Page 28

175 17 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...28....

Inna ramma ce ta kalli iyah tareda cewa,
"Iyah mai za'a dafane yau din,naga bakya jin dadi sosai,sai a danyi wani abun dakike so"
"Lah Ramma kiyi kowanne ma,kinsan ni ban fiye zaben abinci ba ai,rashin jin dadine ma da jiin girma ban haka nikam da abinci"
Yar dariya inna ramma tayi tareda cewa,
"To shikenan iya Allah yakara sauki"
"Ameen ya Allah Ramma Allah dai yamiki albarka keda zuri'arki,Allah yasa kema ayi miki yanda kike min"
Tun kafin inna ramma tayi magana sukaji muryar Ahmad ya shigo gidan,wajen iyah ya koma ya zauna yana tuttura baki,da alama gajiya ce dakuma tension.
"Inna ta yunwa nakeji sosai"
"Anya iya yunwar ce,naga ka hade girar kasa da sama lafiya"
"Uhm uhm innna kina ga waccer yarinyar saboda ta raina ni kinji abijda tace wai?"
"Wace yarinya mai ya faru?"
"Saboda tsabar sumayyah ta raina ni duk abinda tauimin amma ta manta dashi,tacewa abbah wani ta fitar a matsayin wadda zata aura?,wane irin kiyayyaa sumayyah takeyimin a duniyarta,bayan wahlaar data bani a baya bai isheta ba saita kara wahalar dani saboda taga Allah ya tashi kafaduna?"
"Wai Wacce yarinya kake fada baban gida"
"Uhm sumayyah mana inna sumayyah taban mamaki,a tunanin ta zan aureta ne ko mata sun kare a duniya?"
Iyah ce ta kalle shi wanda sai yanzu tayi magana tukunna,ganin inna ramma tayi shiru"
"Yanzu amadu don ta zabeka a matsayin miji a lokaci nabiyu shine tana son baka wahala,kai kanka kasan yarinyar nan ta shiryu da sanja halayenta fiyeda da,yakmata ka bata dama ta biyu mana,kasani Allah yana son mai taimako da kuma mai saurin manta abinda akayi masa,hakanne zai sa ka zama jarumi a fili da boye"
"Dan Allah iyah ki daina fadin wannan maganar,goyon bayan na aureta kikeyi,ni bazan amince na aurenta ba gaskiya,iyah bazan iya aurenta ba bazan iya budar ido na ganta a rayuwata ba,bazan iya daukarta a inuwata ba iyah idan na ganta tsanarta da kuma jin haushinta dawowa suke a cikin rai na tamakr sabi"
"Baban gida ka daina fadan haka,koda sumayyah bata zabeka a matsayin kai take so ba nima dama zan maka maganar ka aureta,iyayenta sunyi maka komai a duniyar nan,abinda komai kayi bazaka sakamusu ba,dan haka ko domin hajiyah mama yakamata ka duba lamarin "
"Innan.........."
"Yah isa haka,ga wannan ka tafi dashi gida,maryma tana so sosai,karka zauna ka barta ita kadai a gida,maza tashi ka tafi,sannan idan ka nutsu kayi tunanin abinda muka ce.
Mu kwana lafiya ka gaisheta"
Haka badan yaso ba ya karbi kular hannun inna ramma ya fita Yana musu sallama ciki ciki.
Bayan ta tafi ne inna ramma ta kalli iyah tareda cewa,
"Amma iyah bakiyi mamakin yanda sumayyah tace baban gida take so"
Murmushi iyah tayi kaman mai nazari,can kuma sai tace,
"Babu shakkah ta gane abinda na fada matane,kuma ta canki amsar daidai kaman yanda nake tsammani,dan haka kaman yanda nayi alkawari idan ta samo amsar zan taimaka mata to zan taimaka mata,kuma samo amsar da tayi shiya sake bani tabbacin ta shiryu kaman yanda take fada,yanzune zata sam mecece rayuwar zaman aure,ba yanda samari da yam mata suke hasashen ta kasance ba"
Jinjina kai inna ramma tayi tace,
"Hakane iyah allah ya taimakesu,idan sukoma su sansanta kansu su zauna cikin inuwa guda shine mafi alkhairi,ai sai muyi fatan hakan,shikuma dole za'a wayar masa da hankali,yagane mai zai masa kyau a gaba ba wanda zai masa kyau yanzu ba"
Haka suka cigaba da zancensu duk bai wuce akan zancen sumayyah da Ahmad ba.

Yau anyi sati guda da kiran sumayyah wajen abbah,kowa ya fara mantawa da abinda yake faruwa,in ka dauke sumayyah da Ahmad,wanda kullum da abin yake kawana yake tashi,gashi yakasa fadawa maryam abinda yake faruwa,duk da yasan bazata nuna bakincikinta ko tashin hankali ba amma abun babu dadi gaskiya.
Ciwon iyah yayi tsanani na tarin da takeyi,wanda har an kaita asibiti sun bata gado.
Har sumayyah tazo wucewa taji hajiyah mama suna maganar da yah mu'azzam,wanda daga asibitin ma yake
"Eh baiyyi tsanani sosai ba,saboda na kaita da wuri kafim ya ci karfinta,kimsan jikinne yayi laushi said a hankali"
"Menene yake damuntane,naji ance wai sarkakewar numfashi ne kokuma asthma ce kai"
"Ah hajiyah mama daga mutum ya fara ciwon Numfashi sai a ceh asthma,ba Asthma ma bace,kawai dai sunce a huhunta ne matsalar,yanzu ma nabaro su Ahmad a can shida wani abokinmu suna cuku cuku,za'ayi mata scanning ne a ga a Ina ciwon yake tukunna,yanzu dai an saka mata oxygen,da sauki dai alhamdulillah"
"To Allah ya dada kiyayewa,bari nayi sallahr la'asar naje na dubota ,Allah ya sawwaka,ina iyalanka lafiya Kalau koh"
Sosa keya yayi irin kunyar nan kafim yace,
"Eh lafiya kalau ina cewa zan kawomiki ita ma ku gaisa kawa nan nan"
"To shikenan ba matsala sai tazo"
Daga haka sumayya ta wuce abinda take bayan ta gamajin abinda suke cewa.
Da la'asar kuwa hajiyah mama ta shirya driver zai kaita ta gano jikimnta,har tazo fita sumayyah tace,"ki gaisheta da jikin" a hankali.itama zataji hajiya maman tace,daga nan ta fice ta tafi.
Washagarin kwantar da iyah a asibitinne su sumayyah suka shirya ita da Muhibba akan zasuje dubota,adawo lafiya hajiyah mama tayi musu kafin suka tafi.
Tun kafin su isa kirjin sumayyah yake bugawa,dan Allah yagani bata shirya haduwa da danginba yanzu,wannan abin kunya da take tayi har yaushe.
Da haka babu yanda ta iya drivern ya sauke su a ya juya akan zai dawo bayan magriba ya daukesu.
A bakin kofar dakin sumayyah ta tsaya tana lekawa,yayinda Muhibba ta shige tana gaishe da inna ramma wacce take zaune akan kujerar mai jinya.
"Inna Ramma ina wuni ya mai jikin"
"Jiki da sauki Muhibba,har ta samu bacci ma,ke kadai kika zone,yah hajiyah mama"
Saida inna ramma tace ita kadai tazo kafin ta kula babu sumayyah a dakin,dube dube ta fariya tana cewa,
"Tare mukazo da anty sumayyah,banganta ba inaga ta tsaya a waje"
Murmushi inna ramma tayi kafin tace,
"Jeki shigo da ita kice tazo in jini"
Komawa Muhibba tayi ta sameta a rakabe a bakin kofar kaman munafuka,dariya Muhibba tasaka kafin tace,
"Inna Ramma tace ki shigo,yanzu sai taho koh"
Bat ace komai ba sai shiga dakin datayi kanta yana kallon kasa,
"Ina wuni inna ya mai jikin"
"Jiki da sauki,meye kuma na tsaya a waje uhm"
"Uhm dama dama babu komai dai"
"To shikenan amma karki sake tsayawa a waje kinji?"
"To "
Daga haka suka cigaba da zancen,duk rabinsa ma yawanci tsakanin inna ramma ne da Muhibba,sumayyah kam batace komai ba.
Wayar Muhibba ce tayi Ring suna ciki zance da wata kanwar inna ramma,dagawa tayi ana magana daga daya bangaren,bayan takashe wayarne ta kalli sumayyah tace,
"Anty sumayyah dama wata kawatace ta kirani akan sun yi schedule din wanna project dinner dazamuyi in group yau da yamma nan,shine nace ko natafi inyaso sai ki taho da drivern idan yazo?"
Tun kafin sumayyah tayi magana inna ramma tace,
"Tunda sha'anin karatune gwara ki tafi kam,inyaso sai ta tafi gida itah,gsshi abu aski yazo gaban goshi,allah dai yabada sa'a
Haka sumayyah badan taso Muhibba ta barta a wajen ba ta daga mata kai akan babu matsala zata iya tafiya.
Da sauri kuwa Muhibba ta fita daga asibitin tana tarar mai napep a hanya.
Bayan tafiyarta wajen shiru yayi dan itama kanwar inna ramman ta tafi,daga sumayyah sai inna ramma kawai,ji take kaman kasa ta bude ta shige dan Kunya da takura,tarin da iyah tayine yasasu saurin bada hankalin su kanta.
Yunkurawa tayi ta niyyar tashi inda inna ramma ta taimaka mata,ruwa tace a bata inda sumayyah tayi saurin dakkowa tabawa inna n.
Bayan tasha ne tayi hamdala tareda kallon sumayyah,
"Sumayyah yaushe kika zo,amma bayan nayi bacci ne koh"
"Eh iyah,ya jikinnaki "
"Hmm da sauki,abinda yake damuna shine wannan maganin na bacci,mutum yayi ta bacci kaman dan yaye haba ina da wannan al'amari"
Dariya suka danyi,jiki yafara sauki tunda iiyah tafara surutun ta.
Komawa gefe sumayyah tayi tai shiru kaman mai ciwon baki,saidia inda sunyi wani a bu tayi dariya.
"Yar nan kalau kike kuwa naga kinyi shiru,kodan abinda ya farune kika maidani abar kunyarki?"
"Uhm iyah kuyi hakuri nasan bai kamata na......."
"Bai Kamata kiyi mai ba,ni ina murna kin gane maganar dana yimiki kekuma kina wani zance,ai ki kawantar da hankali ki,yanzu na yadda da nadamarki fiyeda kowanne lokaci,kuma ina farincikin shigowarki cikin zuri'atah,kaman yamda na fada kuwa zan tayaki yakim gyara kiskuren da kikayi a baya,wannan babu shakka tunda gashi na tashi garau,Allah ya dafa mana"
Hawayene ya jiraro a fuskar sumayyah,tabbas wannan mutanen yanzu ta daina mamakin dattakonsu,gaskiya tayi kuskure a baya da bata samesu a matsayin dangin mijiba.
Allah yabata iko itama ta kyauta ta musu.
Har dare akayi magiba amma dirver bai dawo ba ya dauki sumayyah,tun abin bai dameta har ta danyi magana,
Ba laifi ta dan ware ba kaman zuwansu ba ganin yanda iyah take ta zanta da hira.
"Ahh mai daukar taki har yanzu bai dawoba kalau dai koh,"
"Ahah nima iyah bansani ba,bari na kirashi naji ko lafiya"
Daga wayar tayi suna magana can kuma sai ta sauka tayi shuru"
"Lafiya dai yake koh"
"Ahah yacemin yana dahowa yara suka saka kusa a hanya ya taka,yanzu haka ya kaita wajen gyara,to wajen da layi sosai,gashi babu dama yakara tukata zuwa wani wajen daban bazata tafiba"
"To wanna al'amari haka"
Suna cikin magana ne na rashin zuwan drivern saiga Ahmad ya shigo yana kakkada makullin hannunsa,direct wajen iyah ya nufa yana murmushi ganin ta tsshi kaman ba itace a kawamce ba.
Surutunsu na yau da kullum suka fara,dan ko kula da sumayyah a dakin ma bayyi ba"
"Innata maryam ta aiko abincin rana koh?"
"Ai basai ka tambaya ba,ta aiko mana,Allah dai ya muku albarka"
Ameen yace sai a sannan idonsa yakai kan sumayyah da take zaune akan kujera daya a gefe.
Gaisheshi tayi kasa kasa,koh amsa wa bayyi ba saima dago wani zancen dayayyi kaman bai jita ba,kuma yaji sarai abinda tace.
Inna Ramma ce tace,
"Baban gida idan zaka tafi ka mika sumayyah gida mana a hnayar ka ta wucewa"
"Inna tunda bata tafi ba sai na kaita gidan,da banzo ba fah wazai kaita toh"
"Kaga banason wani yarinta kuma,drivern ne yace motar ta baci yanzu,tunda gaka ai sai ka rakata koh,menene a ciki"
Toh yace cikin kasa kasa daga nan bai sake cewa komai ba.
Daya tashi tafiya ma hanyar waje kawai yayi abinsa bai cemata ta tahoba,saida inna ramma tace ta tashi ta bishi kafin ta bi bayan sa cikin dar dar tana musu sallama





🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now