Page....42...

199 25 2
                                    

     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...42....

Bayan dawowar su maryam shiru ana jira a ga wani sanji amma babu,tun suna saka rai har suka sallama wa Allah ikonsa.
Yanzu abin yayi sumayyah sauki,dan bata zuwa makaranta saidai idan aikinta zata kai dr hunu ya duba mata,ko yaushe tana wajen aikinsu,idan ta dawo kuma in an bata wani aikin tayi,idan kuma babu ta bincika abin karatunta.
Yanzu ta kara busy sosai,abinda hajiya Aisha take sonta dashi na jajircewa yafara fitowa,dan ji take da ita kaman tsoka daya a miya.
Hankalin ta kwance take sakata aiki yanda ya dace.
Wata rana taje aiki da safe,riga da wandone a jikinta na Pakistan sai gyalen daya yafa shima a kanta.
Mai napep ne ya sauketa a kofar wajen tashiga da kafarta.
Dayake tayi dan sabo da mutanen wajen,kusan wata uku kenan da zuwanta.
Office din hajiya aisha ta shiga kafin ta wuce nasu na ma'aikata,a zaune ta sameta tana duba wani abu a takarda.
"Sumayyah kece,an fito kenan?"
"Eh hajiyah ya aiki"
"Lafiya Kalau,dama akwai abinda nakeso nafadamiki,munyi da director mu na abuja akan cewa zan turaki ki kara koyon aikinki sosai,dan sun bude sabon samfuri wanda bamuda shi a nan,ko ya kikace,amma sai sanda kika shirya"
"Eh Toh Idan har za'a jira mai laifin nabari saina gama da makaranta tukunna,inyaso sai nayi service a can,ina zuwa wajen koyon"
"Eh to kin kawo shawara hakanma,inaga hakan za'ayi kam,Allah yabada sa'a ki gama din"
"Nagode da taimakon dakike min hajiya"
"Lah karki damu ba komai,nasan idan kin koyo din zamu bunkasa abinmu sosai,koya kikace,ni fah harkar samu bana raina ta ko kadan"
Dariya sumayyah tasaka kafin ta bar office din.

Lokacin da su sumayyah suka karbo takardarsu kuwa ta service,murna kaman ta nutse.
Da gudu ta shigo gidan da yamma,dan tun sake suke can ana ta bikin samun nasarar gamawa.
Wayah ta daga ta kira salma.
"Hello aminyah ya kike,nasamu nasarar karbar takardata a yau,ki shirya zuwana abuja dan dama can cika kuma nasamu"
"Dan allah kicemin dagaske,kai amma naji dadi,a gidana zaki zauna kuwa ina koh"
"Inshaallah kuwa,ki kawantar da hankalin ki ina nan xuwa,naso cika garinmu ma dan bazasu bani bane banida hanya,da badan haka ba kinsan bazanzo gidanki na dade ba.
"Karki ce komai tinda zakizo din shikenan"
Da daddare su ahmad na zaune shikadai a falo da waya a hannunsa sumayyah taje gefensa ta zauna.
"Barka da dare"
Batayi tsammanin zai amsa ba saikuma taji yace mata barka.
"Uhm dama na karbo takardata tayin service yau,zanyi ne a garin abuja can akayi posting dina"
"Yayi kyau allah ya taimaka,yaushe zaki tafi?"
"Wani satinne"
"Allah yakaimu"
"Ameen"
Daga haka sumayyah ta karbi takardar tata dake wajensa tada bashi ya gani ta nufi dakinta.

Washagari taje gida tayi musu sallama,shikansa abbah yaji ance takoma makaranta,bai dauka dagaske bane saida tace masa zata tafi service.
Fat an alkhairi yayi mata harda kudi tayi gujiri.
Shiryen tafiyar sumayyah take tayi,itama hajiya Aisha tayi mata ihsani sosai,harda kuma takardar dazata nemi ma'aikatar shugabannata daya bukaci sumayyan taje.
Shima Ahmad kudi mai yawa yabata ranar dazata tafi,ya kaita tashar shiga mota tareda yi mata fatan alkhairi.
Duk da bada magana amma kuma rabuwa da gidan dazatayi saida taji babu dadi,musamman ma maryam dasuke zama wani lokacin suyi hira.
Da mamakin dan sauyawar Ahmad din tabar garin,Koyaushe sai ya dunga abinda batayi tsammani ba.

......Bayan shekara daya......

Abubuwa da dama sun faru,sumayyah tagama service dinta harta karibi certificate na shaidar gamawa,farincikin da taji da kuma jinjinawa kanta kar a so a Tona.
Sannan kuma tadawo da nan ma shaidarta na kara koyon ilimin design,na zamani wanda ake yayi. Hajiya Aisha bakaramin ji da ita take ba.
Salma ta haihu danta na miji,dan sumayyah tana can ma ta haihu,haka humairah ma matar yah mu'azzam itama ta haifi yar ta mace(zainab ana cemata yusrah) mai sunan hajiya mama.
Anty Maimuna kuma mijinta yakara mata kishiyah,kullum yanzu cikin masifah suke.
Ita kuma Muhibba tukunna,amma tsohon cikine da ita itama.
Kowanne gida ya cigaba,iyah nasu Ahmad aka sakawa ido,dan yanzu mutane har sun fara zargin ko haihuwar daga shine,dan idan ita maryam bata haihu ba to sumayyah fah(babu wanda yasan dawar garin)
Allah bai bashi da ba amma kuma aikin kasuwancinsa ya bunkasa,dan yanzu har company ya shiga na hadin gwiwa shida yan kasuwa.
Amma haihuwa kam shuru,kullum maryam har ma da sauran dangi abinda suke jira kenan.
Uwar gayyar kuwa babu abinda ya dameta da daga hankali. Ba laifi yanzu ta shiga dutyn abinci,amma shiri kam har yanxu yar gidan jiyace.
Da alama kowa yagane matsayin kowa a zuciyarsa,amma kuma yarda da hakan shine yazama abin matsala.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now