Page .....5....

188 14 0
                                    

     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER.

🏵🏵🏵
...5....

A zaune sumayyah take ta idar da sallahr isha taga hajiya mama ta shigo dakinta,abinne yabata mamaki,dan ba kasai ba take kallon hajiyah mama a dakinta,sai abun yakai serious sosai.
Zama tayi a bakin gadonta tareda fara magana cikin nutsuwa,
"Sumayyah magana zanyi miki ki nutsu kijini,abbanku ne yake kiranki yana falonsa yanzu yagama cin abinci,magana zai miki gameda wa'adin dayayi miki,ki nutsu karkiyi wannan yarintar taki sumayyah,kiyiwa kanki gamdakatar a wannan zaman duniyar,ki maida hankalinki kinji?"
Daga kai tayi cikin sanyin jiki dukkuwa da yanda zuciyarta take bugawa,
Hanyar ta nufah domin zuwa falon abbannasu,babu abinda ya fado mata arai sai yazeed.
A zaune ta sameshi ya cin dabino bayan yagama cin abinci,sallama tayi tareda samun waje ta tsugunna a kan carpet din dakin,
"Abba gani"
Tafada cikin karayar murya,gyaran murya yayi tareda cewa,
"Babu bata lokaci sumayyah,nakiraki ne akan maganar damukayi watan baya na fitar da miji dana baki zabi kiyi,shin kin fitar da miji ko kina son zabina ne?"
Dummm gabanta yafara bugawa ,dakyar ta fara magana bakinta yana rawa,
"Eh....abbb....ah dama akwai wanda mukkke soyayya dashi,sssunansa yazzeeed ne"
"Waye shi?a wace unguwa yake,sannan waye ubansa sannan menene sa'anar ubannasa,tsawon wane lokaci kuke tareda shi?"
Duk wannan tambayoyin sune suka cika kwanyar sumayyah har ta rasa mai zatace,dan bata da amsar ko guda daya a ciki.
"Eh dama watanmu daya dashi,sannan na fada masa yazo,to wai yanada uzirine shiyasa bai zoba,a garinnan dai yake,amma bansan sunan babansa ba nima"
"To shikenan,kice yazo gobe ya sameni,idan kuwa naga wani abu bai min ba a tareda shi,to aurenki da Ahmad babu shi,kisaka wannan a ranki, tashi ki bani waje,ki turomin mahaifiyarku idan kin fita"
Tashi tayi da sauri ta fita kaman dama wanda take kan kaya.
Bayan ta fadawa hajiya mama sakon abban da sauri ta danna wa number yazeed kira.
Saida tayi uku a na hudu ya daga,"baby"shine abinda yace babu ko sallama.
Itama sumayyah bata damu da hakanba sai ma koro masa bayanin abinda yafaru yanzu take,
"Baby bana son na rasaka ,kasan irin son danake maka,wlh am serious yakamata muyi wani abu,dan idan ba hakaba bazamu mallaki junanmu ba,abbah so yake yahadani aure da waccen mayen(Ahmad) nikuma kai nake so"
"Kinga my girl daina daga hankalinki kinji,mai abbanaku yace?"
"U hmm yace Wai yana son haduwa dakai gobe,sannan ya tambayeni abbanka nace ban saniba,sannan yace idan har yaga wani abu bayyi masa ba wai Ahmad zai auramin,please baby kayi iya kokarinka kaji baby,nasan ma babu abinda zai faru,in ma takama karyane kayi kaji,nidai burina na sameka a matsayin miji,dan shine babban burina baby"
Ajiyar zuciya ya sauke ta daya bangaren tareda cewa,
"Look baby karki damu,indai zuwane gobe inshaallah zanzo,hakan bazai gagaraba,nima kinsan bazanso narasa kiba ai,musamman danasan cewa ni kike so ba waccan mai kama da birin ba,babu komai ina nan zuwa goben,ki kwantar da hankalinki kinji,banason bacin ranki"
Da haka yayi ta lallamin sumayyah har ta saki ranta,farincikin fal ranta jin abinda yazeed yace,wanda hakan yakara rura wutar kaunar yazeed din a cikin zuciyarta.
Da safe da murna taje ta fadawa hajiya mama cewar zatayi bako zaizo wajen abba,ita dai mamaki hajiya mama abin yabata,ganin yanda take ta zirga zirga a gidan kaman wanda xata taryi gwamna,har maryam tayi kira akan tazo ta tayata shiryawa.
Itama a nata bangaren mamakin sumayyan takeyi,burinta taga wanne namijin mai sa'a ne haka ya mallaki zuciyar hamshakiyar kawarta ta.
Da azahar kuwa wajen karfe biyu mota ta cinno kanta cikin gidannsu,sumayyah tana daki tana wanka taji su farouq suna cewa bakonta ya iso.
Da sauri ta fito daga bandakin tafara shiri kaman mai zuwa babban taro.
Kayan kwamulashen da tayi tabawa maryam takai musu,dan Muhibba kam ba nemi taimakon ta bama.
Tana cikin saka gyale tagama kwalliya maryam ta shigo tana tabe baki.
Kallon ta sumayyah tayi tareda cewa
"Menene naga kin yamutsa fuska"
"Yanzu dama akan wannan melallan mai bleaching kika ki Yah Ahmad?"
Ran sumayyah ne yabaci tareda nuna maryam da hannu tana masifa,
"Ke dakata maryam,wlh akan yazeed zan iya batawa da kowa,ciki kuwa har dangina,dan haka ki kama bakinki karki kara zaginsa a gabana,kinaji koh?..."
Sakin baki maryam tayi tana cewa,
"Ohh Allah,golden girl anya kuwa wannan mutumin na asiri yayi mikiba kuwa...?"
"Waya sani to,ko asiri yayimin ni mai sake bashi wani aisirinne yayimin,dan yadda nake jin sa a raina ni kadai nasani"
Daga haka ta wuce maryam tayi hanyar inda aka sauki muradin rannata.
Da murmushi ta karisa falon idonta akan yazeed dayasha yadi mai kalar chocolate,bakaramar amsarsa yadin yayi ba.
Idon kyam akansa har ta isa inda yake ta zauna,kwata kwata komai duhu yayi mata,shikadai take gani kawai.
Gyaran muryar da akayi ne yasata saurin juyawa ta kalli wani a gefenta,da kunya ta sunkuya tana cewa,
"Ahh sorry banganka ba,nayi zaton shi kadai ne"
"Ah babu komai masoya,sunana Abdurrahim,ni abokinsa ne"
"Ah Sannu da zuwa to"
Rakiya tayi musu zuwa falon abba kafin ta shige cikin gida zuciyarta tana bugawa bayan sun shiga falon abban,dan bata san mai zai faruba.
Kasa zaune tayi kasa tsaye bayan sun gama tattaunawa da abba ta rakasu zuwa wajen motarsu,abinda yakara tsurarta ma ganin yadda fuskar yazeed ta sanja kadan.
Maryam sai binta take da magana amma taki fur bata time dinta,burinta taji mai abba zaice,gashi har yanzu bai ce da ita komai ba har dare yayi.
Sallama maryam tayi mata ta tafi gida bayan tayiwa hajiya mama sallama.
Har washagari shiru babu abinda abba yace,bandaki kuwa sumayyah taje yafi sau bakwai saboda gudawa.
Bayan angama break fast ne ana zaune,kasancewar ranar weekend ne dukkan sauran yayunta suna zaune,abbane ya kalleta tareda cewa,
"Ke sumayyah,nayi bincike akan yaron da kika turomin jiya,saidai babu abinda nasamu a tattare dashi sai karya da rainin hankali,hatta sunan iyayen dayace nasane duk karyane,dan haka bayyimin kama da wanda zan bawa ya ta ba harna hada alaka dashi.
Maganata na aurenki da ahmad tana nan babu fashi,daga yau banason nasake jin maganar waccen yaron a bakinki......"
Cikin muryar kuka sumayyah tace,
"Abba amma.........."
"Banason jin shiriritarki sumayyah,na yanke hukunci nan da sati biyu zanyi aurenki tunda shi Ahmad ya shirya,yau yan gidansu zasu kawo kaya inshaallah......."
Tun kafin tagama jin abinda abba zaice tayi saurin barin wajen da sauri na fashewa da kuka.
Tunda akayi wannan magana sumayya ta fita hankalinta,kullum cikin kuka take da kuma aikata abinda tasan ba'aso.
Gashi hidimar biki babu wanda aka fasa daga ciki.
Kaman yanda abba yafada kuwa an kawo kaya Mashaallah dadai gwargwado masu kyau,yan uwa da abokan arziki sai hidima ake na shirin biki.
Haka ma Gidan su Ahmad sai shiri sukeyi,kowa ya kalli Ahmad yasan yana farinciki na auren muradin ransa da zayyi.
Yau takama Alhamis,wanda gobe ake niyyar daura auren sumayyah,ba laifi tayi kyau sosai duk da fuskarta babu fara'a.
A zaune take tana kallon hoton yazeed a wayarta,hawaye yana zirowa a idonta.
Wai yanzu shikenan gobe zai haramta a gareta,zata zama matar mutumin da ta tsana.....?kai ina hakan baxai yiyu ba.
Share hawayenta tayi lokacin da maryam ta shigo dakin,tashi tayi cikin karfin hali tareda cewa,
"Maryam zoki rakani waje,zanyi magana da Ahmad"
Da murna ta dauki gyalenta tabi bayanta,dan a ganinta sumayyah ta sauko daga tsanar da take masa.
A tsakar gidan yake tsaye ya jingina da motarsa,idonsa kyam akan sumayyah har suka iso wajen.
"Amarya bakya laifi koda........."
"Dakata ba wasa nazoyi dakai ba Ahmad,zuwa nayi nafada maka abinda yake raina,sannan nayi maka jinjina na winning din dakayi,kayi kokari kam daka dage sai ka sameni,saidai inaso kasani gangar jikina zaka aura,zuciyata nadade da damkawa wani ita.
Kuma sannan kaida farinciki har abada indai nashiga rayuwarka,natsaneka Ahmad bana sonka,amma saboda rashin zuciyarka kuma ka rako mata duniya shine ka nace sai ka aureni,inka cika kai dan inna ne kuma kasha nononta to ka fasa aurena Ahmad......."
Wani irin bugawa zuciyarsa tayi,tareda jin wani ciwo ya jiyaci zuciyarsa,saurin rike wajen yayi yana kokarin zubewa a wajen.
Maryam ce ta kalle ta cikin takaici zata yi magana,amma itama ta katseta tareda cewa,
"Ke maryam karki cemin komai,nagaji dajin maganarku haka,idan kin cika mai nuna kulawa  kuma yar halakke ki aureshi mana,shine zansan kin daku dashi mtsww"
Juyawa tayi takoma cikin gidan zuciyarta a bushe,duk abinda take akan kunnen abba tayi da yah naseer da kuma yayan baban su Baffah Usman.
Rawa jikin yah naseer yafara inda yayi saurin bin bayanta zuwa cikin gidan da niyyar karyata.
Da kyar su baba suka rike Ahmad har numfashinsa yadawo jikinsa,sallama yayi musu cikin sanyin jiki ya tafi gida,ikon allah ne kawai ya kaishi lafiya.
Dukkan su a tsaye suke mutanen gidan sun saka sumayyah a tsakiya,wacce zuciyarta ta bushe ko hawaye batayi duk kuwa da masifar da yah naseer yake mata.
"Duk abinda zakiyi kiyi aurenki gobe kuwa babu fashi,shashasha kawai"
"Aikuwa zan kasheshi idan kuka auran min shi,dan wlh bazan yi zaman da kuke buri dashi ba,saboda na tsaneshi,banasonshiiiiii"
Kowa zare ido yayi jin furucin sumayyah,har yah Naseer ya daga hannu zai mareta Baffah Usman ya rike shi tareda cemata,
"To munji bakya sonshi kin tsaneshi,to wa kike so?"
"Yazeed nake so shi zuciyata take muradi,idan har ba shiba to kuwa bada wanda zanyi zaman aure a rayuwata"
Kallon abban baffa Usman yayi tareda cewa,
"Kaji abinda tace da kunneka ko,to ka bata wanda take so tun kafin abin yabaci fiyeda haka"
Rutse ido Abba yayi tareda budesu jawur akan sumayyah,cikin cije baki yake magana mai dauke da bacin rai.
"Sumayyah zan baki muradin ranki kaman yanda kika bukata,inshaallah a gobe zan daura miki aure da wanda kike son,saidai daga goben inaso kisani na fitardake daga cikin y'ay'a na dana haifa,a wajena ke tamkar matacciyace abin mantawa,sannan idan wani daga cikin y'ay'a ya nuna ko a hanya yasanki idan ya ganki to ban yafe masa ba duniya da lahira,ban yadda kinemi taimako a dangina wani ya mikiba ko kuma ke kiyimusu wani abu.
Daga yau nacireki a cikin alhalina kije can duniya ta zama uwarki da ubanki,sannan mijin da ke kika dauka amatsayin abokin rayuwa to wlh zakiga yanda zaki kare dashi.
Shikuma Ahmad allah bazai tagayyarashi ba,sannan a gobe babu fashi zan daura masa aure koda kuwa badake ba.
Hakika bazan manta wannan rana ba da kika tozartani kika mayar dani karamin mutum a idon duniya.....wannan shine gargadina dake na karshe....."kije zaki gani".
😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥
Yanzu fah wasan littafin zai fara,wlh chakwakiya yanzu zata fara.
🏵.shin wane irin zama sumayyah zatayi a gidan yazeed? ........
🏵.wace irin chakwakiya zata taryar a gidanna nasa,sannan waye shi tunda ance boye asalinsa yayi......?
🏵.Wacece Wacce abbah zai daurawa Ahmad aure da ita....?
🏵.shin sumayyah zata tagayyara kaman yanda abbah ya fada,sannan shin yan uwanta zasu taimakata ko kuma zasu bi umarnin abban akan hukuncin daya zartar a kanta.........?
    Duk wannan amsoshin har ma da abinda baku ji ba zasuzo a cikin littafin mai suna KAICO NAH(ni tauraruwar zamani),babu zuzutawa babu yabo,amma littafin sosai nake jinsa a raina saboda nikadai nasan yanda na tsara dramar littafin.

🏵🏵*sadi-sakhna*🏵🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now