Page ...49...

217 12 0
                                        


 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

Yan uwa don allah kuyi hakuri,matsalar cajine ya rikeni wlh.

Ga chapter ta 49 nan,in allah ya kaimu

zuwa karfe 8 na dare zaku ganni dauke da ta 50.

🏵🏵🏵

...49....






Tsirama sumayyah ido Ahmad yayi,kwata kwata yarasa gane shin,mafarki yake ko kuma gaske ne abin yake faruwa,ga sumayyah tabbas ya ganta,amma ganinta ta yake kaman wata daban ba wacce ya sani ba.

Dan tana shigowa kallo daya tayi musu ta kauda kanta gefe.

Tabbas kam tayi kyau sosai,yanayij siffarta da gayunta ya dawo har yafi na da,saidai amma tafi waccer sumayyah gentle da kuma serious action.

Kowa a wajen kasa cewa komai yayi da sukaji abinda hajiya munawwarah tafada dangane da matsalar sumayyan.

Ahmad tunda tashigo falon yakasa dauke idonsa daga kan ta sam,kulada kallon dayake matane yasa ta tsuke baki tareda dan hararsa,amma hakan ko a jikinsa,saima tashi yayi ya isa inda take.

Hannunta yake kokarin dafawa wanda yake gefensa,wani kallo tayi masa tareda matsawa,tana kallon hajiyah munawwarah.

Hannunta ta daga tanayi mata alamar nan din inane sannnan kuma Ahmad waye.

"Mijinkine sumayyah,sannan nan gidankune"

Zaro ido tayi tareda jijjiga kai tana kokarin tashi.

Tunda suka shigo din sai yanxu yah Isma'il yayi magana,

"Munji abinda kika ce hajiya,sannan muna matukar godiya da kulawar dakikayi da itah,saidai muna so muni mai likitoci sukace akan matsalar tata."

"Toh sunce ba abune da za'ayi magani ba,dan yanda suka fada ma wai tana ganin wanda ta manta zata iyah recovery,amma munsha nuna mata hotunnaku takasa tuna komai akai,bamu saniba ko idan ta tuna abinda yasaka shiga halin"

Jikinsu sanyi yayi bama yah hajiya mama,duk dokin son ganin yar tata gashi itakuma bata tuna da ita ba.

Tashi sumayyah tayi tareda figar hannun islam,akan su tashi su tafi,sai nunawa take ta gaji da kallon dasuke mata,dama tunda suka zauna take duba lokaci a wayarta

Hajiyah Aisha ce ta tashi tareda daga kafadun sumayyan,

"Sumayyah anan zaki zauna fah,saboda nanne gidanku,idan kina zaune zaki tuna komai,batun aikinki kuma hajiya munawwarah ta baki kamfaninta data fara ginawa a garinnan,har ta sanja masa suna zuwa sunan ki GOLDEN GIRL(G-G) DECORATIONS INVESTMENT.

kinga saikiyi zamanki,"

Jijjiga kai sumayyah tayi tareda fisge jikinta daga hajiya aisha,a dole bata yadda da zanceba sam

Har tazo fita ta cinkayo muryar abbah yace,

"Sumayyah!!!"

Cakk ta tsayah a bakin kofar tareda juyowa tana kallon abban,takawa yayi har zuwa inda take yana kallon cikin idonta.

Kowa kallon abinda yake faruwa yayi kafin sukaji abban ya fara magana.

"Sumayyah Kiyi Shiru anan wajen,ban yarda ki sake cewa wani abu,bakinki baya furta alkhairi bare kuma aikinki,sannan kuma daga yau ki manta da gidannan dakuma abinda ya shafeshi,ban yadda nasake ganinki ba daga yau,kibar rayuwar kowa ya huta dake!!.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now