Page ...50...

272 14 0
                                        


 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵

...50....






Tashi sumayyah tayi ta tafi abinta bayan abbah ya sallameta,a ranta tana salle walle kuma,kowa yakama gabansa,dui da yanda nake jinka a raina bazan iya kunsar bakinciki ba yanzu,da din ma wlh dama ka samu banda yanzu kuma.

Bayan sati dayah da kiran da abbah ya mata dakuma takardarta da Ahmad zai bata,bataji komai daga gareshiba,itama kuma bata nemeshi ba,a nufinta duk sanda yagama wanata ya bata takardar.

Komawa ma'aikatar hajiya aisha tayi tana rikemata wasu Abubuwa kafin ginin nata ya kammala,dan program ma taje ya kusan guda uku daga dawowarta kasar,musamman da aka san matsayinta yanxu na kwarewa a design din cikin gida company da kuma event.

Shigar kayah kuwa kala kala,gata da iyah wanka design din ya ratsata sosai,ko ina sunan golden girl yasake karadewa a karo na biyu,saidai wanann golden girl din mai takama da nata daukakarne bana ubanta ba.

Ranar taje wajen aiki suna zaune suna hira da abokanan aikinta Mufeedah tace,

"Dan Allah anty sumayyah idan bazaki damuba inaso mudan ja gefe zan miki magana"

"Okay ba matsala"

Tafiya suka dan yi har zuwa wani waje a can gefe inda aka saka kujeru,wani tagani a zaune a wajen da alama su yake jirax

 Kallon Mufeedah tayi tareda tsayawa tana bukatar karin bayani.

"Karki damu likintan Ahmad ne dr suraj kuma yayana,magana zakuyi mai muhimmanci shine ya nemi ganinki"

Karisawa wajen sumayyah tayi yayinda Mufeedah kuma tatafi abinta.

"Barkanki da aiki malama sumayyah"

"Yawwa barka ina jinka"

"Eh nima sauri nake,maganar data kawoni wajen ki akan rashin lafiyar Ahmad ne,wanda ya boyewa danginsa,sannan kuma yayi sign akan bai yadda kowa yasani ba,saidai ganin abun yanayin worse yasa na yanke shawarar fadamiki,a matsayinki na matarsa"

"Wace irin rashin lafiya kuma"

"Yana dauke da cutar heart attack sanadiyyar shiga damuwa daya dungayi a lokuta daban daban.

Na farko yayu ne tun rasaki a karon farko kika auri wani,wanda sannan ma akan magani yake,na biyun kuma yafi worse,saboda ya hada masa da rashinki dayayi na karo na biyu kin bata da kuma rashin matarsa dayayi sanadiyyar haihuwa.

Koyaushe idan nace ya fadawa yan uwansa sai yaki,duk sanda abin yatashi masa yakan zo ya karbi allura,to yanzu kam ma duk sati sai anyi masa,gashi tana da matsala sosai,kullum zancensa shine bazai iya daina tunanin abinda yayi miki ba,sanann burinsa shine sakaki a idonsa a karo na uku."

"To inda gaskene meyasa ina gidansa amma ko magana bayamin"

"Yanajin takaicin abinda wanda kika aura yayimiki,sannan kuma da tsananin kishin hakan,yana bukatar zamanki kusada shi a lokacin,amma ganinki a matsayin bashine wanda ya aureki da farko ba,wani kikeso daban bashiba shiyasa shi cituwa da zamanki kusada shi.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now