Page....20....

176 19 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...20....

A bakin kofar shiga falon ta tsaya tana motsi da baki,da alama addu'a take ta neman karfin gwiwa,duk da addu'ar da take sai ta zo shiga kuma sai tasake tsayawa,duk tayi gumi shirkif na fargaba.
Maganar hajiyah mama tasji a baynta wacce sai sanann ta iso wajen,
"Me kike a tsaye a wajen har yanzu baki shiga?"
"Uhm dama dama Bakomai"
Haka babu yadda ta iya tasaka kanta cikin falon,da yah naseer suka fara hada ido,wanda yana kallonta sau daya ya dauke kansa,shi dama basa shiri sosai,dan gwanda ma yah Isma'il wanda yake Egypt shida matarsa anty hafsa,saura wata biyu ta dawo ya gama kammala karin karatunsa shiikadai ne yake shiri da sumayyah a gidan,amma inka dauke shi sauran saidai su zauna da ita dan babu yanda zasuyi.
A tsakar dakin ta samu waje ta zauna gefe da Muhibba kadan,ko dago kanta batayi ba tafara gaishe da abba daga hakan,
"Abbah ina wuni ya gida"
"Lafiya"
Daga haka wajen yayi tsit,kkwa yana zaune a wajen da matarsa,sai anty Nafi da kuma Anty Hajara wacce ita suke gari daya da baffah Usman tana auren dansa,ita kuma itace takebin yah naseer.
Dukkansu mamakin haduwarsu lokaci guda a wajen sumayyah tayi, kuma duk ta dalilin ta suka taru,gaskiya batayiwa kanta adalci ba sam.
Abbah ne yayi gyaran murya tareda cewa,
"Hakika nin gaskiya nayi niyyar korarki daga gidanna sumayyah lokacin dakika dawo,saidai yayah usman yayimin magana tareda roka miki alfarma da barki ki zauna .
Maganar gaskiya zan barki ki zauna a gidannan amma akwai sharadi masu yawa,inaso idan na fadamiki saiki zabi wanda kikaga yafimiki,idan kuma basu miki ba kkfa a bude take kika ma hanya zuwa inda kikaga yafimiki,kuma karna sake ganin idonki har na koma ga Allah"
"Abbah ina sauraren sharadinka kuma inshaallah zan amince da duakkan abinda zaka fada"
"Sharadin shine,duk wani aiki a gidannan na goge da kuma abinci kezaki dungayi,gyaran wajene kawai masi aiki zasuyi,saboda kincemin na taimaka miki na barki ki zauna,to zakiyi aiki a maimaikon hakan,saboda har yanzu ban sakkko daga hukuncin dana zartar a kanki ba na bakya cikin y'ay'a na,ina nan akan bakana har sai naga yanda kika dora rayuwarki tukunna,sannna yanzu kina cikin iddah,to zaki zauna a cikin gidanane tsawon lokacin da kike iddah,kina gamawa a washagari nakeson ki kawomin wanda kika fitar a matsayin miji,dan bazan juri ganinki ba a gidannnan.
Wannan shine sharadin idan kinga zaki zauna a gidana"
"Eh abbah naji duk abinda kace,zan zauna bazan tafiba,kuma inshaallah zanyi iya kokarina wajen nayi aikin dayake kaina,nagode sosai"
Dukka wajen kowa tausayinta yaji harda yayunta maza,musamman ma hajiyah mama Wacce runtse ido kawai tayi,saidai duk da haka abin yamata dadi ganin abbah bai matsa akan korar sumayyah bah.
Daga haka taron ya watse kowa babu abinda yake cewa sai alhini kawai.
Share hawayen idonta sumayyah tayi tareda mikewa tsaye ta fice daga dakin lokacin da kowa ya fita.
A tsakiyar falon da samu akwatinta data ajiye ,kowa yana kallon ta babu wanda ta kalla ta kinkimi akwatinta tayi hanyar dakinta.
Budewa tayi ta shiga da kayanta,tana kallon dakin wanda yahada uwar kura,duddubawa tafarayi tareda komawa ta dauko tsintsiya da mopa,dan ta yanzu shiansa shashenna su itace mai gyarashi to inaga kuma dakinta.
Zagewa tayyi da gyara dakin tass,duk kuwa da haki datakeyi saboda rashin karfin jikinta.
Sai can wajen yamma ta gama gyaran dakin,matan yayunta duk sun tafi harda babbar yayarsu mace anty hajara,taso tayiwa sumayyah magana amma sumayyah taki yarda,dan a sharudanta hadda karta karya doka,idan ta karya korarta za'ayi.
A baya bata tsoron korar amma tunda taji furucin hajiyah mama akan mai zata ji idan ta shiga duniya yasa zata jure komai dan ta zauna kusada mahaifiyar tata.
Saida ta gama gyaran tsaff kafin ta shiga wanka,ruwan zafi ta tara mai zafi sosai ta wanke jikinta kafin ta fito daga bayin.
Riga t-shirt da zanin falle ta saka,dan gudun karta tsufar da kayanta tasan bayi mata wasu za'ayi ba.
Sakkowa tayi tashiga kitchen din inda ta samu su fatsima suna kokarin dora abincin dare.
Saurin tsugunnawa sukayi da niyyar gaishe da ita,amma sai ta dakatar dasu tareda yimusu murmushi,abinda yayi bala'in shigar dasu cikin mamaki kenna,dan sumayyah a lokacin baya ko kallonta kayi a rashin sani sai ka karbi rabonka a wajen ta ,amma wai itace take musu murmushi tabb.
"Ahah Dada fatsima basai kun gaisheni ba da haka,sannunku da aiki,dama inaso na fada muku yamzu nice zan dunga abincin sashennan dukka,ku an huta sar daku harda ke ma ladidi,basai kinyi gogen falo ba ni zan dungayi"
Dukkan su zaro ido sukayi a tare suna kallonta,anya kuwa sumayyah kalau take,shine abinda suka fada a ransu.
Itama ganin hakan fadada Murmushin ta tayi tareda jijjiga musu kai alamar hakane.
Shinkafa ta debo ta tuwo tafara gyarawa,wanda ganin hakan yasa su fatsima karba da sauri dan su tayayta,har yanxu jikinsu a sanyaye yake da al'amarin,itadai banda murmushi babu abinda take musu,idan tayi musu tambaya wani su amsa wani kuma suyi shiru.
Da haka har suka gama yin miyar ganyen dakuma tuka tuwon,tafiya sukayi suka hada kayansu domin tafiya gida,tunda aikin lokacin yakare.
Har sun kai bakin kofah sumayyah tabisu da gudu da kula guda biyu a hannunta.
Mikawa kowacce tayi tareda cewa,
"Zaku tafi bakuci tuwon ba,kuma ke ladidi naji kina cewa kina so?"
U hmm uhmmm shine kawai abinda suke cewa kowa tana kallon kowa,hannunsu yana rawa suka karbi kular a hannunta,dan gani suke kaman idan suka karba zata hukunta su ko taci musu mutunci.
Bayan sun karbane tayi musu murmushi tareda cewa,
"Nagode da taimakonku yau,karku damu ku saki jikinku ku daukeni kamar yar uwarku,sai gobe da safe"
Daga haka tajuya koma ciki ta barsu da mamakinta.
Komawa kitchen din tayi ta zuzzuba kkwanne a inda yadace,da daddaya take dauka tana kaiwa dining har gama tsaf.
Dakin hajiya mama ta leka tareda cemata ta gama,to tace daga nan bata sake cewa komai ba.
Nata abincin ta dauka a flate tashiga dakinta.
Tana gamawa takai kwanon kitchen daga nan bata sake fitowa ba ta zauna a dakinta.

Tana zaune ita ba waya ba ita kadai,har zaman ya isheta ta kwanta.
Da safe saboda baccin da tayi da wuri tun kafin kowa ya fito ta gama abincin karyawa tsaff,ta hau gyara kujerun falon da goge.
Tana cikin yine harta kusa gamawa su ladidi suka shigo,rike baki sukayi ganin aikin da sumayyah ta zage tanayi,wacce da sai takai azahar tana bacci,inba hajiya mama ce ta taka taje ta tashe taba,dan har jarabawa tasha missing akan bacci.
"Yadai kuka tsaya kuna kallona,har na gama aikin ai,breakfast din ma nayi shi"
Abbah ne ya fito daga dakinsa da jaka a hannunsa,da alama wani waje zaije,dayake sumayya ta juya masa baya bata ganshi ba sam.
Saida taga su ladidi sun durkusa kafin ta juya.
Saurin durkusawa itama tayi hannunta rike da mopa suna gaisheshi a tare.
Amsawa yayi lokaci daya yana nufar hanyar wajen dining din.
Tun kafin fatsima taje ta zubamasa har sumayyah ta rigata,kanta a sunkuye take zubamasa harta gama bata dago taga mai yake ba,shima kuma bai ce mata komai ba kaman bai santa ba.
Abin dole yana cimata rai saidai idam ta tuna da rayuwar datayi a baya wannna rahama ce tafara samu daga Allah.
Dakinta ta wuce bayan tagama aikin data tabbatar ita zata dunga yinshi kullum,sukuma su ladidi suka tafi gyaran gidan ta waje.
Yauma daga abincin safe har na rana dana dare a dakinta taci,sanda take dakinta kuwa bata shiga harkar kowa,ko su yah mu'azzam sun shigo iya kacinta dasu gaisuwa,daga nan kuma babu abinda yake hadasu da ita.
Bayan wata daya da dawowar sumayyah gida komai yana tafiya mata da sauki,zuwa yanzu tasaba da ayyukan tadake,dan hatta kayan miya da abinda ake bukata ita take gudanarwa.
Ayyukan yanzu sam basa mata wani iri ganin tana yinsu,sannan tskaninta dasu ladidi yanzu shakuwa ta kullu,dan idan babu abinda take can take zuwa gunsu suyi ta hirar duniya harda shewa ana tafawa.
Duk da yanzu jikinta ya mirmure fatarta ta danyi kyan gani amma babu wani abin burgewa a tattare da ita,kulllum idan ka ganta da t-shirt ce a jikinta da zani,bata da mai bare hoda,dam abun biyar babu wanda yayi mata tun sanda tazo gidan.
Salma ce ma takawo mata karamar waya da kuma dan kudi akan kozata bukata.
Saidai ita ayanzu ko sha'awar rike kudin ma batayi bare sakasu a cikin zuciyarta,dan takula sudin fitina ce ba karama ba.
Yau ma kamar kullum ta gama abincin rana takai dining,maimakon ta shige daki saita nufi bagaren su ladidi,dan yau batajin zaman dakin kwata kwata,ga jikinta datakejinsa ba dadai ba.
Abincinsu ta dauka a kitchen ta tafimusu dashi harda nata kason.
Suma suna ganinta suka karbi kwanon ladidi tace,
"Yar uwa sannu da lekowa,yau ya muka ganki da rana haka"
"Hmm za man dakinne yau ya isheni banajin kwanciya"
"Uhmm to Sannu da zuwa"
Abincin suka zuba ana ci ana zance har suka tabo zancen AHMAD gaban sumayya ne yafadi rigiff har saida ta dafe kirjinnata,mamaki abin yabata ganin yadda abin ya doketa daga kiran sunan sa kawai,kallon ladidi tayi tareda gyara zama tace,
"Naji kince ahmad yazo gidannan yaushe kenan?"
"Tab ai inde yah Ahmad ne yana yawan zuwa gidannan sosai,kwanan nan ne ma naga yadade bai zoba,wani lokacin ma tareda matarsa maryam suke zuwa,ayi ta hira a falo kafin su tafi,tabb ai yanaji da matar nan tasa kaman tsoka daya a miya,abu kadan zai kalleta,idan muka kaimusu abin sha muna gani.
Gashi yazama dan gaye na nunawa a taro,daff naji ance fah har plaza shida wani suka hada kudi suka bude,saidai abin tausayin matarsa har yanzu bata haihuba,nasan abin yana damunsa sosai,kuma ........."
"Kidaina wannan zancen ladidi ya isa haka,bari na dan shiga ciki,danji nake kaman cikina ya baci"
To kawai suka ce mata kafin ta tashi da sauri tayi cikin gidan har tana hada hanya,har zuwa lokacin zuciyarta bata daina bugawa ba ,ka jikinta gabadaya yayi sanyi.
A bakin madubinta ta tsaya lokacin da ta karisa dakin tana kallon kanta a ciki.
Hawayen dayake zuba a idonta ta kallah ta cikin maduvin,hannunta takai ta lakata tareda karemasa kallo,tabbasa hawayene to amma na miye hawayen ???......,.....

Yan team dinki watakila zasu san na menene😀😀😀💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼


🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now