page...14...

162 15 0
                                    

    🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03


🏵🏵🏵
...14....

Da safe da wuri sumayyah ta tashi ta share gidan tass,tayi wanke kafin ta koma daki,dan inna kam ko fitowa tsakar gidan batayi ba tun shigarta daki jiya,yau babu sana'ar safe haka ta Rana ma,saidai kowa yasan yanda zayyi kawai.
A zaune sumyya take tayi tagumi kaman mai zaman makoki jin gidan yayi tsitt kuma duk a sanadinta hakan ya faru,duk da tasan batada laifi amma saida taji wani iri aksn abinda tayi din.
Dumamenta ta dauka ta ci kafin ta koma ta dan gishingida akan gadonnasu.
Abinda yafaru agidan su sumayya har yafi wata yana dosar shirin yin wata biyu amma har yanzu inna bata dawo normal ba bare kuma uwar gayyar,dan yanxu ta daina zuwa talle dije ake dorawa kadan zuwa bakim kofar gida.
Yanzu iya abincin dare kawai ake na rans kowa yasan yanda zayyi.
Mutari ba afi sati daya ba da yana siyamata dan shayi daga baya ya daina,a cewar sa zata cinye masa jarin dan shagon daya bude a kofar gidansu,duk da shima cinyewar yake.
A tsakar dakinnasu ta baje kafa daddaya a dole tan shan iska saboda gumin da akeyi,yunkurawa tayi a hankali zuwa bakin kofar dakinnasu ta amar da duk dan kunun gyadar da dije ta siyo mata,kuskure bakinta tayi kafin ta dawo dakin ta zauna tana maida numfashi na wuyah.
Baccin wahala ne ya dauketa sai can wajen magriba ta samu ta tashi tayi sallah,tana kan sallayar mutari ya shigo gidan yana ta mita wani mutum ya sayi garin kwaki bashi har yanzu bai kawo kudin ba.
Juyawa tayi gefensa bayan tayi sallama tayi masa sannu da shigowa.
A dakile ya amsa ransa a bace,dan yasan idan ta kulashi a kwanannan toh so take ta tambayeshi wani abu,kaman kuwa ya shiga zuciyarta ya ji tace,
"Baban dije dama inason zuwa asibitine,tun jiya nake amai ga kuma marata da naji tana ciwo"
"Tabb amma zance kike,yanzu dan kawai bakya jin dadi saina baki kudi kije asibiti?,saboda kece yar gold ko,amai kam ai zai tsaya,ciwom ciki kuwa kisha kanwa inna tana da ita ki karba a wajen ta"
Yana gama fada ya tashi zai fita,sumayya ta bude baki zatace wani abu yayi saurin katseta tareda cewa,
"Kinga dan Allah karki dameni,nasan bazai wuce cikine dake ba kike laulayi,dan haka na fadamiki abinda yake damunki ma kada ki wahalar da kanki,idan kinga zaki haifeshi ga waje nan sai yazo yaci uwar da zai ci,in kuma zubar dashi zakiyi kaman yanda na taimakeki a na farko shima ga wajennan,dan yanzu babu ruwana dan kin haifeshi,iya kaci nayi masa suna shikenan daga nan mun rabu,inna mijine idan ya girma ya jona almajiranci wajen yayansa,dan allah yaga bazan iya wahala ba,nima naji da kaina"
Jijjiga kai sumayyah tafara tana hawaye tareda dora hannunta akan cikinta bayan mutari ya fita.
"Wayyo Allah Wayyo ni,mai nasaka kaina a ciki,anya kuwa nan gidan yan adam ne,wayyo abbah wlh na tuba ka yafemin abinda nayi,nasan hakkinku bazai taba barina ba,yanzu haka ma mutuwa zanyi ban hadu daku ba,dan allah ku yafemun idan kun tuna dani a rayuwarku ,inna lillahi wa inna ilaihi ra jiun,allahummma ajirni fi musibati"
Haka ta cigaba da sambatunta har tayi shiru dan kanta,tana kan wajen bata sauka ba dije ta shigo dakin da gudu.
"Sumayyah (KO anty babu,dan baban su ma da sunansa suke kiransa) wai kizo inji inna ki dora tuwo yamma tayi"
Wani irin ihu sumayyah tayi tareda gallawa dije harara,da sauri ta bar dakin kunkuni.
Komawa tayi tai kwanciyarta,dan yanda take ji a lokacin uban kowa ma ya mutu shiyasani.
Hayaniya ce ta tasheta a baccin daya dauke ta,muryar su mutari takeji da kuma muryar wani daban ba mutarin ba.
Matsowa tayi ta daga labule domim taga abinda akeyi,muryar inna taji tana cewa,
"Yanzu dauda kayiwa kanka adalci kenan nima kayi min,ka duba kaga yanda aka kawoka cikin gidannan an karya maka kafa har ta rube sannan aka dawo dakai,saboda ka gamawa yan siyasar amfani nukuma an kawomin nayi jinya koh? Wannan masifa ta ku yaushe zan hutane,kai wata haihuwar gwanda ma mutum bayyiba wlh"
Duk maganar da takeyi cikin kuka takeyi tana face majina da gefen zaninta.
Shikuwa wanda aka kira da dauda yana zaune a baranda ya sunkuyar da kai,ga kafafunsa sunyi suntum sun kumbura,sukuwa wanda suka kawoshi samari ne biyu da sauri suka fita sum sum jin inna ta zare sai masifa take.
Sakin labulen sumayyah tayi Bayan ta gama jin abinda ya faru.
"Wata cakwakiyar kenan"
Tafada a hankali tana ajiye numfashi.
Dije ta kira ta siyo mata shayi a kudin da tadan samu bayan tayi kananan aikatau na gida,lokacin data kawo mata gidan ya cike da ihun dauda ana dorashi a karayar sa,hakanne yasa ta ajiye tareda zuwa wajen dan ta ga mai yake faruwa.
"Wayyo inna kice su bar tabamin kafar nan akwai ciwo innaaaass"
"Dallah yimin shiru gardin banza,baka da aiki sai tsiya a anguwa ko nace gari,ku a dole ga samarin da basa tsoro yan daba,shine yanzun zaka budemin murya kaman goge kayi ta ihu? Ai wallahi dan hannunka baya rubewa ka yanke ka jefarne da tuni na nuna bansan ka,dukkan ku idan dadine bazan gankuba sai wahala ta sameku ku iyo kaina kuna cewa inna,saboda inna batada rai ita batasan dadi ba koh?"
Shiru dukkan su kukayi harshi da ake gyarawa kafar,dan dukkan su har sumayya sun san anan kam gaskiya ta fada,koda wani abin tanayin son zuciyarta amma kyautatawarsu a gareta yyai karranci sosai,koba komai tana bukatar kulawarsu (hmmm yaran yanzu ance duk haka suke,saidai iyaye suyi wahalarsu badai su sami dadi su nemi iyayenba,wayaga d'an kaza samu ka k'i dangi)

Mai Dori Yana gamawa ya nade kafar tareda da bada wani magani a dunga shafa masa,sannan yace a dunga kula sosai saboda abin ya baci sosai.
Mutarine ya tattageshi da kuma wani saurayi dan anguwar tasu aka kaishi dakinsa na gidan.
Itadai inna har aka gama bada dawo dadai ba sai jan zuciya take,abin duniya ya isheta.
Sumayyah ce ta matsa kusada innan da niyyar dafa kafadar ta,aikuwa ta kaiwa sumayya wani duka tareda cewa,
"Ke Dallah kyaleni karki isheni da iyayi,ki barni naji da abinda yake raina kuma"
Daga haka ta bankada labulen dakinta ta shige.
Bayan wata guda da kawowa dauda gida har yafara takawa da kansa,duk da ma ba wata kulawa yake samu sosai ba.
Sumayyah kuwa cikinta yafara fitowa,saboda ba wani jikine da ita ba ta rame ta kwanjame saboda wahalar ciki da kuma karancin kayan abinci na gina jiki,ga kuma rashin kulawar ta miji.
Sai kayanta ta daga wasu ta siyar tafara yar sana'a tana dorawa dije,shi dinma nan da nan take cinye kudin ribar a cikinta saboda kwadayin ciki.
Yau din ma dai jiya ya yau,fada suukayi da mutari akan ya kawo kudin siyan kayan hadin miya,dan inna tace bata da kudi,da haka ya dauki borin koro kunya akan indai shi ake zubawa ido to ya fasa cin tuwonma,dama wani sarin kaya zai shiga cikin gari sai dare ya dawo.
Haka babu yanda zasuyi sukayi miyar haka daga gishiri sai daddawa,kowa yaci kaman zayyi amai.
Tun abinda ya faru na fallasa shema'u,shikenan ta daina kula kowa a gidan,wani lokacin ma sai kowa yayi bacci ta dawo,yau kuma tana zaune a barandar inna tana yanke farce,duk abinda ya faru tsakanin sumayyah da mutari akan idonta tana kallonsu har ya dau jakarsa ta kaya ya fita,wani Murmushin gefen baki shema'u tayi tareda jijjiga kai tana kama fatar kasan bakinta da hakoranta.
Ita kuwa sumayyah da ta gama aikin da zatayi tayi sallah kwanciyarta tayi,dan dama kowa ba kula kowa yake ba a gidan yanzu,duk abinda kayi ruwanka.
Iya vest ce a sai jani saboda zafin da akeyi,wani numfashi ta ajiye da hakarkarinta ta kwanta akan kafifar,duk da babu laushi sosai amma yafi dai babu.
Ba wani bata lokaci bacci ya dauketa mai nauyi na wahala.
Sai wajen karfe sha biyu kafin mutari ya dawo gidan,dan dama dui sati idan yaje sari yakan kai dare sosai,hanyar dakinsu ya nufah dan yasan zuwa yanzu kowa yayi bacci a gidan.
Turuss yayi a bakin kofar dakin ganin takalma guda biyu,dana sumayyah saikuma takalmin wani gardi wanda ba mai shi a gidan,mamaki abin ya bawa mutari amma sai ya daure ya shiga dakin.
Tantamarsa ce ta share ganin wani katon gardi a kwance a gefen sumayyah yana ta bacci,itama kuma ta jingina bayan ta a bayansa tana ta bacci.
Wani gumi ne ya karyo masa wanda har yafi na lokacin zafin.
Kwalkwalwarsace ta kulle har ma yarasa mai zai fara,wai gardi ne a wajen kwanciyarsa,anya kuwa ya gani dadai.
Wani kwano a gefe ya zara ya rafka masa akai da dukkan karfinsa,saidai yayi bai sameshi sosai ba yakara kaiwa a na biyu,zuwa lokacin mutumin ya farka har yayi kokarin rike kwanon a hannun mutari.
Kokuwa suke kaman a filin kokuwa,kwartonne ya daga mutari ya bugashi da kasa dimmm sannan ya hau kansa da duka kaman an aikoshi,saida ya tabbatar ya dakashi sosai kafin ya bude kofar ya na shirin fita wanda dadai tashin sumayyah kenan daga bacci.
Tana kallon mutum a dakinsu ta kwala wata uwar kara duk a zatonta barawone.
Inna tanajin karar tayi saurin fitowa dadai lokacin da mutumin ya fito daga dakin su sumayyan yayi waje da gudu.
Salati tafara wanda hakan yasa itama shema'u ta fito daga dakin innan.

Daga ido mutari yayi da kyar yana gallawa sumayya wata uwar harara wanda da kyar take kallon idonsa ma saboda karancin hasken fitilar dakin.
"Baban dije mai mutumin nan yake a dakinmu,ko biyoka yayi sata kai?"
"Satar kundun ubanki yazoyi,nazo na ganshi kuna bacci cikin kwanciyar hankali keda shi kuma yanzu kicemin wai meya ke a dakin?"
"Lafiyar ka kuwa,harda zagin ubana akan me kuma"
Wani duka mutari ya kaiwa sumayyah cikin karfin hali duk da kuwa yanda jikinsa yake tsami saboda dukan da kwarton yayi masa.
Muryar inna da sumayya taji ne yasa ta fita da gudu,dan duk a zatonta kaman mutarin ya samu hankali.
"Meyake faruwa lafiya,kodai barawone ya shiga muku,dan naga wani mutum ya fito dag wajenku zuwa waje"
Mutari da yake dakin da yajiyo mai inna take fada ya fito da sauri tareda cewa,
"Barawon me kuma?,kwarto ta kawomin har cikin dakina na aure,a kwance na ganshi a bayanta suna kwance"
Wani salati na munafurci shema'u ta rafka da karfi tareda cewa,
"Biri yayi kama da mutum,dan dama nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,kwanakin baya ma na ga wani ya fito daga dakinta da daddare lokacin da mutari baya nan,nidai ban ce komai ba na yi fitsarina na koma,amma daman nasan koba dade koba jima asiri dole zai tonu,gashi nan kuwa rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya"
Dukkan su dajin furucin shema'u duk sai suka maida idonsu kan sumayyah suna mata kallon tsana.
Ganin lokaci daya sun aminta da abinda shema'u ta fadane yasa sumayyah sunkuyar da kanta idon ta yana zubar da hawaye,a zuciyarta ta ambaton sunan Allah,dan tasan duk duniya yanzu babu mai fitarda ita daga wannan kangin da ta shiga.
Kuma babu abinda zata fada su yadda da ita a lokacin.
Wata irin zuciya mutari yayi tareda rufe sumayya da duka da dukkan sauran karfin daya ke jikinsa,ko kulada cikin jikinta da kuma tunanin zayyi mata illah bayyiba.
Tun tana ihu harta durkusa akan gwiwoyinta tana zan numfashi har numfashinta yayi sama ta fadi ta suma.
Duk aika aikar da mutari yakeyi su inna suna gani amma babu wanda yayi yunkurin hanashi har saida ya sumar da ita.
........uhm.......

    🏵*Sady-sakhna*🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now