Page.....27....

191 16 1
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...27....

"Banji mai kikace ba sumayyah anya kuwa najiki dakyau?"
"Eh abbah hakane,yah Ahmad na fitar a matsayin miji"
"Miji Ahmad kike nufi Ahmad dai wanda na daurawa aure da maryam"
"Eh abbah shine,........shine na fitar a matsayin wanda zan aura"
"Kuma shidim ne ya fadamiki zai aureki?"
"ahah abba bai san zancen ba nice dai na fitar dashi"
"anya kuwa sumayyah baki samu tabin hankali ba kuwa,kimsam mai kike fada kuwa,Ahmad zaki aura? Lallai ki farka daga mafarkin dakikeyi,wato kinga Allah ya rufa masa asiri ya auri mace tagari wacce tasan darajar nagaba da ita mai tarbiyyya,shine bari ki shiga cikinsu ki tarwatsasu koh,to baki isa ba,Ahmad da kika sani a da babu shiyanzu,wannan Ahmad din yafi karfinki ya wuce sa'ank,kuma ban lamunta ki shiga cikin zuri'arsa ki dagula ta.
Idan dan kin rasa wanda zaki kawone yasa kika fadi haka to aikinki yayi kyau,na baki nan da sati biyu kiyi nazarin maganarki kuma ki fiddah wanda zaki aura,tashi ki bani waje anan"
Ta shi sumayyah tayi kafafunta suna karkarwa tafito daga dakin abban,a bakin bangon dakin ta wake ta jingina tareda da dafe kanta dayake barazanar fashewa.
Wannan masifah wace iri ce,a rayuwar nan da wanne zataji,wai uban daya haifeta ne yake kiranta da masifa mai tarwatsa zaman lafiya idan ta shiga wani waje.
Wane abuse ta aikata haka daya gagara daina bibuyarta,anya kuwa zata iya jurewa.
Tafi kusan minti biyar a wajen kafin ta samu ta isa dakinta.key ta sakawa dakin ta zube akan gado tana fashewa da kuka,dan abinda abban yafada mata sunyi mungun tsayawa a cikin zuciyarta.
Hajiyah mama tana zaune akan gado tana gyara kayan su farouq tasuka zo suka cire Muhibba ta wanke musu ta kawo mata.
Daga kai tayi taga abbah ya shigo dakinnata ba cikin yanayin nutsuwa ba,abinne yabata mamaki,dan sai lokaci ziwa lokaci abbah yake shigowa dakinnata,saida kwakkwaran dalili tukunna.
Zama yayi aka kujerar dake dakin kafim yace,
"Maman yara kinji kuwa abinda yarinyar nan ta fadamin yanzu dana tambayeta akan waye ta fitar a matsayin miji?"
"Mai tace maka?"
"Hmm Wai Ahmad ta fitar a matsayin mijifah,kijimin wata magana mai rikita tunani"
Razana hajiyah mama tayi saidai bakaman yanda abbah yayi ba dazun.
"Haka tace,gaskiya abin da daure kai,to kodai dan ka tambayeta a gaggawane shiyasa ta fadi hakan dan babu wanda zata ce,inaga ka jinkirta mata kadan tayi tunani"
"Nima hakan na fada,shiyasa na ce nabata nan da sati biyu,amma zancen Ahmad wannan babu shi Kwata kwata,inbaso take ta maidani mutumin banzaba "
Daga haka abbah suka cigaba da tattaunawa da hajjya mama akan al'amarin har zuwa wani lokaci.
Ita kuwa sumayyah a yanda ta takwanta tana kuka haka bacci ya dauketa.
Da safe bata tashi da wuri ba,gashi kuma ranar aiknta ce,amma shiru bata fito ba,ganin hakane yasa su ladidi yin komai da komai,dan sun sa akwai abinda yafaru,dan saida dalili yanzu sumayyah take zama a daki da safe.
A wajen cin abinci hajiya mama hajiya mama take fadawa Muhibba abinda sumayyah tace a wajen abban,lokacin da ta dameta akan mai yasamu sumayyan taki fitowa,itama mamakinne yakamata har tana rike baki,
"Tabb hajiyah mama wanna bakaramin al'amari bane,taya sumayyah zata iyah kishi da maryam a yanzu,rannan fah ina ganin yanda yah Ahmad ya yi kaman bai ganta ba lokacin daya zo."
"Hmm nima nasan abinnan babbane,saidai bansan menene dalilin sumayyah na ambaton sunan Ahmad din ba,duk da tafi kowa sanin ya yakeji akanta yanzu,mudai idone namu yanzu kawai,Allah ya takaita kawai"
Saida aka shiga kawana na uku amma sumayyah ta daina sakewa da kowa tun abinda ya faru,yanzu takoma tamkar lokacin data dawo gidan,tsohon tabon yadawo danye shakaff,sai ta shafe lokaci bata sakkoba,shima abinci take zuwa dauka,duk yanda Muhibba tayi da ita ta sake da ita abin ya faskara,kullum idanuwanta a kumbure alamar tayi kuka ta koshi.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now