Page ...35....

184 21 4
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...35....

Hankalin ta kwance sumayyah tasha baccinta babu abinda ya dameta,dan dama tayiwa kanta training shanye komai,dan haka ba komai bane zai dameta a gidan bare ya daga mata hankali.
Wayarta ce yar karamar nokia ta buga alarm na tashin asuba a gefen pillown ta,tashi tayi tai addu'a tareda yin hamma kafin ta sako kafafunta kasa.
Bandakin ta shiga wanda sai yanzu ma ta tsaya tana karemasa kallo da gajiya tabar jikinta.
Ba laifi yana da kyau sosai,saidai karamine sosai.
Wata yar dariyah data tuna lokacin da salma ta fada mata abinda su anty maimuna suke cewa,
"Hmm wahalallu kawai,da sunsan abinda na shiga a gidana na baya da su dakansu zasuyimin sam barkan samun wannan dakin ma,su yanzu kayan duniya yadama da abinda yake cikinta,kuma indai ita din zasu saka a ransu to suna ruwa tsundum"
Kawai da tunanin ta tayi a ranta tareda kama ruwa kana kuma da fara alwala.
Bayan ta idar da sallhne ta dauki qur'aninta ta danyi karatu kafin tasake komawa kan gadon ta kwanta abinta.
Karfe bakwai dadai maryam ta fito kitchen ta fara hada kayan abin karyawa,dan Ahmad yayi mata text daga dakinsa akan fita zayyi,abin yabata mamaki amma ta danne,dan ita duk a zatonta ma yana dakin sumayyan a cam ya kwana.
Ba wani abu mai wahala ta dafaba dankaline ta soya sai source da tayi ta kuma dama kunun gyda,dan takula yana sonsa sosai.
Ta fito daga kitchen zata nufi daki tayi wankane ta ganshi ya fito daga dakinsa da jallabiya,da alama anan ya kwana,mamaki abin yabata saidai bata ce komai ba ta shige.
Wanka tayi ta shafe jinkinta da turare na kulaccah da humrah,kafim ta dauko wani bakin boyel yasha zubi har kasa ta saka.
Kwalliyah ta zauna yi har na tsawon minti goma kafin ta fito daga dakin domin zuba masa abincin.
A akan kujera ta ganshi yana dan dube dube a wayah,ganinta ne yasa ya dago yace,
"Honey kin makale a daki bayan kinsan ke nake jirah"
Duk Rabin hankalin sa yabata amma hakan bai hanashi karewa kayan jikinna ta kallo ba
"Kayi hakuri zaujee na tsaya saka kayane,kuma masu aikin ai dole suyi maka uzuri sunsan nice na rikeka"
Haka suka cikin hira har ta gama zuba masa abincin yafara ci,ganin tana tsaye har sannan ne yasashi dan tsayawa da cin abincin kafin yace,
"Yana ga kina tsaye,koba yamzu zaki ci ba"
"Ahah yanzu zanci bari na kira sumayyah tukunna"
Yana jin sunan da ta ambata ya gimtse fuska tareda cigaba da cin abincin sa,itama da taga hakan bata sake cewa komai ba sai wiceea datayi hanyar dakin sumayyan.
Cikin bacci sumayyah taji ana kwankwasa kofah,gashi bugawar taki karewa,dole badan taso ba ta katse baccin tareda sakkowa ta nufi kofar.
Tunda masu kawota suka tafi ta kulle kofar sai yanxu ta bude.
Had'a ido sukayi da maryam wacce take gabanta tasha uban ado cikin bakin boyel,ba laifi kam ko mahassadi sai ya yaba,dan dama itama farace da haskenta koda bata kai sumayyan ba.
"Lah maryam,ohh anty maryam kece da safennan ya gidan"
"Habaaa sumayyah kicemin maryam kawai menene na wani anty saika ce wanda na fiki,dama an gama abin karyawa ne shiyasa na kiraki kizo muci"
Dan  jimm sumayyah tayi kafin tace,
"Shikenan nagode sosai,bari ina zuwa zaki iyah tafiyah karna barki a tsaye"
Amsa mata maryam dim tayi kafim ta bar wajen ita kuma ta koma cikin dakin.
Lokacin da maryam din ta koma babu abinda Ahmad yace,sai cin abincinsa dayake a hankali. Itama nata ta zuba ta fara ci.
KO minti uku sumayyah batayi ba ta fito daga dakin,doguwar rigace a jikinta simple da dan kwalin data yafa akan ta,daga nan babu abinda tasaka a jikinta bayan spray mai karamin kamshi.
Tana zuwa jan kujera tayi ta zauna tareda kallon Ahmad tace,
"Ina kwana yah Ahmad"
Shiru kaman tayi magana da dutsi bai amsa mata ba,dan kallonsa maryam tayi ta gefen ido,daga gani bata ji dadin abinda yayi ba,shikuwa ko a jikinsa.
Basar dashi itama sumayyah tayi tareda kallon maryam ta tambayeta,
"Uhm anty maryam zan iyah diban kunu gyadan,dan bana iya cin abinci  i yanzu "
"Haba basai kin tambayeni ba ai dan zaki deba,bari na mikomiki"
Ta fada tana mika wa sumayyan jug din.
Duk abinda suke Ahmad yana kallomsu ta gefen ido,har sumayyah ta gama diban kunun ta fara sha.
Daukar jug din maryam tayi ta zubawa Ahmad dim a wani kofin ganin yagama cin abincin.
Saidai tana ajiyeshi a gabansa ya tureshi tareda mikewa yana gode bakin sa da tissue.
"Yana ga ka tashi zaujee,bazaka kunun ba duk yanda kake sonsa?"
"Basone banayi ba,da zaki iya yin wani yanzu zan sha,amma lokaci ya kure yanzu,wannan kuma gani nake kaman ya gurbata "
Wata kunyar ce tasake kama maryam ganin dagajin maganar da yayi da sumayyah yake dan ta dauki jug din ta tsiyanya.
Dauke kanta tayi daga kallon Ahmad din tareda mayar da idonta kan sumayyah dan taga wane irin yanayi zata shiga,dan tasan tagane maganar dayayi da ita yake,kuma ta jishi sarai,jitayi babu dadi dan koma mai yafaru laifinta ne ita ta kirata.
Saidai ga mamakinta sumayyan ko a jikimta,saima karisa shanye kunun da tayi ta kalli maryam din da dan guntun murmushi akan fuskarta.
"Nagode anty maryam kunun ki yayi dadi sosai,bari na shiga ciki,idan zakiyi aikin rana ki kirani saina tayaki"
Daga haka ta tashi a wajen ta nufi dakinta ko kallon Ahmad din natayi ba.
Shima tana barin wajen ya zari jakarsa ya fita da sauri kaman ana wullah shi,aka maryam ita kadai a wajen ta kaman kunkumi.
Jijjiga kai tayi tareda cewa Allah ya kyauta a hankali kafin ta debi kayan abincin ta kai kitchen,ta gyara wajen.

Bayan tafiyar Ahmad ta kusan awa biyu lokacin rana ta fara sai ga kiransa ya shigo wayarta tana zaune a falo tana kallo.
"Aslm zaujee ya wajen aikin?"
"Lafiya kalau,ykk ya gida"
"Lafiya kalau"
"Dama kira nayi na fada miki idan kika kuskura ta tayaki aikin gida na abinci to barmiki shi zanyi kaman yamda na bara kunun safe,duk kuwa da yunwar dazan dawo da ita bazan ciba,idan kinason na koma cin abincin waje to ki barta ta dunga saka hannu a abincin dazanci"
"Amma yah Ahmad naga dai ba guba bace a hannun ta kuma......."
Kitt taji ya katse kiran bai tsaya karisa jin mai zatace ba.
Sauke ajiyar zuciya tayi tareda kallon screen din wayar har ya dauke.
Sumayyah kuwa tun a wajen cim abimci tana komawa dakin ta nufi cikin jakarta ta dauko wani dan memo kafin ta zauna a kujerarta tana dubawa.
Ba komai bane a ciki said jerin abubuwan dazata dungayi a gidan.
Wani layi tabi da'aka rubuta gaisuwa ta sokeshi,sannan shima cin abinci tareda su shima ta sokeshi.
Kakkada biro tayi kafin tace,
"Rana d'aya a gidan har an soke guda biyu,bazan sake gaisheshiba sannan bazan sake cin abinci tareda su ba,wannan sun fita a cikin jaddawalin abinda zan dungayi a gidan."
Daga haka ta mayar littafinta ta ajiye ta koma ta kwanta tana kallon silin din dakin.
Wajen karfe sha biyu ganin maryam bata kira ta ba yasa ta fita,a tunanin ta bakunta take mata ganin jiya tazo gidan,dama kuma aikin zaman dakin ya isheta.
Wanka tasakeyi tasaka wata atampa tun ta kayanta ne ma gida,duk da bata sha jikiba amma tasha wanki.
Kitchen din ta nufah inda taji motsin maryam tana blending din wani abu a blender.
Shiga tayi tareda sallama tana murmushi tace,
"Lah anty maryam danace ki kirani kuma baki kirani ba,kawo na dayaki markadawar tunda naga wani abu kika saka a cikin wuta ma gashi can yana shirin konewa.
Kodan bari na juyamiki na kan wutan"
Matsawa sumayyah tayi da niyyar wucewa zata juya mata naman dayake soyuwa akan wutah,saidai tun kafin ta isa wajen maryam tayi saurin tashi ta dauki ludayin tareda juyashi kana ta tsameshi a mataci.
Ita dai sumayyah tana kallonta har ta gama tsamewar kana ta koma kan markaden da takeyi.
Ganin tsayuwar bazai kaita bane yasa ta juya da nufin barin cikin kitchen dan ta kula akwai abinda yake faruwa.
Har ta kusa fita maryam ta jawo rigar ta tareda sha gabanta tace,
"Amm sumayyah kiyi hakuri,bawai dan banaso ne na hanaki tayani aiki ba,yah Ahmad ne ya kirani dazu yace idan kika tayani abincin to bazai ciba,zai daina cin abincin gidan nasan yanda zamyi dashi.
Shiyasa kikaga nayi saurin daukar ludayin na tsame naman,kiyi hakuri sumayyah na hutasar dake aiki,kuma bazan ji haushi ba dam baki tayani ba,ki yi hutawarki kawai"
"Anty maryam karki ji komai,dama da dana shigo kin fadamin ma da zan fahimceki,mata tayi abinci miji bai ciba ai babu kanta,karki damu da hakan allah yabaku zaman lafiyah.
Barina tafi kawai,idan kin gama zan karki dunga sakawa dani ki barmin zamzo na dunga dauka a kitchen din,dan dama ni na saba diban abincina a kitchen"
Takarashe maganar tana dan murmushi da ta tuno da rayuwata ta gidan su.
Itama maryam din dan murmushi tayi ganin sumayyan ta fahimceta kafin tace,
"Nagode da fahimtarki sumayyah,gabadaya kin sanja ba kaman da ba,gaskiya nayi missing din waccer sumayyan"
Tafada yanzu tana dariyah,itama sumayyan dariya tayi kafin ta daga girah tace,
"Hmm duniya mai ta bari,wanda bai zobama zai zo ya sanja ballantana wanda yake cikinta kuma,karki dami nikuma nafison wannann sumayyan mai maida komai ba komai ba"
Daga haka sumayyah ta fita daga kitchen din ta KO ma dak in ta.
Littafin data ajiye dazu ta dauko tareda budewa,wajen da aka rubuta (taimako ta bangaren girki) tasaka biro ta kashe wajen tareda rufewa ta mayar.
"Yanzu na kashe uku kenan,sauran kuma naga daga nan zuwa zamana a gidan wannne da wanne zan kashe kuma.
Kai!! Gaskiyah zaman banza fah zanyi a gidanann,inaga mai zai hana na koma makaranta.
Aiki dankari ta taya kenan,yanzu sainayi baya da shekar daya da rabi fah dole,kuma ta ina xan fara komawa ma tukunna.
Anya zasu karbeni bayan marin malamin su danayi kuma ban bada hakuri ba?............ohnn ni ashe fah hadda alhakin raina malamai ma yana bina ba kadai na iyaye ba?.
Amma kuma ko wacce hanyace ma dole na bi,komin wiyarta kuwa.

Team sumayyah za'a koma makaranta fah.



🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now