Page ....37...

181 20 6
                                    

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...37....


Da dau dan lokaci kafin allah yabata ikon isa bakin department dinnasu,gani take ma kaman an karawa wajen nisa,kodan ta dade rabonta da wajenne kuma da a mota take zuwa ba kaman yanzu ba da zata taka da kafarta.
Shiga tayi da nufi office din HOD dinsu cikin dardar.
Kwankwasawa tayi daga ciki aka bata izinin shiga.
A zaune ta sameshi a kan kujera yana cike cike,bai wani sanja sosai ba kaman yanda ta sanshi a da.
Daga kai yayi ya kalleta sau daya daga nan ya cigaba da abinda yake.
Tunda ga sannan tasha jinin jikinta ganin babu fuska.
A hankali ta karisa ta zauna a kan kujerar dake gabansa,sannan ta bude baki a hankali tace,
"Sir good morning"
"Morning"
"Sir dama nazone na dawo da file din da'aka ce na cike"
Ta fada tana mika masa,karba yayi ya zefashi gefensa kafin ya dago ya kalleta
"Naji sai kuma me,kije idan na duba in inada lokaci zannemeki"
"Sir dan Allah kayi hakuri da abinda yafaru,nasan nayi kuskure na gane kirena ka taimakeni ka barni na cigaba da zama dan Allah,wlh komenene zanyi,ina ta kamama na kwanta na roki yafiyar ka ne wlh zanyi"
"Hmm dagaske kin gane kurenki kuwa,kuma wanda kika mareshin fah,idan ni na yarda shi zai yafemiki ne,ke ina ga yar babban mutum kinaji da duniya koh"
"Ahah sir Ni ba y'ar babban mutum bace yanzu,hasalima yanzu a karatunnan na saka dukkan burina saboda shikadaine gatana a yanzu bayan Allah,ka taimakeni dan Allah,shima dr Nuhu zanje na bashi a hakuri yamzu idan na fita daga office dinnan ku taimaka min dan allah,ko aji daya zaku mayar dani zan karba akan ku koreni"
Duk maganar datake cikin kuka takeyinta da kuma rawar muryah,har prof Saminu yarasa ma abinda zai ce mata,wai duniya kenan idan akace sumayyah zata zama haka zai yah dafa qur'ani ya musa,amma yamzu gashi a gabansa yana gani da idonsa.
"Kinga kiyi shiru ya isa haka,mun gama zance da barr jalal yafafamin halin da kika shiga,kasancewar har yanzu a first semester Muke saboda matsalar strike to ya nema miki wata alfarma kan cewar zaki tsallake IT din ki na wata shida amma zakiyi research sannan ki hada da project dinki ki kawo.
Abubuwan zayyi miki wiyah sosai amma idan kina ganin zaki iya ni zan miki sign.
"Wlh zan iya zan dage sosai na baka mamaki,koyafi haka ma zanyi "
"To shikenan Allah ya taimaka,naji dadin gane gaskiya dakikayi sosai,saidai banji dadi ba da'akace mahaifinki ya cire hannunsa a lamarinki,ba a yiwa mace haka ai,yanzu dai saiki dage sosai,rokon dayayi minne dakuma halin dakika shiga yasa nayi miki wannan alfarmar,ina fatan karki bani kunya,sannan idan wani abu ya faru kizo ki fadamin a nan,karki jd ga wani malamin daban"
"Nagode nagode Allah yasaka da alkhairi ubangiji Allah yakawo mai tallafawa naka ahalin ko bayan ranka malam nagode sosai"
Ba komai kibar godiyar ta isa haka,ga shi wannan information dinki ne na makaranta anyi resetting,course reg kuma kije kiyi a cafe,ta can ma ki cire topic dinki na project,ki fara yanzu dan abubuwan zai kaiki har next semester inaga"
"Nagode sosai yanzu zanje na duba kuwa"
Daga haka sumayyah ta fita daga office dinnasa sai murna takeyi zata cigaba da karatu a karo na biyu,wananm damar data samu bazata taba wasa da ita ba.
Tana cikin tunani har ta isa cafe din dazata cire course form dinta.
Duk tafiyar datake sai kallonta ake ana nunata,wanda suka santa a da suna bawa wanda basu sata ba labari.
Ita kuwa ko kuladasu ma batayi ba ta safgar gabanta takeyi.
Reg number ta bayar aka saka akan zata duba abinda zata karanta,sai a sannan kuma ta tuna akwai wani abu waishi biyan kudin makaranta,jimm tayi a tsaye tana tunanin inda zata samo kudin makarantar a lokacin.
Har mai cafe din ya Danna number tace,
"Tsaya malam dama course reg nazoyi to kuma bazayyi ba sainayi paying school fees dan haka kabarshi kawai karka shiga"
'Amma kuma gashi har na shiga cikin profile din,kuma ya nuna an biya kudin makarantar ma,saidai na one semester ne kawai"
Da sauri sumayyah tazo ta leka wajen da taga kudin makarantar 30000 ciff,mamaki ta fara akan waye ya biya mata kudin makarantar.
"Ayi registration din kokuma a barshi?"
"Ahah kayi kawai bakomai"
Komawa gefe tayi ta kira salma a wayah kafin yagama aikin.
"Aslm salma ina makarantar nazo wajen yin course reg"
"Okay kinje makarantar,to yah kin gama komai normal koh"
"Eh ina kanyi dai,naga an biyamin kudin semester nan,salma wanene nasan kinada labarin hakan"
"Hhhhh kijimin sumayyah wlh brr jalal ne ya biya,ni ban ma saniba saida yazo tukunna yake fadamin ya har kudin makarantar ma ya biyamiki"
"Dan Allah salma kiyi masa godiya sosai,banida bakin cewa ma komai ni yanzu abin yabanj mamaki sosai"
"Lah haba sumayyah karki damu,idan har yayi miki kin cancanta ai,Allah dai yabaki ikon yin karatun,inshaallah zan fadamsa kin gode sosai"
"Yawwa ki fadamsa kema nagode sosai salma Allah yabar zumunci"
Kashe wayar tayi ta koma wajen mai cafe din,har sannan bata bar mamakin karamcin bawan allahn ba.
Karbar takardar tayi ta bashi kudinsa ka fin ta tafi,tana kallon abubuwan dazatayi da kuma venue din,dan Allah yasa tasan wasu abubuwan da dama bazai bata wahala sosai ba.
Lokacin data ga wanda zai mata supervisor nah project saida gabanta ya fadi rass,
"Dr Nuhu!!"
"Wai shine zai dunga dubani,innalillah anyah kuwa zamu kare lafiyah,to Allah gani gareka dai"
Batayi kasa a gwiwaba ta nufi hanyar office dinsa,dama zata je gaisheshi ga kuma wani abin zai sake hadasu,Allah yasadai ya manta abinda tayimasa a baya ameen.
A bakin kofar tasamu wasu samari a suna jiransa,wani ta tambaya  dayake gefenta yace mata baya nan suma jiransa sukeyi,saida ance ba lallai ya dawo da wuri ba,gashi kuma tana da lecture karfe goma,lokacin kuma yayi,hakanme yasa ta tafi kar ayi babu ita,dama anyi mata ratar wata guda.
Ba ita ta gama lecture bah har yamma,lokacin tasan dr Nuhu ya tafi gida,shiyasa itama kawai ta wuce gida.
Lokacin data isa gida wajen karfe shida da rabi,dakyar take daga lafa dan gajiyah abin fah ba wasa,gashi ta manta ji take kaman tana farowa daga farko.
Babu kowa a falon shiru,amma dagajin yar magana tasa suna ciki.
Shigewa dakinta tayi ta zefar da jakar akan kujera tareda fadawa kan gado ta kwanta tana maida numfashin gajiyah.
Tashi tayi ta shiga bandaki ta tayi wanka,riga marar nauyi tasaka kafin ta wice kitchen domin duba abinda zataci,rabonta da abinci tun awarar data siya a wajen yan talle da rana.
Kular da maryam take saka mata abinci ta dauko ta bude,abincin daga gani tun na ranane,inaga bata yi abincin dare ba watakila.
Kenan Ahmad baya gari inaga,dan in baya nan dama bata abincin dare,surutun data ji ina bakuwa tayi suke zance.
Dauko kular tayi ta fito daga kitchen din zuwa nata dakin,haduwa sukayi da maryam dim ita da yayar ta Addah kareema da alama zuwa mata tayi.
"Ina wuni addah kareemah"
"Da ban wuniba zaki ganni ne,anje an yini ana yawon ta zubar yanzun an dawo gida jaka ta dafa abinci za'a dau aci,gaskiyar ki kam maryam bata yin abinci saidai a dafa kawai taci,wannan abin kunya ma har ina,ki ki mutum kawarki ta aureshi daga baya kema kizo ki aureshi,ban taba ganin irin wannan abuba wlh,butulci a fili da zalunci,maza ma saidai a barsu,mai zakayi da ita Ahmad idan kana da hankali"
"Addah Kareema wannan zagim bai kamata ki dungayi ba a matsayinki na yayah indai kinason jan girmanki,saidai kuma idan zaki ajiye mana mu take.
Kekuma maryam dakika fadawa yayarki bana girki saidai ayi na ci,nice na kiyin girki a gidannan ko kuma mijinkine yace karnayi,ah to daga yamzu saina dungayin girkin ai nidake muna ci shikuma ya dunga zuwa wajen yan tuwo tuwo yana ci,saimuga mai damuwa nidake,ki daina yin abun kirki kuma kina kaiwa korafin hakan,wannan dama halinkine kema,inni masifah ce dani"
"Ke sumayyah to karya na fada abinda nace iyee,yazaki zagi yayata nima ki zageni,nakula kwannan wani jin kanki kikeyi a cikin gidannan"
"Zagi kuma,za'a sami wanda ya zagi wani tsakanin nida itah,in gidane kuma dama ai nakine ni in kinyi hakuri ma ganin sai yayi miki wuyah,inada abinyi ba zaman gulma ba"
Daga haka sumayyah ta wuce cikin dakinta da kular abincin ta a hannu ta barsu a wajen
Tana isa dakin tace,
"Maryam kinada matsala,saikiyi abin kirki ki ruguje abinki da kanki,narasa yaushe zaki bar wannan halin,kulluma halim mai masifah ake gani a aibata,shima mai shuru shuru din ai munafukine,ace ke bakida sirri,komai naki saikin fada,kuma idan aka baki shawara kawai saiki dauka,babu tunanin mai kyauce ko a'a.
Kai ina tausayamiki wlh,Allah ya kewayeki da munafukai makiran mata,gaki bakida wayo dole zakisha wahala"
Kwanon abincin ta ajiye tafaraci kafin a kira sallah ta samu ta gama.
Saboda ba karamin aikine a gabanta ba na copyn note da kuma fara karatu,.
Tanayin sallah ta ciro littafin tafara kwafah a cikin note book dim data siyo masu hard cover guda biyu.
Tana farawa tafara karyar da wuyah tana yarfe hannu.
"Wayyo haka zamuyi da rubutunnan,ashefah akwai aiki sosai,kai gaskiya dole na siya wayah saboda tura pdf bazan iya ba"
Ta shi tayi ta dauko wata jakarta a cikin wardrobe,duba kudin cikin tayi,tafara lissafin nawa zata kashe a semester na kudin keke napep da kuma siyan dan abimci idan ta dade a ciki.
Dama kudin sadakinta ne saikuma wasu yan kudade da mutane suka bata a bikin,harda hajiyha mama ma ta Bata dubu goma.
Dubu ashirin ta wata a ciki da niyyar zata biya ko infinx ce tasiya second saboda dan browsing da kuma samu labarai na ajinsu a WhatsApp.
Har wajen goma sha biyu tana zaune tana ta rubutu,baccine yasaka tsayawa badan taso ba,har tayi shirin kwanciyah kuma sai taga kwanon abincinta bata kai kitchen ba,hakan yasa ta dauka da bude kofar ta fita.
Tun kafin ta karisa falon takejin sautin numfashin mutane,bata kawo komai a ranta ba ta karisa zata wuce.
Ido biyu tayi masoyan sai soyayyar su suke sha a falon,dauke kanta tayi ta wuce,musamman data ga ko kulada da tana wajen basuyiba sai kiss dinsu sukeyi.
Tab'e baki tayi ta wuce kitchen din ta ajiye kwanon,
"Hmm jarababbu ko falon ma sun maidashi dakinsu waya sani"
A hanyar tawo wartane tayi gyaran muryah wanda yasa maryam tashi daga kan cinyar Ahmad tana komawa gefensa ta zauna.
"Uhm dama nace zan wuce,kun gama ko baku gama ba,banason nayi mungun ganine yabatamin ido,bayan yanzu ina karatu karnaje na dunga ganin paper dusu dusu"
Har karashi rashin mituncinta basu kulata ba,itama ganin bazasu ce komai ba yasa yin Murmushin gefen baki ta bi ta gabansu tatafi dakinta.



🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now