page ..38...

170 18 2
                                    

     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...38....




Washagari da safe data je makaranta tun kafin ta shiga aji office din dr Nuhu ta tafi,dan tana bukatar su sasanta sannan kuma zayyi mata signing ta duba mata topic dinta,bata taba tunanin wannan bawan Allah zai zamo wani mutum mai amfani a garetaba,sai gashi yanzu kusan rabin kaddarar rayuwarta na hannunsa na karatu,duk yanda ya yanke kuma ya yanku.
Tana cikin tunani har ta isa ga bakim kofar office dinnasa,murda murfin kofar tayi ga sacarta kuwa a bude yake,da alama yana ciki kenan.
A hankali ta saka kanta ciki gabanta yana faduwa.
"Wanene ya shi go mana "
Lekowa tayi suka hada ido,ga mamakinta sai yayi mata murmushi,
"Wata sabon gani,golden girl ceh a makarantar tamu?"
Sunkuyar da kanta tayi takariso har bakin kujerar sa wacce baki suke zama idan sun zo office din.
"Dr ina kwana,ya aiki"
"Lafiyah Kalau"
"Dama dama uhm uhmm......dama na dama na"
"Dama me,dama kin kawo topic dinki na project,ke kadaice dama kika saura baki kawo naki ba"
Mika masa file din tayi data ga ya mikomata hannu,duddubawa yayi kafin yayi mata sign ya miko mata abinta"
Karba tayi har sannan bata fita a mamakinsa ba,
"Dr dan Allah kayi hakuri da abinda ya faru......"
"Wancan ya wuce saiki kulada gaba,a tunaninki zan fadar dake saboda abinda yafaru,never ba haka nakeba,da ma dakika ga namiki wannan maganar dan kiiji haushi ki gyara ne,gashi kuma yanzu kin gyata tun daga shigarki ma.
Kije kiyi kokari kiyi abinda ya dace,indai kinyi mai kyau zan saka miki idan kuma kika fadi nan ma zasaka miki,duk gada ganinki yanxu zakiyi abinda ake so.
Kije Allah yabada sa'a"
"Nagode sosai dr Allah yasaka da alkhairi,koda bazaka karbi hakurina ba amma hakan kara sakani yin nadamar abinda nayi maka nayi,inshaallah zan yi amfani da damar da kuka bani yanda yakamata"
Daga haka ta fita daga office din har sanann tana idonta yana kan sign din dayayi mata akan file din,kenan yabata damar yin project dinta,murmushi tayi tareda rungumeshi a kirjinta ta nufi a ji .
Wasa wasa sumayyah yanzu tayi wata guda da komawa makaranta,har ta fara sabawa da karatun.
Ga wani stress data sakawa kanta nasai ta gane duk abinda ake saboda kar tayi wasa da damarta.
Wata kawa tayi guda daya a ajinnasu mai suna Sameerah matar aurece da yaranta guda biyu,sai kuma course rep dinsu da suke shiri dashi sosai,dan wasu abubuwan ma shine yake fada mata idan bata saniba.
Iyah ranar laraba ne da litinin take da lecture guda biyar a ranar,sauran baifi daya ba ko biyu,idan babu lecture library take wucewa yin research,ba ita take fitowa ba sai karfe shida.
Kullum yanzu sai karfe shida take komawa gida,bata ma san abinda ake yi a gidan ba sai weekend,shidinma yini take wani lokacin a daki.
Abinda aka sakawa rana tofah sai yazo,bikin salma da angonta brr jalal yanzu saura sati daya,bikine na gani na fada na Y'a d'aya tilo a wajen iyayenta.
Duk yanda sumayyah taso a fara bikin da ita tun daga farkon sati abin kin yiyuwa yayi,dan yanzu babu abinda take matukar tsoro kuma take kiyayewa daya wuce ta yi missing din attendance,dan tasakawa ranta zatayi iya kokarinta wajen gujewa shiga tarkon kowanne malami.
Ranar alhamis da safe sumayyah ta shiryah zata tafi gidan su salma,dan a ranar ne za'ayi sakun lalle(kamu) washagari kuma a daura auren ta.
Irin kayanta na gida ta saka,dan a kayan aurenta ko bude akwatunan batayiba ma bare tasan abinda yake cikinsu,bawai dan bata sonsu ba sai dan yanzu saka sabon kaya ma tuna mata da yanda take a baya suke.
Da maryam suka hadu a bakin kofah tana bawa mai aikanta sako ,har ta shige taji maryam din tace,
"Sumayyah ki gaishe da amaryar kice mata ina nan zuwa ran asabar ranar yini,Ahmad yaki barina zuwa kamun"
"To shikenan zan fada mata saina dawo"
Aranta tace,ohh ashe kullene dashi kenan,yayiwa wacce yasan dajarta kam.
Tun daga bakin kofar gidan sumayyah tafarajij hayaniya na mutane,biki yana inda yake kawai.
Da mama suka hadu a tsakar gida tana bada kulolin da za'a saka abinci,wanda aka karbo daga wani waje.
"Lah sumayyah wato bamu ga idonki ba saida bikin mutuniyar taki ya zo,ki isa tana daki,tun dazu dama take leka inda zaki shigo"
Yar dariya sumayyan tayi bayan ta gaisheta kafin ta wuce dakin salamn.
A zaune take suna waya damai dinki,har sanann bai kawo ba gashi in anjima zata saka.
Zama sumayyah tayi a gefenta saida ta gama kafin tace,
"Amarya Abu yazo fah,keda mai dinkine naji kina ta masifah,kefah ni na rasa a Ina kika koyi masufah ma haka,da ba haka kike ba dai"
"To ya zanyi sumayyah ai dole nayi,kimsan tun yaushe aka bashi dinkinnna kuwa,hmmm banni dashi.
Bamu gaisa bama yakk ya karatu ya kuma mutanen gidanku"
"Karatu alhamdulillah,mutuniyar ma tace na gaisheki,taso zuwa mijinta ya hanata,amma tace zata zo miki yini ranar asabar"
"Toh Allah yakawota,ke kuma meyasa bai hanaaki ba sai ita kadai yahana"
"Hmm zancen kike so ance da gwauro ya iyali,ni dama tun farko yace babu abinda yahadashi da rayuwa ta,dan haka sha'anina nakeyi kawai,sanda Allah yasa yaga dama yafara hanani fitar shikenan,yanxu kam yace babu abinda yashafeshi da fitata"
"Lah  kikace wai zatazo min yini ran asabar? To ki fada mata iyah gobene idan aka daura aure yini ya kare,dan ba'a garinnan zan zauna ba can abuja za'a kaini,kinsan dama dan canne aiki ne yakawoshi nan,to a satin Bayan can yanemi transfer zuwa abujan ma"
"Iyee to ai bansani ba,dama ba'a garinnan zaki zauna ba,kice salma sai garin FCT,Allah dai yabada zan lafiya toh da zuri'ah dayyaba"
"Ameen sumayyah,nikuma nafison zaman garinnna dan dai babu yanda zanyine"
"Ah to yazakiyi inda yake ai nan zakije koh,aure ai babu inda baya kaika saidai hakuri".
Haka suka cigaba da hirarsu har lokacin kamu yayi mai kwalliya tafara gyara amaryah.
Tayi kyau kam sosai cikin yadi mai walwali daga ganinsa zayyi tsada,ga fuskar nan tasha kwalliya.
Anyi taron kamu an watse,wani abu waishi turare kam anyi barnarsa a wajen.
Sumayyah ba ita ta koma gida ba sai dare,dan ma amaryar ce ta maida ta a motarta,sai tsiyah take mata wai amarya da tukin mota.
Ta sauka a motar kenan shikuma Ahmad ya cinno motarsa a layin zai shiga gida,yana kallon sumayyah suna magana da wanda yake tuka motar suna dariyah,da yake ita tafito daga motar kanta ta dan saka suna magana,shikuma yana kallon su saboda fitilar motarsa data haska su.
Cije baki yayi tareda buga sitiyarin motar,wato ta raina masa hankali tana zuwa yawon banzar ta sannan ta dawo masa gida.
Wata zuciyar ce tace masa ina ruwanka tunda kace ba ruwanka da rayuwarta.
Sumayyah tana shiga gida sallahr isha kawai tayi ta kwanta,dan dama cikinta a cike yake,saidai gajiyah.
Da safe bata tashi da wuri ba tun  lokacin da ta yi sallahr asuba ta kwanta,wayar ta rarumo domin duba lokaci ana ne taga missed call kusan goma,salma tayi mata shida,yayinda course rep dinsu shima yayi mata hudu,da alama zancen assignment ne daxasu bayar ran monday
Yar karamar tsuka tayi kafin ta mike ta shiga bandaki.
Yau kam atampa ta saka English mai manyan zane green da orange,sai ta saka gyale orange a wuyanta,duk da simple ne adon amma tayi kyau sosai,purse ce a hannunta baka tasaka wayarta da kuma kudin napep.
Lokacin data fito a falo ta samu Ahmad yana gyara agogon hannunsa,da alama daga wajen aiki ya dawo zai dau wani abu,dan goma kam bai kamata a ganshi a gidaba.
Hada sukayi da sumayyah inda tadanyi karfin halin cewa.
"Ina kwana"
Bai amsa ba amma yanayin sa ya nuna ya jita,idonsa ne ya sauka a kan maryam wacce tafito tana saka dan kunnen dayake hannunta.
Sanye take da wata sabuwar shaddah ainihin yar bugu sosai,gashi ta amshi jikinta saboda chocolate color ceh.
Karisa sakawa tayi kafin ta saka gyalen milk kalar adon aikin shaddar a kanta,murmushi tayiwa Ahmad kafin tace,
"Sorry zaujee nasan kanata jirana"
"Hmm kinata batamin lokaci kam,kinsan fah daga aiki na dawo ina so na koma da wuri yau juma'a"
Dauke idonta sumayyah tayi daga kansu tana tabe baki,sai a sannan ta kula da bata lokacin datake.
Saurin fita tayi daga gidan tafara tafiyah domin neman abin hawa.
A gabanta suka zo suka wuce lokacin ta tare adaidaita zata hau.
Lokacin data isa gidan a can taga maryam suna dan hira da mutanen gidan,shigewa dakin salma tayi ta kalleta tana leka abinda ake a tsakar gida.
"Kekuma mai tsaida ke har aka daurah aure kafin kika xo?"
"To Idan nazo  kafin daura auren wani abu zamyi,tunda naxo ai shikenan"
"Ke ki kalli kishiyarki,cikin kaya masu tsada,mutane sai magana suke wai ita mijin ya kawota ke kuma kinata yawo a adaidaita sahu"
"Hmm da ma kinsan halin mutane ai,laifi gulma ta cika cikimsu tabb,shikuma ganin laifi tudu ne,ka tattara naka ka hau kana ganin matsalar wani da laifinsa"
"Hakane kam,karki ga gulma fah kafin kizo dinnan,mutane sai wani nan da nan suke da ita dan gulmar tsiyah"
"Ahh Wai ke maiya hadaki da maryam ne,kinfi kowa sanin batada matsala,barta a daukan zugo,shidinma saidai tayi ta kumbure kumburenta daga baya zance ya wuce,ni wlh ba ruwana da ita,har yanzu inaganin ta a matsayin kawata"
"Kuma nidin fah a me kike ganina"
"Kai salma yaushe kika zama hakane,karki damu ke special ce ai"

"Ina ce ita zaki zaba ki barni ai,yanzu dai ba wannan ba kinsan fah ana gama daurin aure za'a tafi saboda ba gari bane,saiku shiryah"
Aikuwa kaman yanda maryam ta fada wajen karfe biyu saiga motoci na tafiya kaiwa amaryah.
Su sumayyah suna daki ana shiryah amaryah babar su tashigo yayar baban salma.
"Ina kike amaryar ne?"
"Gani inna Fulani"
"Toh zuwa nayi na fadamiki babanki yace ba gayyar mutane ziwa kaiwa amaryah,iyah iyayenki me zasu kaiki,saura duk mai son zuwa taje daga baya,a cewarsa bai yadda a debi mata daga nan ziwa wani gari ba wai rakiyar amaryah,da acikin garine sai su je amma banda wani garin"
Tana gama fada ta fita daga dakim,sumayyah ce ta kalli salma yayinda itama ta kalleta,
"Summy kina jin abinda aka ce,wai bada kowa za'a tafi ba,mai yasa toh?"
"Kinga karki damu duk mai so daga baya ai zaije,kema kuma ai zaki zo ina,tafiyah ba mutuwa bace ai"
"Uhm Hakane kuma nima nayi tantamar zuwannaki sumayyah,saboda kinsan Ahmad bayason yawan fitar dakike dan kawai bakwa magana ne,balle kuma ace wani gari.
Sannan kuma ga makarantarki yanzu kike rainon abin,nima bazanso ki sami matsala ba duk da inaso kije gidana sumayyah"
Hawayene ta ciko a fuskar sumayyah ta share tareda jijjiga kai kana tace,
"Hakane kam abinda kika fada salma,nima ina tsoron har tafiya wani gari batareda yasani ba koda bazai magana ba ai akwai doka da kuma hakkinsa akaina,sannan kinga akwai assignment ma banyiba,kije dakinki salma Allah yabaku zaman lafiya keda mijinki,inshaallah watarana zanzon gidanki.
Koda banzo ba kema ai zaki zo,dam haka babu komai"
"Hmm nagode sumayyah,komai yafaru na matsala ki kirani ki fadamin kinji,koda Ahmad ne zanyi miki maganinsa(tafada tana dariya),allah ya gyara tsakanin ku da mijinki kema ki huta sumayyah"
Daga haka suna cikin maganganun bankwana har aka zo aka tafi da itah domin tafiyah gidan mijinta tana kuka abin tausayi.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now