda a wajen aiki ko wata batayiba amma ta samu cigaba sosai,musamman da suke shiri da hajiya aisha din.
Karar budewar get taji mota tashigo gidan,dan daga kai tayi tacikin glass di idonta tana ganin shigowarsu.
Yah mu'azzam ne yake tuka motar sai Ahmad a gefensa maryam kuma tana baya.
Saukar da kanta tayi daga haka,har suka gama fitowa daga motar suka zo zasu wuce ciki.
"Daga kanta tayi tareda semusu,
Sannunku ta dawow" daga haka ta dauki system dinta da lemon ta wuce cikin gidan zuwa dakinta.
Mamakin yah mu'azzam yayi ganin bata ko gaisheshi ba,sukuwa su Ahmad hakan ba sabon abu bane dan su suka fara shareta ita take share sun.
Fitowa tayi daga dakin bayan ta ajiye system din.
Lokacin dukkansu suna ciki,iya yah mu'azzam ne a falon,
"Ina wuni yah mu'azzam"
"Sai yanzu kika ga damar gaisheni kuma"
Ga mamakinsa bata bashi hakuri ba sannan bata tanka masa ba,sai ma cigaba da ajiye abinci data yi a kan dinning.
Tana cikin yi su maryam suka fito suma suka zauna,zuzzuba musu tafarayi,da bazata zubawa Ahmad amma kuma saita zuba din.
Ga Mamakin ta kuwa da Maryam sai gani sukayi yasak cokali ya fara ci,zaro ido sukayi itada maryam din,shikuwa yayi kaman bai gansu ba suka cigaba da magana da yah mu'azzam wanda bai san me ake cikiba.
Zaman wajenne ya ishata kawai ta tashi tabar wajen,dan tanada abinyi ba tsayawa jin hirasu ba da bai shafeta ba.

    Yasriba yanzu kin farajin dadi? Su ummu najwa kuwa Ahmad yabada su fah,dasu ummu husna.
    Jinjina ga daukakin masoyan littafinnan dukka ina matukar godiya sosai da bada hadin kanku.









🏵*sadi-sakhna ce*🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now