Page ....31....

174 18 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

Sorry kun jini shiru akasi aka samu,ga 31 nan 32 ma yana  zuwa inshaallah

🏵🏵🏵
...31....



Ana sauran kwana uku a daura auren sumayyah kanwar inna ramma dakuma matar kawun Ahmad inna karimatu suka kawo kayan auren sumayyah.
Akwatina set guda amma kanana na set ne,saidai suna da kyau babu laifi.
Su anty hajara ne da su anty Maimuna suka karbi kaya ana ta raha da dariya,dan dama an san juna sosai.
Sumayyah tana daki tana karatun qur'ani bayan tagama sallah Muhibba tashigo dakin tana dariya.
"Anty sumayyah an kawomiki kayan kaurenki,wai gani nake kaman a mafarki wlh,kayan masu kyaine kam,amma gaskiya yah Ahmad yaci yayi kayan dasukafi haka,karamin set ne fah anty sumayyah bako gansu ba"
Duk maganar cikin bata fuska Muhibba takeyin ta,dan daga gani bataji dadin ganin kayan haka ba"
"Ke Muhibba miye hakan kike fushi marar dalili,menene to dan yayi karamin set din,haka Allah ya gore masa,ni banyi tunanin zai bani kayan aure bama,dan haka mamaki nayi da akace an kawo su ma,ba wai manyane ko kanana ba,ki kwantar da hankalin ki nibata kaya nake bama,kayana ma sun isheni sakawa"
"Amma anty sumayyah wlh......."
"Salma taxo ne?"
Sumayya tayi saurin tambayar Muhibba saboda takawar da ita daga barin maganar da take mata na kaya,dan ita bashine a gabanta ba.
"Eh in a ga tazo,dannaji maganarta suna gaisawa da su anty nafi lokacin dana shigo nan"
"Okay shikenan nasan zata shigo ai"
Lokacin da salma tashigo gidan an bude kayan kenan ana gani,kallo biyu salma tayi musu ta dauke kanta ta koma kan kujera da zauna,haushin kayan takeji musamman ma dataji abinda anty maimuna take fada,
"Lah kaya mashaallah,ai tasamu ma muda munyi zaton kawo kayan me ne,sao gashi dan kirki yayi mata kuwa badan halinta ba"
Ita kanta anty nafi duk abinda sumayyan tayi amma da taji abinda anty Maimuna take fada saida taji haushi a ranta,wanda hakan yasa ta kasa hakuri ta maida amsa.
"Kaya kam sunyi kyau,amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba,duk lalacewar kura tafi kare,tsohuwar zuma kuwa duk yanda aka kai akawo dole sai an nemeta tunda da ita ake magani"
Kallon kallo sukayi ta dan kasa kasa salma na kallonsu kafin suka ware aka cigaba da zance.
Tashi anty maimuna tayi tai dakin hajiya mama da humairah takita kan cewa ana kiranta a waya,tashi tayi ta bar wajen ta nufi dakin.
Ita ma salma dakin hajiya maman ta nufa domin su gaisa da ita kafin tawuce wajen sumayyan.
Tsayawa tayi a bakin kofar jin abinda su anty maimuna suke cewa,
"Ke maryam fadamin gaskiya,dagaske ke yabawa babban set din?"
Shewa anty Maimuna tayi kafin ta cigaba dacew,
"Hmm ai dama na fadamiki,kina kwantar da hankalin ki kika ra narkewa saikin ki fita samun komai,musamman ma da ba sonta yake ba yanzu tursasashi akayi,kedai shakuruminki komai zaiyi yadda aka tsara,inna tuno da dakinta ma nafi dariya,amarya a dakin yara,sufah yanzu duk sun dauka gida zai kamata yamzu,ko kuma daga baya,basusan a dakin yara zata zauna ba"
"Dama naji suna maganar a gida shida mu'azzam kan cewar wai bashida kudi a dakin yara zai saka ta"
"Ke humairah babu wani rashin kudi kawai dai dna baya ra'ayintane yanzu,kuma ai gwara hakan,sai muga girman kannnata inda zai kaita koh?"
.........
Karar shigowar mutum ne yasaka su yin shiru kaman ba magana suke ba,salma ce ta Shigo tana kallon dakin kaman mai neman wani abu,yayinda take kokarin yin kaman bataji abinda suke fadaba .
"Salma mekike nemane"
Anty Maimuna ce tasamu karfin halin tambayarta tana kokarin kwakwulo murmushin dole.
"Ahah dama hajiya mama nazo gaisarwa koh bata nan kai"
"Eh Bata nan tana sashen abbah "
"Okay shikenan barina tafi idan ta dawo saimu gaisa"
Daga haka salma tasaka kai tabar dakin,a ranta tana jinjina munafurci irin na su anty Maimuna.
Dakin sumayyan ta nufah har sannan abin bai bar ranta ba,lokacin data shiga har sumayyah tagama karatunta tana kokarin nade sallayar,murmushi tayiwa salma wacce tashigo da fuskarta kaman an dama kunu.
"Ke kuma mai yafaru naga fuskarki kaman mai tunanin wani abu"
"Hmm summy kennan ai dole ki ganni haka,daga dakin hajiya mama nake naje gaisheta,ban sameta ba saina samu su anty Maimuna itada waccan amaryar yayannaki marar kunyar(humairah),ke karki so kiji irin maganar dasukeyi a maryam a waya....nan ta zayyanewa sumayyah abinda taji suna fada.
Murmushi sumayyah tasakeyi bayan taji abinda salma ta fada mata,
"Haka suka ce to ai kansu sukeyiwa duk da banga wani laifinsuba,dama ba shiri mukedasu ba da maryam suke shiri,to kimga kuwa dole zasuji haushi idan suka ga zan aure mata miji,kaya kuma ni basune a gabana ba sam.
Zancen daki kuwa kekanki bai kamata hakan yadameki ba bareni,tunda ke kadai ce kika shiga dakina na gidan mutari kika ga yanda yake,to tundaga sannan kuwa kinsan zan iya zama a irin kowanne dakine batareda ya dameniba,nasan dakin Ahmad kona karen gidansane aljannar duniyane akan dakina na gidan mutari,dan haka ni hakan bai dameniba,fatana shine Allah yasa dakin a can gefe yake yanda zanyi rayuwata batareda natakuramusu ba.
Ni bazaman aurene zai kaini ba inta kwantar da hankalin ta ma,zanjene kawai saboda iyayena,nasan abbah idan na auri Ahmad wata rana Ahmad yace yayefemin to zai iya sassautamin hukuncinsa,itakuma hajiya mama ta ce idan na fita a gidannan ba silar gidan wani zanje ba bata yafemin ba,kinga banida mafita sai yin abinda zai warwaremin abinda suka fada ta hanyar auren Ahmad,kinga zan cika burin abbah ta hanyar bari masa gida sannan zan cika burin hajiyah mama ta hanyar barin gidan a matsayin aure nayi zanje gidan wani,kuma nasan idan ina gidan Ahmad hankalinta zai fi kwanciya tasan inda nake akan na auri wani daban bata san inda nake ba.
Dan haka ki kwantar da hankalin ki salma tunda kinfi kowa sanin dalilin aurena da Ahmad,kuma kaman yanda na fadamiki har yanzu banajinsa a raina da har zan kwaceshi a hannun maryam"
"Nasan da haka amma abinda suke bai daceba,koba komai ke kanwar mijinsu ce bai sannan itakuma maryam ai kawarkice"
"Hakane kam,kowa yayi nagari dan kansa,nikam naga tawa izinar ai sauran su idan sunada rabon ganin tasu"
Suna cikin tadinne bayan da wani lokaci humairah tashigo dakim tana kalle kalle,
"Salamu alaikum,tunda ba'a nemeni an je inda nake ba ni gashi nazo inda kike na baki girman amaryar Ahmad"
Murmushi sumayyah tadanyi bayan ta amsa mata sallamar tace,
"Lah meyayi zafi anty humairah,bansan kinzo bane,batun nemanki kuwa ai laifin mijinkine dayaso muje inda kike daya kaimu dakansa"
"Ah meruwan mu'azzam anan kuba yaraba,gaskiya nayi fushi da bansan kannennnawa ba saida nazo dakaina,ita Muhibba ai tajemin kuma munhadu a wajen biki"
"Saikiyi hakuri,watarana inshaallah zanje"
"To shikenan ya shirin biki kuma,gaskiya dakinki yayi kyau,karfah yazo yafi na gidan auren,irin wannan tsari"
"Lahh I'd an yafi ma ai bakomai,shi gidan uba ai dashi ake tunkaho,kuma menene ma na kwadayin duniyar ne abinda taku daya za'a saka mutum,koya ma yyi mata zata gode kuma bazata raina ba inshaallah"
Dukka daga humairah har sumayyah kallon salma sukayi yanda ta maida maganar,dan dama tun dazu data jisu abin yake cin ranta,sai yanzu ta danji dama dama,takuwa fuske kaman ba itace tayi maganar ba.
Basuyi wata magana ta arziki sosai ba humairan ta fice a dakin,duk da ma yawanci salma ce mai maida mata martan,ita sumayyah wani aikin ma tafarayi na gyaran kayan tana jinsu.
Bayan ta fitane salma tabita da harara tana jan tsuka,
"Aikin banza ko kunya ma bataji,ku gama surutunku na munafurci sanann kizo kina yiwa mutane iyayi,wlh yah mu'azzam bayyi sa'ar mata ba,yau dubeta sai kace muciya kaman za'a hureta,a hakan har tayi kwarin yiwa wata iskanci tana fama da kanta"
Dariya sumayyah ta kwashe da ita jin abinda salma take cewa wanda hakan yakara kufuleta ta koma kan sumayyan.
"Kutt dan walakanci ina tayaki fada kina min dariya koh,wai yaushe ma kika sanja kika zama wata sanyu sanyi ana miki tsiya kina gani?"
"Hmm salma wannan duniya kokai karfene sai dole ka narke ka sanja,kema gashi nan ai kin sanja kin xama masifaffiya,musamman ma ga maza,dan ma ba aurennaki yayi ba ya shafamiki ciwon,nida akayi min gyambo nace me?"
"ke na manta ban fadamiki ba ma mun hadu da wani barr tanma ya dameni ya takuramin bai san haushinsu  nake  ji ba ma gabadayansu mazan"
"Kedai kicigaba da addu'a kawai,Allah yakawo sauki a lamurah,sannan kidan bashi dama mana ki gani,idan da sharri yazo allah bazai bashi dama ba ai,dan inane shikuma ?"
"Dan garinnan ne,amma ba 'anan yake aiki ba a abuja yake,sannan babbanmune ma a wajen aiki fah"
"Kinji ma Ashe kimsanshi ma,saiki bashi dama kawai kigani,allah yashige mana gaba"
"To ameen dai kawai "
Dayake ba aurene na budurwa ba ana kawo kayan kowa ya watse sai kuma ranar daurin aure in allah ya kaimu.
Kayan aka kinkima aka kai dakin hajiya mama,wanda ita samun damar gani ma batayiba,datai saka albarka a ciki.
Washagarin ana gobe daurin aure sumayyah tana zaune a dakin ta hajjya mama ta aiko tana kiranta,amsa wa tayi da tana zuwa,dan yanzu ta fi zama a dakinta fiyeda ko zaman ta wajen.
Wata yarinya ta samu a zauna a dakin hajiyah maman wadda bata santa ba,bata tambayi wacece ba.
Sai matsawa da tayi inda hajiya mama take tace gani.
"Wai ana gobe zaki daura aure amma banga kina shirin komai ba,haka zaki je gidan mijin a kode"
"Hajiyah mama to mezanyi?"
"Oh bakisan me ake ba idan za'ayi aure,wannan ne karonki na farko ko me?,ga nan mai lalle da gyaran jiki zatayi miki sai kuje can dakinnaki"
"Nikam hajiyah mama ta hutasarta,dan babu abinda zanyi gaskiya"
"Dallah rufamin baki,ki wuce kuje tayi miki lallennan saura kuma naji wata magamar,ke ummi tashi ki bita,ki gyara mata gashin da lallen idna akwai abinda ake bukata kizo ki fadamin kinji"
Daga kai alamar to kafin tabi bayan sumayyan wacce take tura baki gaba alamar anyi mata dole.
Washagari daurin aure tunda safe su anty nafi suka zo,hadda su anty Maimuna wanda ake abu dan idon uwar miji.
Duk da gidan bai cika kaman aurenta na  farko ba amma kuma ba laifi mutane sunzo,a cikin kawayenta kuwa iya salma ce kawai.
Lallen nata kuwa na jiya yayi kyai sosai,duk da ba a son ranta tayi ba amma yayi mata kyau,sai kallon sa takeyi,rabonta da lalle tun na aurenta a gidan mutari,tana tuna hakan taji wani bacin rai da danasani a ranta,anya kuwa zata manta mutari da zuri'arsa a cikin ranta,gaskiya sunyi mata tabo mai wuyar warkewa.
Tana cikin tunanine salma tashigo dakin tana ta magana  amma bata jita ba,tafa hannunta tayi a kusan fuskarta wanda hakan yasata yin firgigit ta juyo tana zare ido.
"Mrs Ahmad ina kike kallon nazo ina ta magana bakijini ba,ko tunanin mijinnaki kikeyi"
Gaban tane ya fadi da taji salma ta ambaci kalamar miji,
"Salma naji kina cewa miji,an daura aurenne ?"
"Eh mana shi nazo na fadamiki ai "

To fah dankari.

...

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now