page.... 29.....

170 16 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...29....


Tafiya suke zuwa wajen da yayi parking din motarsa,ita dai binsa take batareda tace komai ba bare kumashi.
Motar ya Shiga ya bawa wuta tukunna kafin ya tsaya yayi shiru,shi bai tafi ba shi bai cewa sumayyah ta shigo ba .
Ganin hakanne yasata kama murfin motar a hankali ta bude ta shiga.
Tafiya suka farayi akan hanya zuwa gidan su sumayyan,ko kallon inda take bayyi ba har suka dan bawa asibitin tazara kadan,har suna shirin kawai unguwar su sumayyan.
Kallon window take yi tunda aka fara tafiyar bata kalleshi,dan ita kanta a takure take da zaman motar tasa,jin datayi motar tatsaya ne yasata juyawa ta kalleshi,har sannan kan hanya yake kallo amma kuma fuskarsa a daure kaman bakin hadari a tsakiyar damina,kumatun sa har rawa yake kaman an taba kububuwa a cakin raminta.
Duk da hakan yabata tsoro amma bata ce komai ba sannan bata dauke idonta daga kallonsa ba,juyiwa yayi yana kallon cikin idonta dana sa idin wanda sukayi jawur kaman gauta.
"Mekika daukeni sumayyah,kin maidani abin wasan ki daxaki bawa wahala sanda kike so,menene dalilinki na son aurena,wane irin mungun nufi kika boye a zuciyarki kike son ki cutar damu ta hanyar shiga cikin rayuwarmu nida matata.
Cutar da kika mana a baya bai ishaeki ba saikin sake yimana wata cutar,yanzu kuma so kike ki kashemu koh,dan in ba kashemu zakiyiba me kuma yarage a duniyar nan bakiyimin ba na hukuncin ki sumayyah.
Idan kina tunanin wai har yanzu ina sonki zan zauna dake cikin so kaman da to ki sanja tuanin tun wuri,dan ina baki sani ba to ki sani yanzu,zaman cikin gidana dakike kokarin yi a yanxu tamkar kin yanki ticket din ukubarki ne na wahala a cikin gidana,ina gargadinki ne da karki kwafasa kizo kiyi danasani,amma idan kinga zaki iyah fine Allah yabaki sa'a.
In kunne yaji jiki ya tsira"
Duk maganar dayake idon sumayyah ya gagara barin kan fuskar Ahmad,duk wani yanayi da yake kan fuskarsa tarewa yake a cikin kanta,sannan kuma duk wani sauti da amon muryarsa yake fitarwa,buga wani abu yake tamkar ganga a cikin dodon kunnenta.
Wani irin bugawa zuciyarta takeyi kaman zata fito daga kirjinta,ikon allah ne kawai ya dakatar da ita daga fitowa.
Kawar da duk abinda yafada take kokarin yi a cikin zuciyar ta tareda bude baki zatayi masa dalilin aurensa,
"Yah Ahmad bad an.........."
"Yi shuru karkicemin komai,na manta ban fada mikiba,acikin abinda banaso kuma na tsana harda muryarki,dan tun ranar data gasa min maganganun da suka zamemin tamkar tabo a kirjina na tsani jin muryarki koda a mafarki ne bare na jita a kunnena a zahiri,na tsani komai naki sumayyah.
Ki fita min a motata yanzunnan,bazan iya cigaba da tuki kina gefena ba,dan ji nake kamar ina tafiya a tsakanin dutsen wuta,sannna ba sanyi nake ji ba saima tururun dayake kara hauhawa,dan haka fitamin a motata.
Motar dakika raina kike ga kin fi karfinta ma bansan mai yasa kika shigeta ba yanzu,dan haka fitamin a motata tunda badake muka siya ba,kuma ba bazawarinki ne yasiyamin ba ko kuma wannan kazamin tsohon mijinnaki"
Ganin Ahmad magana yake ta yaba mata babu tsayawa yasa ta saurin bude motar ta fita da sauri,dan takai makurar inda bazata iya jureba sam.
Tana fita daga motar tasa ta dafe dukkan kunnuwanta da hannayenta,babu abinda takeji sai bugun zuciyarta a cikin dodon kunnenta,ko karar jan motarsa yabar wajen ma batasani ba.
Tafiya take tana rike da kunnuwanta wanda takejin kaman ana kara a ciki,ga idanunta wanda suke zubar da hawaye batareda yardarta ba,kai tsaye kukan da takeyi daga zuciyarta yake fitowa zuwa cikin idanuwanta,wanda suke ta zubar hawaye batareda yardar ta ba.
Ba ita takai gida ba sai bayan isha likis,dan har dare yafara, kasancewar da kyar kafafuwanta suka temaka mata suna mika ta gaba a duk lokacin da ta taka su.
Hanyar dakinsu ta wuce kai tsaye,ko gaisuwar baba mai gadin ma bata amsaba kaman yanda takeyi a kullum yanzu,sa'arta daya kuwa babu kowa a falon har Allah yabata sa'ar shigewa dakinnasu.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now