Page....16....

165 18 3
                                    

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...16....

Masifar da shema'u take akan awakin inna sun cinye mata abinci ta tsaya dayi lokacin da ta dora idonta akan wacce suka shigo da sumayya tare,kayan jikinta shema'u take karewa kallo tareda hadiyar yawu mukut.
Salma kuwa bata kula shema'u ba dan dama ta gama jin labarin rashin albarkarta,iya inna ta gaisar shima sama sama kafin suka nufi dakin sumayyan.
A bakin gadon salma ta zauna tana karewa dakin kallo saboda kankantarsa,
"Tabbas maganar da kikayi min gaskiya ne summy kin sanja sosai fiye da da,dan nasan da a lokacin bayane bazakiso wani yaga nan gidan ba,saboda bakya kaunar wani yaga rauninki da kuma inda kika kasa"
Hmm kawai sumayya tace tana Murmushin yake,juyar da wani zancen tayi tareda cewa,
"Salma gashi babu ruwan dazan baki kisha a gidanann,ruwan mu idna kika ganshi zaki iya amai tun kafin kisha"
"Babu aman daxanyi summy,tunda har kema kika shashi kika rayu to babu wanda bazai iya sha ba,rayuwar duniya babu abinda ta bari ai,ke kanki mai fadawa wani ne"
Suna cikin maganar ne mutari ya bankada labulen ya shigo tareda fara masifa tun kafin ya kula da wanda take dakin.
"Yanzu isakancinki hsr yakai ki dauki kudina ki tafi yawon neman maza a wajje,saboda na tsare babu wanda zai zo gida ya sameki koh? ......to wlh......'"
Shiru yayi ganin sun hada ido da wata a dakin,sai kuma yafara inda inda kaman marar gaskiya,summayya da taga haka dama ranta ya baci tace,
"To wlh me,nabiyaka kudinka ko inba haka ba kayimin dukan kudinka,nasan abinda zakace kenan mutari saboda rashin tausayinka irinna mutanen farkone,sannan bari na gyara maka koda bazaka dauka ba,ba karuwanci naje ba asibiti naje domim a dubani aga mai yake damuna,saboda wahalar danake sha ta isheni,saidai maga Allah da annabi sun taimakeni,iya kudin mashin din tafiya nayi da kudinka,ga guntun sanjinka nan dari biyu da hamsin,sauran cikatom idan allah yabani ban mutu ba zan biya ka,idan kuma na mutu bansamu dama ba ka je iyayena su biyaka"
Ihu ta rusa bayan ta cilla masa canjin kudin jikinta,tashi salma tayi ta riketa tareda gallawa mutari harara,yana ganin haka ya fita da sauri daga dakin yabar gidan.
Saida salma ta lallashi sumayya ta tabbatar tayi shiru kafin tafara magana,
"Kiyi hakuri kinji komai na duniya mai karewa ne,sanann komai tsanani yana tareda sauki,kici gaba da addu'a wata rana sai labarin inshaallah,tabbas kina ganin rayuwa kam sumayya amma kici gaba da addu'a wata rana sai labari kaman ba'ayi ba,ga wannan number ta ce idan wani abu ya faru ki kirani ki fadamin,wannan kuma kudine ki biyashi wanda yace kin dauka sauran kuma ki dunga siyan abin karin lafiya kina ci,inshaallah kafin ya kare zan dawo kinji"
Kamkame jikin salma sumayya tayi da taji abinda ta fada mata,tabbas mutum ko ya yake rahama ce karka rainashi,dan tunda take bata taba tunanin zata nemi taimako a wajen gwamna bama bare kuma salma.
Godiya tafara yi mata amma tayi saurin dakatar da ita.
Da haka sukayi sallama salma ta fita taja motarta ta bar kofar Gidan.
Bayan sumayya taga wicewar salma sai ta dawo gida,iya kwana daya kadai har ta ji karfin jikinta babu wannan jirin da hakin da takeyi kaman na da,lallai jinya babbar jarabawa ce,ba mai gane hakan sai wanda yake yinta kuma ya warke.
A hanyar ta ta komawa daki tanajin shema'u tana habaici inna na amsa mata,
"To wani sabon salon kuma gemu a kafada,innna kina gani koh,anje wajen wani an kwana,saboda kar a zargeta ya hadota da wata ta rakota,hmmmm lallai kam"
In dutsi ya kulasu to sumayya ta kulasu,dan ko kallonsu batayiba,a duniya in akwai abinda take jin haushi bai wuce mutanen gidannan ba,duk da wani lokacin tafi jin haushin kanta a kansu.
Kudin da salma ta ajiye mata ta dauka tana dubawa,dubu gomane ciff yan dari biyar biyar,wani hawayen farin cikine ya zubo mata,dan rabonta da kudi irin haka nata na kanta har ta manta ma,Dari biyar ta dauka ta bude wajen ajiyar kudin mutari ta saka masa,itakuwa sauran nata kudin da saka a cikim kayanta inda babu mai cewa akwai kudi a wajen.
Da daddare bakin dakin dauda taje da tsaya tana jiran shigowarsa,dan duk gidan da shi kadaine take magamar arziki,zayyyi shaye shayensa ya kwale,wani lokacin yayi ta maganar hauka,amma duk da haka baya mata walakanci ko kadan wani lokacin idan yaga abinda suke mata yayi yawa tashi yake ya shiga mata koda kuwa mutari ne,dan kirar karfine dashi shiyasa mutarin baya tankawa.
Duk cikinsu yafi daraja dan adam,bayason yaga ana cin mutuncin wani musamman ma mace(halin yan shaye shaye kenan).
Jiyama daya ga tana amai ya zo fita sai gashi da bobo irinna yara n nan guda biyu ya kawomata,abinne yabata dariya amma ta danne tayi godiya,a ranta tace kwayar ta motsa.
Tana tsayen kuwa saigashi ya shigo zai wuce,saurin tsayar dashi tayi tareda mika masa kudin hannunta,
"Amm dauda dama dan taimako zaka min ka soyomin indomie a waje dan allah"
"Ahh to ai bakomai ai bari naje nagani"
Har yafara tafiya tace,
"Kudin na guda biyune idan kasiyomin kaima ka siyo ma kanka,na dan samu kudine"
"Ai naga alama,yanzu haka mai motar nan ce ta dazu tayi wani alherin gashi muma zamu lasa,toh godiya nake sosai,dama kuwa banida ko asi,ashe da rabon yau zanci soyen teburin Ilah"
Ita dai sumayya dariya maganar yanda dabar tasa take bata sosai,juyawa tayi ta koma daki kafin ya dawo.
A kusan tare suka shigo shida mutari,yana rike da ledodinsa na indomie sai kamshi sukeyi.
Karisowa tayi ta karbi daya daga hannunsa tareda yi masa godiya,
"Ah haba ai nine da godiya matar mutari,irin wannan kyauta da kikayimin na maiko,Allah dai yasa albarka"
Kwallah ido yayi yana kallon mutari tareda kara jijjiga ledar tasa yayi hnayar dakinsa yana murmushi.
Itama shigewa tayi ta bar mutari yatsaye wanda yayi sakam ya zuba musu ido tareda son gano mai yake aukuwa.
Dakin ya biyota lokacin ta baje indomien a tsakiyar dakin tana ci,sai kamshin kwai takeyi.
Zama mutari yayi a bakin gadon yana hadiyar yawu,ga kamshi ya rufeshi amma babu yanda zayyi dole ya maida yawun.
Saida sumayya ta jera kusan sati koyaushe sai ta danci wani abun,har ta fara murmurewa kaman ba ita ba,duk abinda ake mutari kuwa bai ce kala ba,har saida wata rana ya faketa ya jare dubu uku a cikin kudinnata,ranar har kuka saida sumayya tayi na bakin cikin halin mutari,amma haka yayi mursisi kaman ba shiba.
Bayan kaman sati biyu ta zuwa ta asibitine ciwo yasake dawowa har yafi na da,gashi kudin mutari ya debesu bare ta koma asibitin,magani ma bata gansu ba,wanene ya dauka oho.
Ciwo yafara cinta tun tana jurewa har yazamo abin ya gagara,haka zata fara burburwa tana ihu amma babu wanda zai kulata har sai tayi ya isheta ya lafa mata kafin ta tashi.
Ga wani abu da take zubarwa wanda ta rasa menene,cire komai tayi a ranta ta nufi dakin inna da la'asar tana zaune a tsakar daki.
Shiga tayi da sallama tareda tsugunnawa,
Tun kafin tagamawa inna bayanin abinda yake faruwa da ita ta dakatar da ita tareda nuna mata hanyar fita,
"Yanzun abin yana zubamiki shine kika shigo dakina zaki batamin saboda kina min shara ko kuwa wanki,maza bacemin dagani,wanda yayi miki cikin a can waje kike zuwa wajensa da shi bai zoba yazo ya fadamiki mai yake damunki amma bani ba"
Haka sumayyah ta dauko kafa ta dawo dakinnta cikim sanyayyar gwiwa.
Leda ta shimfita a tsakar dakin ta zauna akai,saboda duk ta bata dakin da wani irin ruwa mai karni wanda yake fita tareda jini.
Mutari ne yashigo dakin,saidai tun daga bakin kofar ya toshe hancin sa tareda niyyar komawa,sumayyah ce tayi saurin rike rigarsa a cikim halin ciwon da take tace,
"Kaji tausayina mutari,koda ba a matsayin matarka ba a matsayin yar uwarka musulma ka taimakeni,kai ka sani cikin jikina nakane ba na kowa ba,kabar wannan wasanna ka ka taimakeni domim Allah,na rokeka"
Fisge rigarsa yayi yana cewa,
"Wai to me kike so nayi miki,cikin zan mayar jikina ko me,idan haihuwa ce ai da haka zakiyi tayi har sai kin haihu tukunna,kowama da haka yakeyi saike raguwa zaki damu mutane,idan asibiti kike som zuwa ni banida kudi"
Daga haka yayi gaba abinsa tana kallonsa ko kuyowa bayyi ba.
Cigaba tayi da matagugun ciwonta tana jiran tsammanin lokacin mutuwarta,takardar data rubuta number salma a jiki ta gani a karkashin gado.
Allah ya taimaketa kuwa dije tana tsaye a bakin kofar dakin tana kallonta,alama tayu mata da hannun tazo.
Nuna mata takardar tayu akan ta dauko,warewa tayi ta tabbatar numbar ce kafin tace,
"Ddddauda yana dakinsa ki kaimasa kice yakira yace maza tazo ina nemanta kinji"
Amsawa tayi da to tareda nufar dakin daudan,duk da har sanann din bata tsammanin zata samu daukin da take fata.
Can kamar wajen awa biyu har ta cire tsammanin ganin wani ya nifota sai kuma taji muryar salma a kanta,dagowa tayi tana kallon ta dishi dishi,dan hatta ganinta ma zuwa lokacin yafara bacewa.
Dauda ne ya taimaka mata suka kinkimeta zuwa cikin motarta,bayan sun dagata ne suka kula da kafar jinjiri data fito daga jikinta,fatar yaron tayi kore shar,abinne yakara tsoratasu da sauri suka nufi asibitin.
Tun daga bakin maternity aka turo wheel bed aka Shiga da ita,zuwa lokacin harta suma.
A tsaye suke sunyi cirko cirko da salma da dauda suna jiran su ji mai zai faru,wata nurse ce ta fito da wata paper a hannunta tareda mikawa dauda,dan a zatonta mijinta ne,
"Malam zaka yi sign anan dan da alama dole sai anyi mata tiyata tukunna,kallon salma yayi domin yaga mai zata ce,daga masa kai tayi akan yayi sign din.
Saidai tun kafin ya karbi biron wata ta fito tareda shaida musu ta haihu amma kuma gaskiya ta samu matsala,shikuma dan bai zo da rai ba.
Basu ji dadin mutuwar dan ba amma kuma hankalin su yadan kwanta tunda ita din da ranta,likitan ne ya kirasu office tareda yimusu cikakken bayani kam cewa,baza'ayi mata dinki ba saboda bata karu ba,amma kuma mahifarta tayi rauni sosai,saboda kwayar da ta sha na zubar da ciki a baya ba bida ka'ida ba,sannan kuma ba'a kawota asibiti da wuri na harta jigata,shikansa mutuwar dan a cikinta saida yabada tasirin matsalar da mahifarta ta samu.
Salma ce tayi ajiyar zuciya tareda cewa,
"Likitan mungode,amma yanzu zamu iya ganinta"
"Sure why not,ta far fa do ai"
Dakin da aka kwantarta sukaje,a kwance suka sameta tana kallon cilin,hawayen dake idonta yana gangarowa ta gefe,dukkansu tausayinta sukaji ganin yanda take iya kokarimta wajen ganin ta daure.
Waigowa tayi ta kallesu,tun kafin su ce wani abu tayi saurin cewa,
"Nasan d'an ya mutu,shikuma likita wace matsalar yace inada ita,dan nasan dole akwai"
Ganin tasan mai yake faruwa ne yasa su kawai fada mata gaskiyar zancen.
Numfashi taja tareda cewa,
"Mutari ka cuceni duniya da lahira,kayimin tabon da bazai taba gogewa ba,saidai dukkan abinda yafaru mafi kason yawa na laifin nawa ne KAICO NAH ni sumayyah"

🏵_*sadi-sakhna*_🏵

Share fisabilillah domin wasu ma su karanta.

Ina godiya🙏🏼🙏🏼

KAICO NAHWhere stories live. Discover now