Page....32...

176 19 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...32....

"Salma dagaske kikeyi an daura aurena da Ahmad?"
"To miye na mamakin,ba haka kike so ba dama,sai yanzu zakiji bakya so bayan aikin gama yarigada ya gama,yanzu kam kuma ai saiki rungumi zaman gidan ki saka a kirjinki"
"Ke Ni ba wannan ba jinake kaman a mafarki shiyasa"
Baffah Usman ne yashigo gidan bayan an gama daura auren,inda ya nemi ganin sumayyah amarya.
Salma ce data shiga dakinta ta fada mata neman ta da akeyi.
A dakin abban su ta sameshi suna ta hira shida abbah,wanda daka ganshi babu wani farinciki na yayi auren ya akan fuskarsa.
Tusugunnawa tayi ta gaishesu kafim baffah Usman yafara mata kashedi,
"To sumayyah aurenki dai da Ahmad and daurashi yau,sannan kaman na farko shima wannan din ba dole akayi miki ba,abinda nake so kisani shine,yanxu ke ba yarinya ce ba,kin dandana zaman aure kinji ya yake,keme fadawa watace abinda kika gano,dan haka ki kwamtar da hankalin ki kiyi zamanki a gidanki,kar ki tada fitina kokuma wani bore kamar yanda kowa yake cewa haka kike,kibawa kowa mamaki ki zauna a gidanki.
Sannan kayanki na wancan lokacin da bai baki ba yanzu yace a dauka a saka miki a dakinki,za'a je a saka miki inshaallah,wannan kuma gashi sadakinki ne dubu talatin,mu muka ce ya rageshi saboda albarkar aure,Allah yabada zaman lafiya.
Ni zan tafi yanxu na baro wajen aiki babu kowa,ga nan ubanki sai yasake jamaki kunne"
"Ahah yaya ni babu wani sake jan kunne dazanyi mata,naka ma da taji ya wadatar,jan kunnena tsohone kuma tariga da tasanshi,idan har tayi wani abun aka kawokim kararta to babuni bani ita kuma tanemi wani gidan wannan karon"
Tashi sumayyah tayi tafito daga dakin bayan ta gamajin gargadin  da akayi mata,dan wannan ba nasiha bace.
Wai meyasa kowa yake mata kallon azzluma tantiriya wacce take jiran karamar dama ta aikata wani mungun abune?,dama tsiyar kayi wani abun ki kenan,koda ka tuba ba lallai ne kowa ya yarda dakai ba.
Dakinta ta koma inda salma take itada Muhibba,tazo wucewa ne suka hadu da humairah ta zo wucewa,
"Ahh amarya ce nake ganine haka a araha ban cike file ba"
Wuceta sumayyah tayi dan a halin da take ciki bata bukatar yin magana ko kadan.
Yini aka cigaba dayi,yayinda gidan maryam kuwa tamkar ma ba wata za'a kawo ba,dan girkinta tayi daga ita sai mijinta ta sheka wankanta tana kallo a falon gidan,Ahmad ne yashigo yana hada ido da ita yayi turus,bayyi tsammanin ganinta a babban falon ba da wannna lokacin tana kallo.kallon shaddar jikinsa yayi wacce yaje daurin auren da ita,itama kallon shaddar tayi kafin tace,
"Ango an daura aurenne?"
"Uhm andaura"
A hakali yabata amsar cikin yanayin damuwa kafin ya wuce cikin dakinsa.
Da yamma tayi fitowa akayi da kayan dakin sumayyah za'a tafi jere,su anty maimuna ana daga gaba gaba za'a je jere,danyi sukayi kaman basusan ya dakin daza'akaita yake ba.
Har wasu sun fara tafiya sumayyah taja salma gefe tace mata.
"Salma tunda ke kinji mai su antu Maimuna suke fada nasan kinsan wane daki zaku kai kayan,sannan kuma kimsan dakin bazai cinye kayan ba,idan har hakan ta faru kusaka gado kawai da kujera daya idan zata Shiga,da madubi,sauran kuma ki sayar dasu karku dawo dasu gidannan abbah yasan meyake faruwa shida hajjya mama"
"Kai sumayyah a siyar kuma? Mai zai hana a kai wani wajen a ajiye,bashida store ne a gidansa, a can zamu saka su kawai"
"To shikenan kusaka din amma idan baku samuba karku dawo dasu gidannan kisayardasu salma kawai,tunda ba gini ake minba bare na ce zan tashi watarana anan din zan zauna har mai kasamcewa ta kasance"
"Karma kice haka,za'a san yadda za'ayi kawai,bari mutafi,duk yadda ake ciki zaki jimu inshaallah"
Daga haka salma ta fita zuwa inda motar take suka tafi.
Suna isa tun kafin a yi komai anty Maimuna tayi cikin gidan tana gida,daga ji ta tsiya ce,anty nafi ce tabita da kallo ta jijjiga kai kawai.
Sallama suka rangada a gidan,can bayan kaman minti biyar maryam ta fito tana hamma da alama bacci takeyi,dankwali a hannu.
"Lah anty Maimuna sannunku ta zuwa"
Anty nafice da taga ba kulata zatayiba tace,
"Uwargida sai a nuna mana dakim amaryar zamu saka kaya dan sauri mukeyi"
"Ayyah yi hakuri ga can dakin idan kunbi wannan lungun,salma ga makullin"
Tafada tana mikawa salma key din wacce take rike da wani ledar kaya a hannunta.
Karba tayi tashige hanyar dakim,dan dama ita tasan wane dakine tun kafin suzo,dan haka batayi mamaki ba ganin dakin acn lungu,a ranta tana Allah wadai da wannnan hukunci na sumayyah data yanke.
Budewa dakin tayi tashiga anty nafi tana binta baya itada Muhibba,bude baki sukayi suna salati ganin dakin karami irinna yara.
"Mai nake gani haka ni nafisa salma?"
"Hhh dakine mana anty nafi,ita amaryar ai tasan da labarin dakin,sannan tace dan Allah wai kar a fadawa hajiya mama wane kalar dakine,dan ita a bangarenta taji ta gani"
"Hmm wai yanzu a wannsn dakin zamu saka kayan,ta ina zai cinye su to? Naji ana cewa ya kama mata haya,ko duk zancene kai?"
"Eh to inaga zancenne amma babu wani zancen haya daya kama,wannan ne dakim,tace idan bao cinye ba wai a siyar sauran kayan kawai"
"A siyar kuma,baza'a siyar ba,a saka wanda aka saka sauran kuma saina tafi dashi gidana na ajiye mata,tunda ina da extra daki "
"To shikenan kam anty nafi kin kawo shawara mai kyau hakan za'ayi,watarana ai zasu mata amfani inda rai"
Daga haka suka fara saka kayan a cikin dakin.
Ana saka gado dama gashi irin babban nan aka saka kujera mai daya da kuma madubi shikenan dakin ya cika fam,dan ma Allah ya taimaketa drawer madubin irin masu manyan ne zasu isheta saka kayanta.
Lekawa suka farayi amma babu wani waje sai wajen sallah kawai shine ya saura.
Muhibba sai mita takeyi kaman zatayi kuka ganin dakin yayartata.
Har suka gama jernsu suka fito anty Maimuna tana zaune a falo suna zance da maryam,dan itakam humairah tunda safe ta tafi,cewa tayi bazata zo jeren ba.
Sauran shirgin kuma na kayan kitchen tafiya sukayi dasu,dan babu inda zasu saka su,sannan maryam tace itama nata mayarwa tayi shiya zuba kayan gidan dukka da Kansas ba ita tayi ba,shiysa suma anty nafi tace zata tafi dasu dukka.
Magana sukayi da mai motar kayan inda tayi masa kwatancen gidan ta xai kaimata su,akwai wanda zai karba ya shiga dasu,basai an koma dasu bama wanj yagani gudun abin magana.
Da daddare shirye shiyen kaiwa amarya aka fara dakinta,
Salma ce ta fito mata da wani less daga cikin kayan aurem ja,abinka da farar fata kuma tasha jan lalle sosai ya amshe jikinta dass.
Juyata salma tayi Bayan ta gama mata daurin dankwalin ta kalli madubi,kalleki fah kiga yanda kikayi kyau amarya,yaushe rabonki dakiyi kyau irin haka.
Kallon kanta sumayyah tayi a madubin kafin ta dauke idonta,duk da cewar daga kyan datayi a cikim madubin amma hakan bai sa taji wani dadi ba kokuma shaukin hasken datayi din,saima tabe baki da tayi kawai.
Duka salma takai mata na wasa a baya tana hade rai,Juyowa sumayyan tayi tana kallon fuskar salam kaman irin kayiwa yaro aika yaje yayi ba daidai ba
"Miye kika wani tabe baki dakika ga kwalliyar danayi miki,nasan dai baki isa kice batayi kyau ba,saidai wani abinne a ranki"
"Nidama bance kwalliyarki batayi kyau ba,kawai dai niba kwalliyace a gabana ba,ba irin wannan auren akeyiwa gargaji ga ba......"
"Kinga yimin shiru da wannan zancennaki,muyi sauri muje kasa hajiya mama tana jiranki"
Daga haka salma ta dauko mayafin ta shikuma baki ta sanya mata.
Fita salma tayi tabarta tanayiwa dakinta kallon bankwana a karo na biyu,shin yanzi kuma zata dawo kokuma ta tafi kenan allah masani.
Hawayen dake idonta tayi saurin daukewa ta bar dakin.
A hanyar zuwa dakin hajiya maman ta hadu da salma suka karisa tare,
Saida salma tarakata ta tsugunna kafin ta fito daga dakin tabarta daga ita sai hajiya maman.
"To sumayyah allah yayi kinyi aure na biyu zaki kara tafiya gidan miji a Karo na biyu,duk da wannan bama kinsa kaman na farko amma duk da haka kowa shuru zayyi yaji abinda zakiyi,yace ai gashi nan dama mun fada.
Dan haka ki nutsu kisan mai kikeyi sosai,idan wani abune ma yasaka ki shiga gidan toh ina fatan yakasance ba abune na cutarwa ba,dan duk yadda kika ga ina inashiga lamarinki idan har aka zo akace kinyi wani abu na cutarwa to bazan yafemikiba nima ballantana kuma abbanki.
Sannan duk da baya maryam kawarki ce yanzu yaya ce a gareki,dan ita kikaje kika samu,dan haka kibita sau da kafa,kiyiwa mijiki biyyayya Allah ya muku albarka,tashi ki tafi"
Tunda hajiya mama tafara magana sumayyah take rusa kuka har tazo karshe da maganar ta,sassauta kukan tayi kafin tace"
"Nasan kowa yana tsammanina da aikata wani abin amma inshaallah babu abimda zai faru sai alkhairi,zanyi kokarin wajen ganin nazauna a dakina lafiya batareda wata fitina ba inshaallah"
"Shikenan allah yayi miki albarka kije maza suna jiranki"
Daga haka matar baffah Usman inna karima takama hannun sumayyah suka nufi motar da Ahmad ta turo guda daya.
Iyah salma ce da inna karima sai anty nafi kawai.
Gidan tsitt babu hayani ya har suka shiga gidan suka nufi dakin sumayyan.
Zaunar ta sukayi a bakin gadon suka yimata nasiha suma suka kamo hanya zasu tafi.
Dan babu lallami dazasu mata tunda ba budurwa bace tasaba zama ita kadai dama

Har zasu fita sumayyah tajawo hannun salma tana marairai ce fuska.
"Kema tafiya zakiyi tun yanzu,bazaki dan zauna ba"
"Hhhh kijimin mata mai zan zauna nayimiki,kema kinsam ai zan dawo kwannan ki kwantar da hankalin ki kawai"
Daga haka salma ta kwace hannunta ta fita tanayiwa sumayya dariya.
Ita kuwa amaryar tana gani sun fita itama ta tashi akan gadon ta nufi bandaki ta dauro alwala,dan bazata tsaya batawa kanta lokaci ba a zaune.
Alwala ta iyo kafin ta bude kayanta ta dauko rigar bacci goduwa har kasa ta saka takuma zunduma hijabin ta.
Batasha wahalar neman sallayar bama dan dama komai kaman na dakinta haka aka saka mata shi.
Bayan ta idar da nafilar ne ta fara neman tsarin daga sharrin sabuwar rayuwar data shiga dakuma fatan haduwa da alkhairinta.
Tana nan zaune akan salalyar har bacci yafara kamata ta yage hijabin tabi lafiyar gadon,ko minti uku batayiba bacci yayi gaba da ita saboda gajiyar datayi,finally komai yakare na wani fargabar auren,saikuma zaman auren kuma........

Shine yanzu za'a  saka a gaba,Allah ya saukaka.

To ranar farko kenan na amarya a gidan mijinta,sai a cigaba da bibiyi danjin yanda zata cigaba da kasancewa a gidan Alhaji Amadu😂😀
😀😀😀
😀😀😀😀
😀😀😀





🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now