Page ...43...

273 25 2
                                        


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...43....



Ahmad ne ya tashi ya bita da farko,dan ganin mai yake faruwa.
Daga baya jin aman yaki tsayawa yasa sumayyah itama ta bi bayansu da sauri.
A bakin kofar bandakin ta samu ahmad,itakuma maryam tana gaban sink.
Karisawa tayi a hankali wajen,Matsawa Ahmad yayi kusanta ya riketa,dan gabadaya ta galabaita sosai,dan ma tayi sa'a aman ya dan tsaya.
Shiga bandakin sumayyah tayi ta wanke inda maryam tayi aman,dan yaune karonta na farko shigowar dakim maryam din,ba laifi yana da kyau kam,dan yayi kusan ukun dakinta a girma,ban kuma kayan dake ciki.
Lokacin data fito daga bandakin har ya taimaka mata ta saka wani kayan,har sannan jikinta a mace yake,sai maida numfashi takeyi.
Kallon sumayyah yayi tareda cewa,
"Jeki dakina ki daukomin key din mota,dazu na ajiyeshi a bed side drawer,inaga gwanda mutafi asibiti"
Amsa wa sumayyah tayi tareda barin dakin ta nufi dauko masa key.
Fitowa yayi daga dakin yana tallafe da ita,yayinda iyah ta tashi ta isa inda suke tana cewa,
"Ikon Allah a abin har yakai hakane ne,mai ya sametane,ko dama batada lafiyah"
"Ahah iyah lafiyanta kalau,saidai kwanannan yanayin halayyarta sai a hankali,yanzu dai ku zauna a gida bari muje mu dawo a dubata"
"To shikenan Allah ya sawwaka"
Summayah ce ta mika masa key din tareda fadin Allah ya kiyaye.
Daga haka suka shiga mota sai asiviti,aka bar iyah sumayyah dakuma iyha a gidan.
Shuru shuru basu dawo ba har wajen yamma,iyah sai mita take itakam zata tafi gida,shibai kira yafadi lafiya ba shikuma bai dawoba,duk tabi ta daga hankalin ta,sai sumayyah ce ma take kwantar mata da hankali wani lokacin.
Karar motarsu ne yasa su sumayyah kallon bakin get din,dan dama a harabar wajen suke zaune,sumayyah ta debowa iyah kayan makulashe tana ta sha.
Bayan Ahmad ya fito daga motar saida ya zagaya bangaren inda maryam take bude mata,har wani kaffah kaffa yake kaman mai tsoro kar iska ta rabeta.
A hankali suke tafiya sai wani narkewa take tana karyar dakai kaman kadangaruwa.
Tun kafin su iso wajen hakoran Ahmad sukeyiwa su sumayyah welcome,kaman an masa albishir da aljanna.
Yana karisowa ya rugume iyah wacce take zaune,abin mamaki ya bata saidai ta gagara cewa komai.
"Iyah!! Maryam cikine da itah ashe har tsawon wata hudu amma bamu saniba,kibar datayi da kuma rashin jin dadi ashe cikine da ita iyah"
"Mashaallah mashaallah mashaallah kai wannan abin dadi. Har yaushe,ashe rabon yana tareda mu ma bamu sani ba,kai wannan abin murna ne,kumafah yaci ace mun kula,kasan abinka da mutum baya kawowa zai faru shiyasa.
Allah ya dayyaba ya albarka ce shi,maza rakata ta huta a yi mata dan abinda zata iya ci"
Jikin iyah har rawa yake,banda Ahmad daya gagara rufe bakinsa dan murna,ita kuwa maryam sai wani kara hade rai take tana shagwabewa.
Ita dai sumayyah ta tsaya tana kallon ikon Allah.
Cikin hanzari Ahmad ya ciro wayarsa yafara kiran mutane yana fadamusu ya samu karuwar ciki,shima kwannan zai ga gudan jininsa in Allah ya yadda.
Kowa sai murna yake tayashi,da kuma fatan alkhairi.
Ta shi Ahmad yayi zai raka iyah gida,wacce takeji kaman ta zauna ta kula da maryam din,
"Sumayyah zan raka iyah gida magriba tayi,kafinnan ki kulada ita kan dawo,idan wani abune tace miki tana sha'awa kiyi mata,ina nan dawo,inkuma babu kiyimin waya sai na taho dashi"
Kallon mamaki takeyiwa Ahmad din tareda daga masa kanta,dam ta gagara yin magana ba,cikin abinda baifi minti biyar ba duk sun fita hayyacinsu saboda labarin cikin,wannan da zai ga wani abu waishi gata idan ya zo duniya.
Bayan sun fita sumayyah juyawa tayi ta kalli maryam wacce take zaune akan kujera ta dora daya kan daya,fuskarnan babu alamar fara'ah.
"Me kike so a dafa miki wanda zaki iya ci"
"Babu komai bana bukatar komai,in ma ina bukata ba yanzu ba,sanda nake so zan fada miki"
Duk maganar cikin basarwa takeyi kaman anayi mata dole,sumayyah tace "dankari" a ranta,ita kuma haka ta koma,ikon Allah mai yanda yaso.
Daga nan itama sumayyan bata ce mata komai ba ta wuce dakinta,dama itama ba mace bace bai bin mutum yanda yake so,shiyasa tashige dakinta ta barta a wajen ita kadai.
Can Bayan magriba sumayyah ta gama sallahr magriba taji ana kwankwasa kofar ta,ganin shuru ne yasa shi shigowa cikin dakim yana kallonta,ita kuma addu'a ta gama tana shafawa.
"Ka maida iyah lafiyah,yah inna ramman take"
Dan tsuke fuska yayi kafin yace,
"Keda nace kikulada maryam kafin na dawo shine kika barta ita kadai tana ta amai babu kowa a kusada ita,kina nan dakinki hakan ma kin rufo kofa,taya zakijita toh.
Sannan na tambayeta mai taci tacemin wai babu komai meyasa toh"
"Na tambayeta mai take some ci tacemin babu komai ,shiyasa na tafi"
"Kuma dan tace babu komai bazaki lallameta ta fadamiki ba,kinsan fah ba ita kadai bace yanxu,dole zatayi wasu abubuwan ta da batayi,sannan kuma nace ki kirani inda wani abun"
Yanzu cikin daga murya yake maganar wanda hakan ya tunzura sumayyan itama.
"Haba Ahmad!! Wai miye ma abin laifin a cikine danna tafi,na tambayeta tacemin babu komai,to ya kakeso nayi,sannan kafi kowa sanin yanzu ta sanja fiyeda da,kuma kasanni farin sani banida hakuri da juriyar lallamin wani,ni bazaka min uzuri a yanda nake ba.
Kuma maryam ai ba yarinya bace,sannan ciki ba bakon abu bane ga mata"
Itama cikin bacin rai ta mayar masa da maganar.
"Okay haka ma zakice,wato bakiga lafinki anan ba kenan"
"Eh bangani ba, kudin kula kuke da ratuwa ta akan mai ya sameni wane hali nake ciki,kodan ni banjda ikon yin complain akai , lokacin dana sha jinya ta har nakusan mutuwa daga ita har kai saida nayi awa kusan takwas ban fito ba babu wanda yasan mai nake ciki,akwai wanda aka tuhuma a cikimku,sannan tunda ga wannan ko sannu bata sakemin ba har na warke,kayi mata magana akan hakan?.
Ni karewa ma banida number ku a wayata,saboda babu wanda yataba kirana a cikinku yaji yana ke ko lokacin dana bar garin ma nayi shekara,sai yanxu zakaga laifina danna bar matarka na awa biyu."
"Hakama kika ce koh,nidama nasan babu wani sanjawa dakikayi,kawai wani abin kike shiryawa "
Dagaa haka yabar dakin da sauri tareda buga kofar dakin da karfi.
Fadawa gado sumayyah tayi tana kama kukatunta,kai wannan masifah yaushe zata barta ne wai,kai kai kai.
Kwana ki biyu Ahmad ya dauka yana fushinsa daga baya dole ya sakko dan babu yadda zayyi,saboda maryam takasa yin girki,ko bakin kitchen din ma batason zuwa ballantana tayi girki.
Ya gaji da siyomata abinci shima ya saya,dan haka dole yasake komawa dakin sumayyan yace ta dunga yi musu girki.
To kawai tace daga nan ta dauke kanta,dan bakaramin haushi abinda yamata yabata ba.
Shiyasa ta danja baya daga shirginsu gudun abin haushi,idan sun gama dokin goyon cikin sai a koma a dunga magana mai dadi.
Dan maryam fushinta ta yawan kuka ko Ahmad din ma bata bari ba bare wani,kullum yana cikin aikin lallashi.
Yanzu da gangan take zama a wajen aikinsu ko babu abinda zatayi,kullum yawanci sai an samu wanda yazo gidan,ko daga dangin Ahmad ko kuma daga dangin maryam din.
Wannan yace wannan,wannan yace wannan kullum zance akan ciki,suyi ta lallabata,wasu kanma ko kukasu batayi tana wani sharewa.
Ga shi Ita sumayyah mai dafawa ta basu itace kashin gindinsu,harda mai cemata juyah,kalmar tana bata dariya sannan kuma tana bata haushi,wasu kuma sai suce tsohon mijintane ya siyar mahaifar,wasi kuma suce ancire mata a asibiti ta lalace.
Bayan cikin maryam yayi wata bakwai ya shiga na kusan takwas sai ta daina jinyace jijyacen,saidai wani lokacin har yanxu tana ciwon mara,amma cin abinci kam sai taci na kusan mutun hudu ma,tayi wata katuwa da itah,ga wani so da da kukawa datake samu daga dangin miji dana nata dangin.
Wata kanwarta aka dauko ta zauna a gidan take mata ayyuka,dan ance ta daina yin wasu abubuwan dayawa.
Ita kuwa sumayyah taji dadij kawowa yarinyar,dan zata samu ta dunga aikin gabanta,dan yanzu busy take sosai suna shirin daukar sabin matan daxa'a koyar a ma'aikatar..
Yau ma tun safe ta fita daga gidan tana sauri,har ta manta wani document na sunayen mutanen.
Saida taje kafin tagani a wajen aikin.
Wajen karfe sha daya ta shigo gidan daukar file din,Ahmad baya nan ya fita aiki,ita kuma kanwar maryam ummi ta tafi makaranta.
Babu kowa a falon lokacin data shigo,direct dakinta ta shiga ta dauko file din ta fito tana sauri,dan sannan za'a fara interview.
Muryar maryam taji wadda tafito daga dakinta da turtsetsen cikinta tana turashi.
"Sumayyah ina zaki"
Mamaki tambayar ta bata saikace itace hajiya mama
"Kamanya ina zani,wajen aiki zan koma mana"
"Ki tsaya ki dafamin tuwo shinake son ci yanxu,ko bazaki dafaba kai"
"Tuwo kuma,bazan iya dafa tuwo yanzu ba,kibari ummi takusan dawowa ai,saita fada miki"
"Ni yanzu nake son ci,dama nakula bakin ciki kike da cikin dayake jikina kuma miji yana sona yana kulada ni"
"Wannan wace irin magana kike haka,me ruwana da sonki dayake kuma,sannan wayace miki ina bakin ciki da cikin ki,wani ne ma bai tabayi ba sai yanxu,kizaki fadawa cikin,abinda saida kowa yayi ya barki"
Cikin haushi maryam takama wuyan rigar sumayyah ta rike sai masifah takeyi,wanda shikuma dadai da shigowar mai gadin su yakawowa maryam din aikanta ma agwaluba.
"Madam ga Aikan......"
"Kaima ajiye nan ka tafi ina zuwa"
Shidai cikin mamaki ganin yanda suke fada da wannan yanayin ya fita abinsa,dan Ahmad din bai fiyeson ya dunga shiga sha'amin iyalansa ba.
"Ke maryam ki sakemin riga,yanzu da wannan yanayinnaki kike kama wani fada,saikin jiwa kanki ciwo tukunna koh"
Sumayyah tafada tana fizge rigarta tayi hanyar waje da sauri,dan ita hankalin ta yana kan inda ake jiramta ba wajen maryam din ba.
Da sauri ta fita bakin titi ta tari napep.
Ita kuwa maryam ganin sumayyah ta manna mata aniyar ta yasa ta zuciya tareda bin sumayyan zuwa waje da sauri.
Zanin ta daya rikene ya hanata karisa kaiwa bakin kofar,inda hakan ya hadu da fisgar zanin datayi da kuma santsin tiles din.
Sai jinta tayi a kasa timmm takan cikin,ko kwakwkwaran motsi kasawa tayi bare kuma neman dauki.
Take ta suma a wajen jini yana fitowa daga kasanta,da alama yasamu hanyar fitar.......

Toh fah ya kukaji wannan chapter.....






🏵*sadi-sakhna ce*🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now