Page ....7...

182 15 0
                                    


🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Zan maida littafin kaico nah page biyu a rana,amma said naga comment din ku na littafin yafi haka gaskiya,so ina jiranku 😊😊😊😊
🏵🏵🏵
...7....

Sanyin asubane ya busa sumayyah,Wanda hakan yasa ta tashi badan ta so ba.
Jan jikinta tafara amma sai taji kaman wani abu ya danne ta.
Daga kanta tayi taga yazeed akanta hankalin sa kwance sai zuba uban bacci yake.
Kayan ta tagani a can gefe inda yazeed ya ciccilillarsu jiya da daddare.
Kallon jikinta tayi taga tsirara take haihuwar uwarta babu komai a jikinta,ga kuma yanda jikinta yayi bala'in tsami,musamman ma daga kan kunkuminta zuwa kasa.
Da kadan kadan kwakwalwarta tafara tariyo mata abinda ya faru a jiya da daddaren,tabbas dagaske ne ba mafarki take ba,dagaske ne yazeed ya karbi budurcinta a jiyan,abinda tayi ta burin tattalawa shi yazeed ya karba bada yardar taba,a cikin bacci yafatattakata tamkar ya samu bandir.
A jiyan ya nuna mata bata da matsayi bare yanci a wajensa,tunda har zai iya saduwa da ita tana a cikin bacci,kuma hakan ma farkon darenta dashi a rayuwarta.
Tureshi tayi a jikinta tareda jawo zaninta wanda tayi sa'a yana kusada ita,ko motsi shikuwa bayyi ba kaman yasha maganin bacci.
Dakyar da dauriya tafara bin bango har ta samu ta isa bandakin dake cikin dakin.
Allah ya taimake ta kuwa akwai ruwa a bandakin,botiki ta dauka ta tari ruwan da sanyi da komai tayi tsarki ta tsaftace jikinta.
Banda karkarwa babu abinda jikinta yake har ta fito daga bandakin.
Kayanta dasuke kasa ta mayar don bayansu bata da wani kayan.
Leka window tayi taga har gari yayi haske,da alama rana ta kusa fitowa.
Har ta idar da sallah tafara yan addu'o'i gari yafara haske amma yazeed bai tashi ba.
Matsawa inda yake tayi tareda dan buga cinyoyinsa akan ya tashi.
Buge hannunta yayi tareda juya ya cigaba da baccinsa,bata hakura ba tasake buga bayansa tareda cewa,
"Baby ka tashi mana gari ya waye fah anyi sallahr asuba tuntuni,sannan ga najasa a jikinka yakamata ka cire"
Buge hannunta yayi cikin magagin bacci Yana cewa,
"Mtsww Dallah ki barni sai na tashi tukunna,koda safema naga in mutum yayi sallahr tana karbuwa,musamman ma da aka ce in bacci yake bayyi ba,dan haka zaman lafiyarmu dake karki kara tashi na idan ina bacci,kinji na fadamiki"
Daga haka bako kunya ya juya yagyara kwanciyarsa ya cigaba da bacci.
Sokoko ta tsaya tana kallon sa kamar a sankareta tsabar mamaki,abubuwa dayawa ne suka fara mata yawo akai na halin yazeed tun ba'aje ko ina ba.
Nadewa dankwalinta tayi ta fita zuwa falon gidan,dan lokacin har hasken safiya ya haska ko ina.
Wurare ta dunga shiga na gidan tana kare masa kallo,ba laifi mai kyaune sosai an kawata shi matuka,ciki da falo da bandaki,kitchen a ciki sai kuma wajen shan iska a wajen gidan.
Abinda yayi cikas shine rashin kayan gidan,dan babu komai wanda mutum zayyi amfani dashi.
Lokacin da ta koma dakin wajen karfe tara ta samu yazeed a zaune Yana zuba hamma,da alama sannan ya tashi.
Bandaki ya nufah yayi wanka ya mayar da kayansa,sai shinshinasu yake yana yamutsa fuska,duk abinda yake sumayyah bata kukashiba har ya gama yasakai zai fita daga gidan.
Ganin dagaske yake fita zayyi bai kulataba kaman wanda suke fada yasata saurin shan gabansa.
Kallonta yake da alamar tambaya,sai kuma yaga ta rausayar da kai.
"Amm dama gani nayi zaka fita ko gaisawa bamuyi ba bayan a gida daya muka kwana muka tashi"
Kamota yayi tareda dora hancinsa akan nata yana kallon cikin idonta,
"To ai kedince baby,jiya fah daga fara kai miki caji kika farayimin kuka,ko irin kissar matannan bakiyiminba,sannan da asubama kika dameni,bayan jiya har karfe hudu banyi bacci ba,shiyasa kika ga nayi fushi dake"
"Uhm to kayi hakuri bazan sake ba "
"Yawwa my baby doll,yanzudai bari naje na dawo,driver zai taho da kayan furniture a zo a saka,tunda naga su baba basuyi mana ba,sannan zan taho mana da kayan sakawa da kuma na abinci"
Daga haka yayi mata kiss a goshi yasakai ya fita daga gidan.
Binsa sumayyah tayi da wani mayattaccen so,dan duk abinda yayi mata da daddare da kuma kin sallahr da yayi duk neman bacin ransu tayi ta rasa lokacin daya manna mata kiss a goshi.
Yanda yazeed ya fada kuwa haka akayi,zuwa wajen azahar masu kaya suka sauke suka shiga dasu cikin gidan,dayake harda kudin sakawa ya basu nan da nan gidan ya sanja kamanni zuwa na yan gayu.
Murna ne da farinciki ya ishi sumayyah lokacin data ga yanda suka mayar da gidan,abin ban sha'awa,batasan lokacin data fara tsalle ba tana daukar videos din kowanne bangare na gidan.
Tana cikin hakanne taji ta bigi mutum ta baya,da hanzari ta juyo suka hada ido da yazeed,dan ita kwata kwata ma bataji shigowarsa ba.
Ledodin hannunsa ta karba tareda nufar fridge dasu,dan takula na can dinne.
Kafin dare suka gyara gidan tsaf,duk wani abun amfani an saka shi a inda ya dace.
Kwanciya sumayyah tayi akan kujera tana huce gajiyar aikin dasuka sha na gyaran gidan,har bacci yafara daukanta taji muryar yazeed yana mata magana,
"Baby bacci zakiyi,kamata yayi kiyi mana abinci ai kiyi wanka sannan kuma mu tafi gado dutyn wajen yana jiranki koh"
Ji sumayyah tayi kaman ta rusa ihu na maganar da yazeed yayi,saidai tana kallon idonsa da kuma yanayin yanda yayi maganar cikin kwantar dakai kaman karamin yaro yasa ta kasa yi masa musu,duk kuwa da zuciyarta taso yin hakan.
Ta shi tayi tareda cewa "toh"tayi hanyar kitchen din kaman kwai ya fashe mata a ciki.
Jallof din taliya tayi da dankali,lokacin data fito daga kitchen din har yayi wanka yasaka kananun kaya na bacci masu kyau farare.
Tana arba dashi taji duk wata kasalarta ta sauka saboda yanda yayi mata kyau,kafeshi tayi da ido har tana kokarin yin tuntube da kafar kujera,saurin tashi yayi yariketa tareda sake kasheta da wani dan iskan murmushi,shikansa yasan yana bawa y'ar mutane a jikinta,indai ta wajen kyansa ne.
Wanka tashi tayi da sauri sauri kafin ta zubo musu abincin suka fara ci,haka suna cin abincin yana mita bayyi masa test ba har suka gama ta gyara wajen.
Iya gajiya ta gaji ranar,saidai a yanda take ji ko tafi hakan gajiya bazata iya tsallake bukatar mai gidannata ba.

Haka sumayyah takwashe sati biyu cur a gidan yazeed,har zuwa lokacin kuwa babu koda kare na gidansu daya leko inda take,tun kwanakin baya bata damuwa har abij yafara damunta yanzu,bata dauka zatayi missing dinsu kaman yanda tayi a yamzun ba.
Ga Kayan abinci mai kyau ga gida mai kyau ga kuma miji dan gayu kyakykyawa wanda take so,amma kuma kwata kwata zuciyarta ta gagara samun salama da rayuwar,maimakon tayi kiba saidai rama da takeyi wanda tarasa gane dalilin hakan.
Duk da cewa yazeed yana nuna mata so amma baya nuna mata kulawa,indai taga karyar da kansa to wani abu yake nema a wajen ta,ko kuma idan ya cutar da ita.
Ga shi Abu kadan zatayi masa ya debi fushi da ita kaman wanda ta zagi iyayensa.
Duk wannan tunanin a zaune take tana yinsa akan kujera,saida ta dawo hayyacinta ta kulada hawayen dayake zuba a kan fuskarta,saurin sharewa tayi tareda goge fuskarta.
Kallon agogon dakin tayi ya nuna mata karfe sha biyu na dare,har sannan yazeed bai dawo gida ba,ta rasa gane wani irin hali kuma ya daukarwa kansa,dan yau kwana hudu kenan yana jerawa baya dawowa gida da wuri.
Haka zatayi ta jiransa har tayi bacci bai dawoba,abu daya yake nuna mata ya dawo shine idan taji yafara nemanta a cikin bacci,wannan abu yana damunta sosai,dan har fada masa tayi akan idan har bukatarta yake yakamata ya tasheta tukunna,amma akan hakan ya debi fushi da ita wai ta hanashi hakkinsa dama karya take ba sonshi take ba.
Duk yinta daya fahimta haka ya kekasa kasa yace ta hanashi hakkimsa ne,idan bazata bashiba zaije inda zai bada kudi a bashi.
Wannan magana ba karamin batawa sumayyah rai tayi ba,dan saida tayi kuka har ta godewa Allah,jitayi dama batayi masa magana akan hakan ba.
Daga karshe dole saida tazo tana bashi hakuri akan lamarin,nan ma ya dade kafin ya hakura ya sakko daga dokin zuciyar daya hau.
Karar bude kofar falon taji hakanne ya sata tashi ta nufi bakin kofar,dan tasan shine ya dawo.
Hada ido sukayi da ita dashi har sannan yana rike da handle din kofar bai sakeba,kallonta yake da mamaki,dan bayyi tsammanin ganinta a dadai lokacin ba.
Cikin kasalalliyar murya yafara cewa,
"Mekike a tsaye har wajen karfe biyu bakiyi bacci ba?"
"Kai kuma mai kake a waje har wajen karfe biyu baka dawo gida ba?"
"Oh yanzu sumayyah ina tambayarki kina tambaya ta?"
"To mai yasa ka tambayeni bayan kasan kaine abin tambaya?"
Ganin hawaye yana zuba a idonta me yasashi sauke ajiyar zuciya,dan ya kula duk abinda zai mata a kwanakin baya bata nuna masa,kullum kokarin hadiyewa takeyi,amma yanzu yaga karaya tsantsa a cikin idanunnata.
Jawota yayi jikinsa tareda mannata a kirjinsa,sauke ajiyar zuciya tafarayi tana kokarin saita kanta.
Saida yabari ta kwantar da hankalinta kafin yadagota tana kallon idonsa,
"Look kinga baby bawai wani abu nakeyi ba fah,kawai wasu kayane ake shigowa abba dasu daga waje,to basa isowa sai dare,shiyasa muke tsayawa har se munga saukarsu kafin mu dawo gida,yanzu hakama Abdurrahim ne ya saukeni ya wuce gida,cos ni motata wacce kika ganni da ita ranar haduwar mu na sayarta ina jiran ta gabanta ta fito tukunna.
Abinda yasa kika ga na tambayeki saboda naga ga dare ga Sanyi amma kina tsaye ke kadai,kinga dole zanji haushi saboda lafiyarki koh?"
Daga kai tayi tareda sake narkewa a jikinsa,cikin shagwaba tafara magana kamar y'ar yaye,
"To amma ai da ka fadamin ko baby,shine kabarni cikin damuwa da tunanin inda kake ?"
"Sorry dolly bazan sake ba,daga nan zuwa six month inaga za'a kai ana sauke kayan,kinga muma mun hadu da aiki koh? Sannan ki shirya gobe zamuje ki gaida hajiya,dan yau satinmu biyu da aure bakije ba yakamata gobe na kaiki ki yini a can"
Daga kai sumayyah tayi badan tasoba,dan ita sam matar batayi mata ba,musamman dama ita bason mutane ne da ita ba,saidai babu yanda zatayi tunda uwar mijinta ce,dole sun riga sun hadu tunda ta auri dan ta.
Da haka suka wuce daki sai muce kuma mu kwan lafiya,allah ya tashemu da rai da lafiya.
Dasafe kuwa kaman yanda sukayi da yazeed akan zai kaita gidan hajiya saratu hakane ya wakana.
Shiryawa tayi cikin shadda mai adon duwatsu milk,yayinda ta yafa mayafi ma milk,hakama takalminta flat shoe shima milk(mai karatu in baka manta ba kunsan sumayyah da son yin match color a wajen saka kaya).
Lokacin data fito bakaramin kyau tayi ba,dan dama ba daga baya ba wajen kyau,ita dai barta a halinta.
Tun da ta doso motar da yazeed yake tsaye a jikinta ya kafeta da ido ko kiftawa bayayi,tana isowa wajen yajawota jikinsa tareda rada mata wata kalma a cikin kunnenta,wani murmushi tayi tareda boye fuskarta da tafukan hannunta.
A cikin motar shiru sukayi babu mao cewa komai,kowa da abinda yake sakawa a ransa har suka iso gidan su yazeed din.
Tun daga bakin kofar gidan kan sumayyah ya kulle,dan a yanda taga gidan nasu bai fi na yan aikin gidan ba,wai hakan ma daga wajen kenan,ana shiga gidan a lokacin ta raina kanta,dan tunani tafara anya za'a bar yazeed ya shige kuwa,sai kuma taga masu gadin sun bude musu sun wuce.
Saidai daga yanda suka gaisa da masu gadin bai yi kama da yanda zasu gaisa da dan gidan ba.
A wani dankareren falo aka saukesu sukayi tsurut a zaune kaman almajirai a gaban mai kudi.
Kalle kallen gidan sumayyah tafarayi tana kuma tuno yanda gidan su yake,dan ko sashen yan aikin gidan da suka ci karo dashi a waje yafi gidan su kyau.
Maganar da abbansu ya fada ana sauran sati biyu da aurensu ce ta dawo cikin kanta inda yake cewa.
"Hatta mutumin dayace shi dansa ne,bashine uban sa ba,mayaudarin yarone kawai,dan haka bake bashi"
"To idan ba wa'ennanne iyayen sa ba to suwaye iyayensa,mai yasa ya boye nasa iyayen?.....?"
Oho wakuma yasani,wannan daga baya kenan.

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now