page ....13...

154 21 0
                                    

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...13....

Da safe tun kafin sumayyah ta tashi mutari ya shirya ya fita,bayan ya ajiyewa mata kashin dumamensa da aka bashi.
Dan inna kekasa kasa tayi tace baxata bata dumame ba,saidai idan yau tayi mata tuwo to saita raba da ita inyaso.
Kasan cewar maganin da mutari yabata jiya akwai mai sa bacci shiyasa bata tashi ba sai wajen karce sha daya.
Bayan ta gyara fuskarta ta share dakin ta futo ba da wanda suka fara haduwa sai shema'u,suna hada ido kuwa ta gallawa sumayhan harara tareda murguda baki,ko kulata sumayya batayi ba dan a ganinta bata da lokacinta.
Kwanon dayake hannunta na tuwo wanda tafito dashi daga dakinta takai inda ake wanke.
Yau ba kamar jiyaba ta rutse ido taci tuwon sosai,dan ita kadai tasan wahalar da taji jiya da taji ci din.
Wajen ta tarar wayal an wanke kwanukan tass,hakan yasa ta dauki soson ta. Wanke kwanon nata kawai.
Bayan ta gamane tana dagowa suka hada ido da inna ta fito daga dakinta,tsugunnawa tayi tareda gaisheta,bata wani amsa gaisuwar sosai ba ita a dole fushi take da sumayyan.
Shiru sukayi babu wanda ya e komai,sai shema'u ce ta kore shirun ta hanyar cewa,
"Uhm nikuwa inna kaman ledar biredi nagani a bayan dakin mutari da kuma da k'wai"
Saurin Juyowa inna tayi tareda cewa,ke yar nan harda ta kwai ma?"
"Oh inna baki ganiba dazu,hmmm ai inna abubuwa dayawa sun sanja a rayuwar mutari,idan baki tashi tsayeba kina ji kina gani zaki rasa danki,gashi gaki baki isa da shiba,wai a gabanki ma kenan inaga kuma in an shiga daki,jifah yanda ya dunga wani kareta da safennan"
Duk zigon da shema'u takeyi tanayi tana kallon idon sumayya wacce ta yi kaman ma basa wajen,tana kuma murmushin mugunta.
Ita kuwa innna duk abinda shema'u take fada hawa take ta zauna daram.
Kallon sumayya inna tayi cikin tunzura tace,
"Bari kiji na fadamiki yarinya bazaki zo har cikin gidana ki mallakemin yaro a gabana ba,haba mana ni abin ya dauremin kai,mutarin dana sani a baya bashine na yanzu ba,duk yaro yabi ya susuce akanki.
Kuma daga yau ma kezaki dunga tuwon gidannan,awarata kuwa kullum ke zaki dunga doramin,idan kuma kinga bazaki iyaba ga nan hanya ki koma inda kika fito,duk ranar dakikayi tsallaken aikinki kuwa to bakida abinci a gidanannan"
Haka inna ta gama fadanta sumayyah tana jinta har ta gama.
Aikin awarar su inna suka fara shema'u tana daga baranda ta dora kafa daya kan daya tana kallomsu,mintuna bayan mintuna sai wayarta tayi ringing an kirata,wani ta amsa wani kuma tayi tsuka ta kashe wayar.
Haka ranar ma sumayyah ta niki aikin awarar kaman na jiya,dan ma yau da dama tunda batajin yunwa tashi abinci.
Da rana tayi fargaba tafarayi na tuwon dazatayi ranar,dan batama san ya akeyi ba bare tasan ta inda zata fara.
Da akayi la'asar kuwa taje da dauko tukunyar tareda hura wuta,shikansa wajen hura wutar saida tayi da gaske tukunna ta samu ta kama.
Dora tukunyar tuwon tayi ta cikata ruwa ta fara izawa,tana cikinyi har ta tafasa.
Dakin inna ta nufah tareda tambayar ta garin tuwon,buhun garin inna ta mikomata da kuma kwanon awu.
"Gashinnan ki auni kwano biyu ki tankadeshi,karkuma ki kuskura ki kara daga kwano biyun"
Tana gama fada mata tasake shigewa dakin,itadai sumayyah ko magana bayiba,idan tasake diban ina zata kaishi toh.
Jikinta fututu  yayi da gari kaman mai tashe,dan iska ake sosai ga kuma bata iya tankade da rariyar ba.
Tana cikin tankadanne shema'u ta shigo ta dawo daga tallen awararta,shekewa tayi da dariya ganin abinda sumayyah takeyi,sai fada sukeyi itada garin tuwon,dakin inna shema'u ta shige,saikuma daga baya sai gata ta fito a hankali kaman mai sanda.
Wayarta ta fitar yar karama ta danna kira,tana cewa eh kashigo yanzu nan"
Sumayyah bataji mai aka fada a daya bangaren ba,daga nan ta ajiye bokitin awarar tareda fitoda kudin cinikin,kirgasu tayi ta wari wani ta cusa a kugunta.
Bayan mintuna dayin wayarta ne wani gardin saurayi ya shigo gidan yayi irin askij yan karyar nan.
Shema'u ce tayi saurin jan hannunsa tareda nuna masa wani daki acan gefen gidan
"Yi Sauri ka shiga wancan dakin ka jirani a ciki ina zuwa,inna tana bacci nasan ba ji zatayiba,karka damu ba kowa a gidan,inyaso idan dare yayi kowa yayi bacci sai ka tafi"
Duk maganar da suke cikin kasa kasa sukeyi saboda kar inna ta jisu.
Saida shema'u ta tabbatar saurayinta ya shige dakin kafin ta rafkawa inna kira.
Fitowa innan tayi tana hamma ko addu'a babu,dan kawalin dayake hannunta ta daura tareda cewa,
"Ke ma'u menene haka kike wannan kiran kaman wata yarinya,yaushe kika dawo,kin siyar dukka koda saura?"
"Dukka nasiyar gashi kudin,amma wasu sun bata a cikin kudin,dan cikina ne yake ciwo to da ina kwancene wasu suka yimin sata"
Wani marairaicewa tayi kaman mai shirin zubewa a kasa saboda tsabar munafurci,saurin karbar kudin inna tayi tareda kirgawa tana cewa,
"Ayyah Sannu to da jikin,kishigo daki ki kawanta barina je dubo su dije su sayo miki magani"
"Ahah inna ki barshi,barina je dakin Dauda na kwanta har ya lafamin,karki bari kowa ya shigo dan banaso a dameni"
"Toh inna tace tareda sake cewa allah ya sawwake"
Haka ba kunya shema'u ta kama hanyar dakin da ta kira dana daudan,inda saurayinta yake jiranta,jijjiga kai sumayya tayi tana jinjina wannan al'amari da ta gani,wai bama namijiba har mace ta kawo saurayinta gidansu subaje tsiyarsu,wannan wane irin zamanine.
Haka dai ta cigaba da cakuda tuwon da takeyi,dan ita wannan shine babban aikinta.
Lokacin da tazo tuka tuwon da kyar ta tukashi duk kulli,miya kuwa ruwanta kawai ta zubamata da ajino moto sai kuma kuka da kalwa.
Sai yanzu dagane dalilin dayasa miyar bata da dadi,ashe dan batasamu Kayan hadi bane.
Bayan ta sauke tuwonne takira inna ta fadamata ta gama,banda ciwo babu abinda bayanta yakeyi,saboda bata saba ba kwata kwata.
Babu KO Sannu haka Inna ta balbaleta da masifa ganin yanda tuwon yayi kulli,itada dai batace komai ba duk kuwa da yanda taji haushin zagin da innan tayi mata,dan iyayenta ma saida ta zagesu tasss.
Wani kwano ta dauka ta zubawa sumayyan a ciki tareda mika mata tana mita.
Karba tayi ta nufi hanyar dakinsu,zuwa lokacin an yi sallahr magriba,har sannan shema'u basu fitoba itada saurayinta a dakiba,a cewarta batada lafiya.
Har takusa shiga daki saikuma ta dawo da baya ta nufi dakin da shema'u suka Shiga,kara kanta tayi a bakin kofar tanajin mai ake cewa,
Nishinsu ne ya cika dakin sai masha'arsu suke.
Tunani sumayya tafarayi can wata dabara ta fado mata.
Dakin inna tayi da gudu kaman an jefota,turus sukayi da inna wacce take zaune a tsakar dakin tana kirga kudin sana'ar ta,dagowa tayi ta kalli sumayya tareda cewa,
"Menene kuma kika dawomin,koh bai isheki ba kai?"
"Ahah dama dama,inna shema'u ce take ta nishi da ihu a dakin da take kwance,shine nazo na fadamiki ki duba ki gani ko lafiya?"
Tun kafin ta karisa inna ta tashi fiyat tareda nufar hanyar dakin daudan.
Inna tana zuwa batayi wata wata ba ta bankada dakin ta shiga,dawowa tayi ta gudu daga dakin tareda rafka salati,mutarine daya shigo yazo wajen yana tambayarsu meya faru.
Duk maganar da yakeyi inna bata kulashi ba sannan bata daina salatin datakeyi ba.
Saidaga bayane tace,
"Oh Ni diyar tasi'u mai zan gani a wannan duniya,shema'u shema'u shema'u,abin har yakai haka?"
Ganin bazata yi musu bayani ba ne yasa mutari shima shiga dakin,saidai shi ba fitowa yayi ba saurayij ya hau da duka kaman an aikoshi,dakyar ya samu hanya yazo ya fice da gudu.
Burburwa inna tafarayi a tsakar gidan tana kururuwa kaman yar bori,
"He heh her hehe Wayyo Allah naga ta kaina,shema'u ta kasheni a rayuwarnan mai zan gani ni kursiyya mai zan gani,shema'u gardi har gidanku kisa uwarki tayi mungun gani?"
Mutari ne ya tsugunna tareda rirrke inna wacce tayi tububu da rairayi wajen.
Hannunsa ta buge tareda cigaba da abinda takeyi,cokai cokai su sumayyah sukayi suna kallomta harda shema'u wacce tasaka kayanta ta fito daga dakin tana sunkuyar dakai.
Nunata inna take da yatsa tareda cewa,
"Shegiya annamimiya saboda tsabar ke karuwancinnaki yafi nakowa har gardi kika shigomin dashi gida saboda bazaki iya hakuri ba,to wallahi kafin ki zawomin abin kunya gwanda nayi aurenki na huta,nan da kafin azumi kice ya tura iyayensa wajen kawunki Dan ladi idan kuma ba haka ba koni ko ke a gidanna,shegiya hajira kawai"
Duk tsine tsinen da takeyi babu yanda mutari bayyi da itaba amma takiyin shiru,saida tayi mai isarta kafin tayi shiru tana maida numfashi.
Yaran gidanne da suka dawo daga yawonsu suka taru suka tsurawa innan ido,ganin tayi fututu da kasa tana zaune daram.
Ganin abin yafara yawane yasa mutari saurin daukarta tareda nufar dakinta da ita,dan shima abin ba karamin batama sa rai yayi ba.
Bayan ya kaita shema'u na tsaye sai jin karar bulala tayi ta ko ina,ihu tafarayi tana kiran inna tareda nufar dakinnata,inna tanajin ta iyo dakinta tai sauri ta saka sakata.
Saida mutari yayimata duka dan Kansa kafin ya rabu da ita ,zefar da bulalar yayi ya fita daga gidan.
Sumayyah tana zaune a dakinta taag shema'u ta shigo bakinta yana zubar da jini.
Tofarwa tayi tareda gode bakinta kafin tace,
"Nasan kece kika fadawa inna abinda yake faruwa,to burinki ya cika kin hadani da ita,saidai ina so kisani,bakici bulus ba bashi kika dauka.
Dan Kisaka a Ranki tamkar takin rrashin zaman lafiyar aurenki kika saya,dan abinda zanyi miki sai ya fi nawa,kuma muzuba nidake a cikin gidannan kafin na tafi zakiga abinda zanyi.
Tana gama fadan hakan ta juya ta bar dakin sumayyan,jijjiga kai sumayyan tayi,dan ita har ranta badan akamata tayi mata ba,tayine dan asan halin da take ciki ayi maganin abin,saidai gakuma yanda abin ya kare.
Allah ya tsaya dashi iya hakan......shine fatanta amma ba fatan shema'u kenan ba.

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now