page ...36....

187 18 8
                                    

   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...36....




Bayan sati biyu da auren sumayyah da Ahmad abubuwa da dama sun faru,yayinda ta kashe abubuwa da dama a littafin kaddarar ta na gidan,sunan data saka masa kenan.
Da fari kafin zaman ta ya danyi nisa ta daina zancen komawa makaranta,saidai yanzu dagaske tana son komawa makarantar,duk yadda zatayi ma zatayi ko wacce irin kunya ce a shirye take da jita data zauna bata gama karatunba,dan ta kula yanzu karatunne kadai gatanta.
Mahaifinta har yau bata sanja zani ba tsakanin sa da itah,yayunta kuwa haushinta sukeji wai ta auri Ahmad zata ruguza masa gidansa,musamman ma yah mu'azzam.
Hajiyah mama kuwa babu yanda zatayi koda tasan ya ake ciki,bare ma batasan wace waina ake toya ba,dan sumayyah ta fadamusu karsu bari tasan irin yanayin datake ciki a gidan Ahmad din.
Tun da tashigo gidan har yau ko harafi daya bai hadashi da itaba,barekuma uwa uba wani abun ihsani.
Abincine dai maryam zata dafa ta zuba mata nata ta ajiye a kitchen,idan taji yunwa taje ta dauka taci,daga nan shikenan abinda yake hadasu.
Ita kanta maryam wani lokacin zasuyi zancen arziki,amma daga sunyi wayah dasu anty Maimuna sun zigata shikenan saita fara hura mata hanci.
Da sumayyah taga haka tafara zanye jikinta daga nasu,take harkarta itah kadai a gefe,dan babu dole tunda ba uwarta bace.
Yanxu watanta guda kenan a gidan,abubuwa da dan dama ta saba dasu yanxu,dan saidai ta bawa wani labari ma.
Tana zaune tanajin karatu a wayar ta tana bi,taji kaman hayaniya a bakin kofar dakinnata,dagowa tayi tana kallon wazai shigo said kuma taji an tsaya,abinnne yabata mamaki,waye kuma a bakin kofar dakimta,dan rabonta da wani ya shigo hanyar lungun dakinta tun sanda maryam tazo ta kirata cin abinci.
Tashi tayi ta kashe karatun tareda karisawa wajen kofar,budewa tayi suka hada ido da maryam,
"Lafiyah wani abune ya faru?"
Shine abinda sumayyan tace,
"Ahah dama baki mukayi a falo kizo ku gaisa"
Jimm sumayyah wane bakine kuma zasuzo gidannan har maryam tazo kiranta,dan su kansu yan uwan Ahmad ba sonta suke ba in ka dauke inna ramma da iyah,tuj abinda ya faru a baya suka dau dumi da itah.
Inaga kuma yan uwan maryam wanda in akace su bude kasa su hura wutah su sakata a ciki a zasu iyah.
Yan uwanta kuwa in sune suka zo ai dakinta zasu shigo koh,bare ma Muhibba cema tazo sau daya,itama tundaga sannna abbah ya hanata zuwa,a cewarsa kartazo su hadu suyi ta munafurci.
Tun daga sannan Muhibba tayi zuciya tace bazata kara zuwa ba itama.
Dawowa da tunanin tayi tareda bin bayan maryam dan ganim suwaye bakin
Anty Maimuna ta gani a bararraje a falo itada humairah,saikuma wata wacce sumayyan bata saniba.
Karemusu kallo tayi dukkansu kafin ta juyah ta kalli maryam.
"Ina bakin dakika ce munyin,indai wannna abunuwanne bakin su ai ba baki bane a wajena,hasalima kece baki a gareki bani ba.
Ita kam waccer(tafada tana nuna anty Maimuna) kekanki tare kika ganni da ita,dan haka banga baki a nan ba"
Tagama tabe bakinta kaman taga kashi tans kare musu kallo tarwda juyawa zata bar falon,anty Maimuna ce cikin zuciya tace,
"Lallai ma yarimyar nan wuyanki yakai yanka,har ni zakiyiwa rashin mutunci ina matar yayanki"
"To Ina matar ubana ce ma so what,ke mai yakaiki zuwa cikin gidana kici nawa mutuncin"
"He hehe wane Gidan kike kira nakin,lallai maryam kin bani mamaki da kika barta take fadan gidanta,lallai ki maida komada zakice haka mana"
"To in ban kirashi gidana ba gidan nasiru zan kirashi?,ke kuma maryam kiyi ta zama suna zugaki,indai su zaki biye ta wallahi bazaki iya kama mijin bama,ke da muke zaune dake kinsan mijinki ba a gabana yake ba,meye kike wahalar dakanki da maganar su,ki cigaba da shan maganin dasuke baki,in kika rube ai wata zai auro karama kina gani saidai idone naki ,za'ayi maganin mai yarda da kowa,an fadamiki sonki suke?"
Saida sumayyah ta karishi masifar ta data dade batayi ba,am tabota kenan.
Dukkan su tsitt sukayi suna jinta har ta gama tabar falon.
A zaune take ta rasa mai zatayi kawai ta dauki wayah ta dannawa salma kirah,yau kam za'ayi ta takare.
"Hello mrs Ahmad yakk ya amarci?"
"Mtseww ke ni ba wannan nakira ki fadaminba,dama inaso na fada mikne cewa zan koma makaranta ne"
"Makaranta kuma sumayyah bayan duk abinda ya faru,anyah kuwa zaki iyah"
"Hmm salma kenan keta iyawar ma kike,ni ban damu da wahalar da karatun zai baniba dakuma kunyar dazan sha,ni abinda ya tsaya min arai shine anyah kuwa zasu amince su daukeni,kin sam ajiye karatun nayi a second semester yanxu kuma sun shiga second samester shine naga na KO ma na karisa"
"Wai akwai aiki kam,amma tunda kinsaka kanki bazai bada wahala ba inshaallah,amma ina dama IT ne zaki tafi ina kika bar makarantar koh?"
"Eh IT ne mana ban je ba na tafi,yanzu idan sun amimce shi zam tafi inshaallah,yanzu ykke ganin za'ayi salma?"
"Karki damu zan samu brr Jalal da zancen,inya so sai ya taimaka mana,tunda dama yana visiting lecturing a can din,sannan babban abokinsa ne HOD  din department dinky"
"Kai nagode nagode sosai salma sain jiki toh,amma idan sunki amince kice masa kada ya takura ya barshi kawai,nida kaina zanje na rokesu "
"Kinga kibar wannan zancen,bari na fada masa muga yanda za'ayi kawai"

"To shikenan sai najiki din"
Daga haka ta ajiye wayar tana murmushi,inda rabon zata koma makaranta itama saita koma inshaallah.
Bayan kwana uku da wayar da sukayi saiga salma tazo mata ta hantsi,dan tsabar murna rasa inda zata sakata tayi.
A falo tana shigowa ta hadu da maryam wata tanayi mata lalle.
Sallama tayi cikin hade rai kaman wanda aka zageta,
Itama maryam din tunda ta daga ido suka suka kalli juna daga nan bata sake cemata komai ba bayan amsa sallamar.
"Sumayyah fah tana nan"
"Tana inda kika san zaki sameta mana salma,ko kin manta dakin dakuka kawotane wata daya daya wuce"
Daga haka salma tashige hanyar dakin sumayyan,abin yana bata haushi ganin dakin sumayyah,shiyasa ma dan karta debi abin haushi taki zuwa gidan ,rabonta da shi tun lokacin da suka kawo sumayyan.
Rungume juna suka fara suna ta murna,saida sukayi dan kansu kafin suka zube a gadon suna maida numfashi.
"Salma kwana biyu ya gida da mama,sai yau kika ga damar zuwa koh"
"Yanzu ma ba zuwa kawai nayi ba daliline yasaka,nafadawa barr Jalal tarihinki kiyi hakuri,nayi hakanne dan yah taimaka mana sosai,ina fatan bakiji haushiba"
"Hmm Allah na tuba wani can  maai yasan labarina ba wai mai taimakona ba,babu komai ina godiyah sosai salma,ince dai dashi za'ayi Kai"
"Eh to ganinan dai har yanzu,ni wlh shidinma tsoronsa nake,dan dai nasan halin sa ne kuma yanada kirki sosai,yanzu haka ma babane yace ya turo magaba tansa,sai murna yake ya samu dama"
"Ke kuwa ai dole yayi murna,irin wannan zukekiyar budurwa ga hankali ga ilimi so kike yayi miss"
Dukan wasa salma ta kai mata tana yar dariyah,
"Dallah ji wani zance,oh na manta nun  Kama zance ban fada miki abinda nazoyi bah.
Ga wannan file din jiya brr ya bani da daddare,yayi magana da HOD dinku,da farko kin sauarensa yayi,har yanzu ma dai bai yarda sosai ba,shiyasa ya bada yarjejeniya akan saikin bada a hakuri tukunna mai karfi kafin a gyara reg number ki tacigaba da aiki,wannan file din bayanan da suke so kibi ne da dokoki,idan kin amince toh kiyi sign sanann ki kai masa ranar monday.
Har issue akan IT din ma sun tat tau na dukka,idan kika je zaki yanda suka yanke"
Saurin rungume salma sumayyah tayi tana kukan farinciki.
"Wayyo salma kinmin komai,mai zan miki na biyaki da wannan halaccinnaki,kedashi bazan taba mantawa dakuba a rayuwa ta,karki damu inta kama kwanciya a kasane ma zanyi wlh indai zasu hakura su barni"
"Kai sumayyah kidaina fadan haka,koba komai ke kawata ce,wacce nake jinta tamkar yar uwata,shikuma brr jalal dama halinsane na tausayawa da kyaitatawa wanda bai saniba ma yana taimaka masa bare kuma na nema daga bangarena,dan haka kikwantar da hankalin ki,Allah ne ya dubeki yafara fiddaki daga jarrabawar daya tsomaki sumayyah,kedai kicigaba da kokari kici jarabawar watarana sai labari"
Share hawayenta tafarayi tana kallon file dim,har sannan fuskarta shaba shaba take da hawaye.
Hirarsu suka cigaba dayi har salma ta tashi tafiya ta rakota,akan zasuzo itada barr jalal ranar monday su je da itah,idan tana ganin bazata iya ba.
Saurin jijjiga kai tayi tareda cewa,"
"Ahah karki damu salma zan shiga rayuwarku dayawa ai,babu komai zan je da kaina,in kun rakani yanzu wazai dunga rakani toh,zanyi yakin da kaina,nina bata niya kamata nayi wahala ta saboda nafi sanin darajarsa da kyau"
Tun da daddare ran lahadi sumayyah ta shirya zuwa makarantar,wanda rabonta da ita shekara uku kenan yau zata koma kuma,wai abin da kamar wuyah.
Da safe da wuri ta tashi lokacin maryam tana kitchen tana abin karyawa,lokacin da taga sumayyah ta fito da wuri saida abin yabata mamaki,dan bata taba ganinta ta tashi karfe bakwai ba.
Dakin Ahmad ta wuce ta bude ta shiga,a bakin dakin tayi sallama saida ya amsa kasa kasa kafin ta shiga dakin.
A tsaye yake ya juya bayansa yana kallon madubin sa ta comp irin na maza a hannunsa,da alama daga wanka ya fito.
Dauke kanta tayi gefe tana kallon wani waje daban saboda ganinsa sanye da towel.
"Me kika zo yi dakina?"
"Inaso na fada maka cewa zan koma makaranta,zan dunga fita"
"To ta ina hakan ya shafeni,in kudi kika zo tambaya banida shi"
"Ba kudin ka nake bukata ba,ko ka bani ma bazan karba ba,nazo fada maka ne a matsayinka na wanda nake karkashinsa,tunda nariga na fada maka shikenan,kuma ma nasamu amsar danake so "
Tana gama fadan hakan ta fita daga dakin.
Shiryawa ta farayi cikin wani less pink mai adon blue sai tasaka hijabi shima blue,babu abinda ta saka a fuskarta daga man dayake kan fuskartata.
Daga haka ta dauki jakarta ta saka file din a ciki ta fito.
Kitchen ta nufah inda abincinta yake taci a gurguje ta fito,lokacin ma har maryam ta fita waje yiwa Ahmad rakiyah.
A tsaye ta samesu suna magana a bakin motar tasa,tana zuwa ta wicesu ko kallon inda suke batayiba,suma da kallo suka bita basuce komai ba.
Hanyar anguwar tasu ta fara bi saboda ta samu ta isa bakin titi,kasacewar safiyace babu abin hawa tukunna.
Tana cikin tafiyane taji karar wucewar motar Ahmad ta gefenta,tana kallonsa har ya bacewa ganinta,kuma tasan ya ganta sarai,saidai ko a jikinta bata kawo ya tsaya ya dauketa ba,dan dama bata saka rai ba.
Ba ita ta isa bakin titin ba har takwas saura.
Tayi sa'a kuwa tana zuwa wajen saiga wani mai napep ya dauketa har kofar makarantar ya ajiyeta.
Tsayawa tayi tana kallon get din makarantar,bayan wasu shekaru finally gata ta dawo karisa abin da ta bari bata kammala ba,kanwarta da take bayanta har ta gama ita sai yanzu zata cigaba.
Jan iska tayi ta fesar kafin tasaka kai zuwa cikin makarantar tana mai addu'ar neman tsarin abin sharri a cikinta.
Department din su ta nufah gabanta yana faduwa,koya zata kare.



🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now