Page ....48...

120 8 0
                                    

 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵

...48....







Ranar sadakar bakwai na rasuwar maryam aka radawa yaron suna MUHAMMAD yaci sunnan kakansa mahaifin ubansa,ana kiransa Abeeh.

A wajen mahaifiyar maryam aka bar yaron,dan yanzu babu inda yafi masa nan din.

Saida akayi sadakar bakwai din lafin Ahmad ya koma gidansa,tun daga bakim kofar gidan memory na abubuwan da suka faru gidan suka fara dawo masa.

Da su ukune a gidan,amma yanxu sauran shikadai.

Daga wacce ta rasu ta barshi da marayan dan sa,sai wacce ta bata a cikin duniyar bai ma san inda take ba,taya za'a tsammaci kwanciyar hankali a zuciyarsa.

Dauke ruwan hawayen daya fara zuba a kan fuskarsa yayi tareda tunkarar cikin gidan.

Dakinsa yafara nufah ya tattara kayansa daya san zayyi amfani dasu,dan bashida karfin zuciyar zaman gidan a lokacin

Dakin maryam ya shiga ya kalli kayanta da komai nata,kafin azo a debesu in anjima.

Shikenan fah rayuwar,kayan da'akayin fah sun gama aiki kenan,sannan koda da tsinin allura bazasu tana amfanarta ba yanzu,aikinta na garine kawai zai bita kabarinta.

Inkayi mai kyau mai kyau zaka gani,haka akasinsa ma,duk dukiyar da mutum ya tara,da cutar da kansa da yayi domin wanda miji ko kuma fadawa halakar bata daga kan turbar daidai,haka fah zaki muti ki barshi,in baki barshi ba dole shi sai ya barki,in babu saki yar iwa akwai mutuwa,wacce take tsinke igiyar alaka.

Allah ya hanemu fadawa tarkon shaidan ameen.

Har yazo fita daga gidan saikuma ya hango hanyar dakin sumayyah,karkata kafarsa yayi ta daukeshi zuwa dakin sumayyan.

Tura kofar yayi ya shiga,yana nan yanda ta fita ta barshi lokacin da ta dauki file,sai kura dayayi alamar ba'ashiga.

Har zai fita ya hango wani littafi a kan madubinta,dauka yayi ya bude inda ta kashe yin gaisuwa cin abinci dasu da kuma wasu abubuwan.

Murmushi yayi tareda shafa rubutun yace 

"Inason wannan bangaren na halinki sumayyah,akwai ki ta fadar abinda bai mikiba,duk da shiya zefani a halinda na shiga daga farko amma bazan daina sonki da kuma halinki ba sumayyah,yanxu ke kadaice bangaren hasken dayayimin saura a rayuwata da wani,idan ban ganki ba bansan yanda zan komaba,bansan zuwa wane lokaci zan kasa daurewa ba zuciyata ta buga saboda halin datake ciki.

Ki waigeni a rayuwarki ki dawo,kodah tsanta ce zata dawo dake,ina farinciki da hakan,da ace na daina ganinki a duniyata sumayyah"

Haka Ahmad yagama sambatunsa tareda daukar littafin ya tafi dashi.

Dakinsa na gidansu ya share yasaka kayansa,suma su inna ramma basuce komai ba dan sunsan yana bukatar hakan,suma kuma zasu dunga ganin mai yake a kusada dasu.

Wasa wasa rasuwar maryam da batan sumayyah anyi kusan shekara guda.

Mutumin daya san a Ahmad a da idam ya ganshi yanzu sai ya tausaya masa,kuma yayi Mamakin yanda ya koma,ya rame ya tara gashin fuska.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now