Page....8.....

274 20 0
                                        


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

🏵🏵🏵
...8....

Karar sakkowar hajiya saratune ya kore shirun dayake wajen,yayinda hankalinsu gabadaya ya koma kanta.
Less ne a jikinta mai matukar tsada da kuma kyau,kallon da taga sumayyah tanayiwa less din yasaka ta kara wani shan kamshi kaman bazata taka kasaba.
Saida ta dauki lokaci a iya tafiyar kafin ta zauna akan kujerar tana kallonsu daddaya.
Yazeed ne yafara sunkuyawa ya gaisheta cikin girmama,mamaki abin yabawa sumayyah,dama yanada nuna girma har haka,batayi zaton ko a gaban iyayensa zai sunkuyar dakai haka ba,har da wani zamewa gefe kadan akan kujerar.
Bayan sun gama gaisawa da yazeed kafin itama sumayyah ta gaisheta,kaman yanda ta amsawa yazeed ciki ciki haka itama ta amsa mata.
Shiru sukayi bayan sun gaisa din,babu wanda ya sake cewa komai.
Kulada hakan da hajiya saratu tayine yasata cewa,
"Ohh kawomana amaryar kayi mu muganta ne?"
"Eh dama kawota nayi ta yini,tunda naga har anyi sati biyu batazo ba"
"Eh hakan yanada kyau,amma inaga bananne suka fi bukatar su ganta ba ai,dan nasan daga gani baka kaita can din ba,saidai nan kawai za'a nuna mata,wanda kuma can din yafi muhimmanci a gani na"
Jikin yazeed ne ya hau tsima yasha jinin jikinsa,dan daga jin maganar da tayi kaman da biyu ta fadi maganar.
Cikin rawar murya yace,
"Eh... Dama zan kaita can din idan an kwana biyu,uhm abbah yana nanne?"
"Uhmm baya nan,kasan yanada aikin yi,yaushe zai tsaya jiran zuwanku koda ya sani,gwanda ma da bai sani din ba,dan kwanannan bayason yawan hayaniya ta mutane masu bani bani,yanzu sai a tada masa hawan jini a barmu da tashin hankali"
Tana gama fadan hakan ta tashi zata tafi,har takai bakin kofar barin falon ta juyo ta kalli su sumayyah.
"Oh na manta ban fada muku ba,yau akwai inda zanje,idan har yazama dole sai ka barta to saina fadawa yan aiki su kawo mata abinci "
"Ahah zamu tafi ma babu matsala,wani lokacin saina kawota ta yinin kawai"
Murmushin gefen baki  hajiya saratu tayi kafin ta juya hankalinta kwance tayi shashenta.
Har hajiya saratu tafara maganar ta,ta tashi zata  tafi idon sumayyah yake kanta,saida ta bace mata ne kafin kallonta yakoma kan yazeed,dan gabadaya kwakwalwarta ta kulle,bata gane lissafin da sukeyin.
Saurin dauke kai yazeed yayi da suka hada ido da sumayyah,daga ganin yanayinsa kasan bayason yin karin bayanin dayaga tana bukatar ji daga gareshi.
"Baby tashi mutafi tunda kinga hajiyan aunguwa zata tafi"
"Dakata mai nene yake faruwane honey,anya kuwa.......uhm uhm to shikenan tashi mu tafi"
Bata karisa yimasa maganar datake ranta suka fita daga gidan zuwa na su gidan.
A hanya sumayyah kasa shanye maganar tayi a ranta har ta kaita ga sake tambayan yazeed.
"Amma naji tana bayanin baka kaini daya gidan ba,wane gida take nufine wai haka"
"U hmm kibari ba wani abu bane ba,kawai tana magana akan gidan kakannina ne da suka raineni,dayake ba ita ta haifeniba,Abdurrahim ne kawai danta,ko yanda muke tamkar abokai ma bata so,dan dai babu yanda zatayi ne shiyasa"
Jan ajiyar zuciya sumayyah tayi tareda cewa,
"Haba shiyasa mana take maka haka,ashe ba ita ta haifeka ba shiyasa,gaskiya masoyina kasha wahala daga gani"
"Uhm danma baki gani ba kenan"
"Am sorry ai gani yanzu koh"
"Thank for your luv my wifeyyy"
Daga haka da dadin baki wannan chakwakiyar ta tafi aka manta da ita.
Haka rayuwar gidan su sumayyah ta cigaba da garawa da mijinta cikin halin godewar Allah kawai,har zuwa yanzu wajen wata uku da aurensu yazeed bai daina kaiwa dare a waje ba,har yanzu a cewarsa aiki sukeyiwa abbansu na kayan da ake shigowa dashi.
Yauma tun safe yazeed ya shirya ya fita ganin har tara sumayyah batayi komai ba na abinci,bai damu da sanin dalili ba yasaka kai ya fice.
Yunkurawa sumayyah tayi daga kwancen da take ta hangoshi ta window yana shirin ficewa daga gidan,gashi babu damar ta kwallah masa kira,karfin dazata tashi ma bata dashi bare na kiransa har ya jiyota.
Dan jiya kwana tayi tana amai bata runtsaba ko kadan,gashi ko lekata bayyiba bare ya kaita asibiti yasaka kafa ya bar gidan.
Dan tsabar takaici da ta rasa abinda zatayi rusa ihu tayi da dushashshiyar muryarta tareda kwantawa a kan gadon tana kallon sama.
A haka ta cigaba da kwanciya akan gadon,bayan aman ya tsaya daya tabbatar ta gama amayar da duk wani abu data ci a jiyan.
Karar bude falon taji,saikuma muryar yazeed data jiyo yana bin wakar alan walker da take playing a wayarsa,hanyar dakinta ya nufo tareda bude kofar da dan karfi yana magana,
"Wai mai ya samekine haka,kina nufin bazaki yi mana abinci bane?,indan abinda nayimiki jiyane kike fushi to kin dade bakiyi ba,ki tashi yanzu ki ........."
Katsewa da maganar yayi tareda kashe wayar tasa ganin yanayin da take ciki na mawuyacin hali.
"Mai ya sameki haka,kalau kuwa"
Kallon idonsa take kawai,dan maganar ma ta gagara fita sosai,saidai kallo da ido.
Ganin hakan dayayi ne yasashi daga ta yayi bandaki da ita,gyara mata jikinta yayi tareda zumbula mata wata riga daya gani a gefen gadonta.
Kinkimarta yayi sukayi hanyar waje domin tafiya asibiti.
Hanyar emergency ya nufah da ita,inda ba bata lokaci aka saka mata karin ruwa mai dauke da saukakekken abinci.
Samun waje yayi ya xauna a bakin dakin yana jiran fitowar likitan,tunani ya tafi kan cewar yaushe hakan ta faru to,dan yasan jiya kalau ta kwanta bayan sun danyi sabani.
Karar bude kofar ne ya ankarar dashi tareda nufar likitan dan yaji halin da ake ciki.
Dakatar dashi yayi tareda cewa,"kasameni a office yanzu" cikin takaitaccen bayani.
Dakin da sumayyan yazeed ya nufah yana kare mata kallo.
A kwance take karin ruwa yana bin hannunta zuwa cikin jikinta,a iya daren jiya har ta rame ta fita hayyacinta,duk wanda ya ganta a jiya ya ganta yau yasan ba karamin wahala tasha ba a daren jiyan.
Jawo kofar dakinnata yayi tareda nufar inda office din doctor yake.
A kan kujerarsa ya sameshi yana ciki cike akan wasu takardu,samun waje shima yayi ya zauna akan kujerar da take facing likitan.
Dago da kansa yayi ya kalleshi kafin yayi gyaran murya,
"Uhm Kaine malam yazeed mijin sumayyah koh?"
"Eh nine"
"Right,to a binciken da mukayi mata mungano tana dauke da karamin ciki na wata biyu,wanda shine ma ya haddasa mata tashin zuciya har ta dunga amai,rashin kawota asibiti da wuri shiyasa ta galabaita sosai"
Duk bayanin da likitan yakeyi jinsa kawai yazeed yake,dan kwata kwata bai dauko bayanin dazai aminta dahi ba.
"Ciki"!!!! ,shine abinda yazeed yake ta maimaitawa a ransa,ciki kuma? Kai ina bazai yiyuwa ba.
Dawowa yayi daga tunanin dayake tareda fuskantar likitan da kyau,
"Uhm likita naji abinda kace,saidai maganar gaskiya zubar da cikinnan za'ayi,dan a tsarinmu a kwanannan babu wani haihuwa a ciki,yanzu abu daya zakayi shine ka taimakemu ka zubar da cikinnan kawai"
Zare ido likitan yayi tareda kara kallon yazeed din,
"Haba malam da aurenku fah ba cikin shege bane,yah Allah zai muku kyauta amma ku nemi yin fatali da ita,gaskiya ni bazan zubar da wani ciki ba gaskiya,saidai kayi hakuri ko kaje wani wajen"
"Kaga likita ka fahimta mana,baka ganin yanda cikin yake bata wahalane?,gaskiya banason rasata akan wani ciki,sannan wannan aikin ba kyauta zakamin ba biyanka zanyi fah,kayi tunani a kai"
Kaman yanda yazeed yafada kuwa tuanin yatafi dayaji abinda yazeed yace na biyansa zaiyyi.
"Eh to yaushe kakeson a zubar da cikin?"
"Yanzu mana kafin yayi kwari,kuma ma yafi sauki a gama bata cikin hayyacinta,koya kace?"
Haka kuwa suka gama shawararsu na zubar da cikin dayake jikin sumayyah batareda tasani ba tana kwance kaman matacciya.
Wasu kwayoyi yabawa yazeed din tareda zuba wani ruwan magani a cikin drip din dayake shiga jikinta,bayan ya gamane ya juyo ya kalli yazeed din.
"Inshaallah Idan Har maganin ya karbi jikinta zuwa nan da gobe cikin zai iya fita,yanzu dai idan ta tashi ka bata wannan maganin dana baka,saidai guda daya zaka bata,shi zai kara saurin fitar da cikin"
Jijjiga kai akan yaji abinda ya fada,kujerar da take gefenta ya koma ya zauna dayaga likitan ya fita.
Lekawa yasake yi dayaga bakowa yayi sauri yakara gudun drip din da'aka saka mata,duk dan saboda cikin ya fita da wuri kafin ta farka😲😲.
Ware idonta tayi akan farin cilin din dayake dakin,ta dade tana nazari kafin daga baya ta yunkura da niyyar mikewa,saikuma tajita kaman a daure,hannunta ta duba wanda sai a sannan ta kulada abinda yake hannunta.
Tana cikin dubawa ne yazeed suka shigo da likitan daya dubata,da sauri likitan yakama hannunta tareda cire mata ruwan da dama ya kare.
Sannu yazeed yafara jera mata duk lokacin datayi wani motsi,tun tana amsawa har tayi shiru ta rabu dashi.
Takardar sallama yah rubuta musu ganin jikinta zuwa lokacin yayi sauki,sannan yace musu idan da wata matsala zasu iya zuwa suyi bayani.
Godiya suka fara masa musamman ma yazeed da burinsa ya cika aka biya masa bukata.
Bayan sun fito daga asibitin ma sumayyah ta dade a mota kafin yazeed ya fito daga wajen likitan suka kama hanyar gida.
Tunda ta farka batayi magana ba,haka kawai takejinta wani iri.
Gashi cikinta sai wani suka yake kaman ana yankanta da wuka ta ciki.da hakadai ta dafe wajen tareda daurewa,dan a ganinta kaman kwanciyar datayi a asibitinne yasaka hakan.
"Hello hello Wai mai naji kana fadane Abdurrahim,shin kunnena yaji dadai kuwa,innalillahi wainna ilaihi raji'un"
     Toh fah wata sabuwa.........

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now