Page ..,..4......

215 14 0
                                    

  🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

          
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER &UNKNOWN OLD WRITER

Godiya ta musamman a wannan shafin gareki *ummu najwa*,nagode ta bada hadin kanki dari bisa dari Allah ya bar zumunci.
Sauran masoyan wannan littafin kuma ina godiya sosai da sosai.

🏵🏵🏵
...4....

Tunda sumayyah ta shiga daki bata sake fitowa ba bayan jin maganar da abban su yayi mata,abincinta ma sai mai aiki ce takai mata,da safene har sun dauka zasu kai hajiya mama ta dakatar dasu tareda cewa,
"Kubarta idan taji yunwa ai zata sakko,kuma ai yau weekend ne tare ake cin abinci kowa da kowa,har yayunta ma anan suke cin abinci,dan haka idan taji shiru ai zata sakko tunda tasani"
Daga haka aka cigaba da shirye shiryen abincin gidan,kasancewar al'adarsu ce duk yayan gida maza ran weekend anan suke cin abincin rana dana safe.
Bayan angama da daddaya suke shigowa har aka fara cika wajen ana hira,kamar sumayyah bazata sakko ba can wajen wani lokaci sai gata ta sakko fuskarta kaman anyu mata mutuwa.
Kujerar da take gefen Muhibba taja ta zauna tana zabga mata harara,ciki ciki ta gaishe da mutanen wajen kafin ta ja nata abincin.
Yah mu'azzam ne yayi gyaran murya tareda cewa,
"Ke sumayyah dama na manta ban fadamikiba,Ahmad yacemin zaizo idan najima zuwa wajen yamma wajenki,dan haka saiki shirya,jiya da daddare yake fadamin"
Zabura tayi kaman an mintsine ta tace,
"Ahmad kuma mai zaizo yayimin Toh"
"Me ake idan anzo wajen mace zance,ko so kike nayi miki bayani dallah dallah tunda baki saniba,sumayyah ki fita a idona fah,yaronnan banda jarabawar allah ma daya halicci so mai zayyi dake,tun kina yarinya fah yake sonki,kema kina sonshi,amma tunda kika girma kikayi wani bore wai ke adole kin waye kika zuba masa kasa a ido,allah wadaran wayewa kuwa idan haka take"
Ganin surutun hajiya mama bazai karebane yasa sumayyah saurin cewa,
"Shikenan hajiyah mama allah yakawoshi,kafinnan inason zanje shan mai tacan kuma na wuce gidan su maryam"
Har yayunta zasuyi magana hajiya mama tayi saurin cewa,
"Allah ya kaimu,idan kinje ki gaishe da mamarta"
"Toh"
Daga haka wajen yayi shiru bakajin karar komai sai na cokala har suka gama cin abincin kowa ya tafi harkar gabansa.
Shiryawa tayi cikin wani pink din material anyi masa riga da wando sai kuma after dress din itama irinta,sai jewelries suma pink da kuma pouch din wayarta.
(Daga ganidai tanason saka komai iri daya).
Nu far motarta tayi cike da takama kaman dai duniya babu abinda yake damun rayuwarta.
Direct hanyar gidan mai ta nufah tana kakkada kai sakamakon karar sautin kida dayake bugawa a motar tata,layi ta samu a wajen kasancewar anyi albashi kowa yana bukatar ya cika motarsa saboda zirga zirgar aiki.
Wani tsuka ta saka taeda buga wani uban horn ita a dole sai an matsa mata ta wuce,wani bawan allah ne ya bude glass din motarsa tareda cewa,
"Haba baiwar allah ba ke kadaice fah a wajennan ba kike bukatar mai,hasalima ke yanzu kika zo wajen,kiyi hakuri mana kaman kowa har layinki yazo?"
Galla masa harara tayi duk da yayi sa'an babban yayanta,
"Ina ruwanka to damin shishshigi,ko kuma neman cusuwa ce duk,angaya maka ni makahuwace banga mutanen ba,mtswww"
Saurin zuge glass dinsa yayi dama mai duhu ne,saboda gudun cin mutuncinta.
Sun kusa wajen awa daya a wajen amma har sannan sumayyah bata samu damar shan mai ba,iya kuluwa ta kulu,dan ji take kaman tasakawa wajen wuta kowa ya watse,motocin Bayan ta taji nayiwa magana su matsa wani zai shigo,hakanne yasa ta cire earpiece din kunnenta tareda lekowa taga menene.
Wata arniyar motace ta doso wajen tana numfashi kaman bijimin da akayiwa duka,sakin baki mutane akayi ciki kuwa harda sumayyah wacce take ganin kaman a mafarki,dan limited edition din motar da ake talle a tv allah ya kyauta tayi tozali da ita a filin maliki yaumiddini.
Fakawa yayi a bakin wajen da ake zuba man bayan ya wuce kowa ya isa gaban kowa,gashi masu gidan man ma basuyi magana ba bare kuma wanda suke kan layi.
Kashe power motar yayi tareda jefo kafarsa da take cinki wani arnen sneaker na gaban kwatance,yayinda yagama fitowa daga cikin motar sumayyah batasan lokacin da taja numfashi ba tareda hadiyar yawu,kaman taga nama danye haka tayi(kaji mayyah😎).
Jawur yake kaman kankana gashi kirar larabawa,a takaicedai har yafi irin kalar mijin da sumayyah take burin aura.
Hanyar super market din wajen yayi cikin tafiyar takama kaman bazai taka kasa ba.
Cikin rawa jiki sumayyah ta bude motarta da sauri tabi bayansa zuwa cikin super market din kaman robot wanda wani yake control dinsa.
Wawware ido tafarayi a cikin wajen daga baya ta bada ajiyar zuciya lokacin da idon ta yayi mata tozali dashi a can kuryar wajen shikadai a zaune,takawa take a hankali tana nufar sa,tareda share duk wata tantama da take wanzuwa a cikin kanta,duk kuwa da bugawar da zuciyarta takeyi haka ta tunkareshi,burin ta  a wannan lokacin shine isa ga muradin ranta koda kuwa hakan shine zai zama action na karshe daxata kudanar a rayuwarta.
"Hi"
Shine abinda tace cikin sanyin murya,dagowa yayi ya kalleta tareda sakin mata wani murmushi daya kara narkar da zuciyarta fiyeda kallonsa a farko,mayar mata da "hello" yayi cikin sanyin murya tareda nuna mata sit din dayake gabansa da alamar ta zauna.
Rausayar dakai tayi bayan ta zauna tareda cewa,
" i am sumayyah"
"Cool,me I am yazeed"
"Wow fantastic,ya kake "
"Lafiya Kefah,your pretty"
"Really I am fine too"
Dadine yakashe sumayyah lokaci daya ganin suna ta magana kaman wanda suka saba na tsawon lokaci,murmushi yasake yi mata tareda cewa,
"Idan bazaki damuba zan tafi cos an saka min maina tun dazu"
Karyar dakai tayi cikin kunya ganin da takurashi da surutu tana ta arar lokacinsa,
Zabura tayi inda take jin kamar a mafarki lokacin dayace ta bashi numberta.
Cikin sauri ta karanto masa yana sakawa a tasa wayar,yana gama copied ya wuceta da nufin komawa motarsa,har zata ce yabata number sa tayi shiru saboda karta zake dayawa,addu'a tafarayi da rikon allah a zuciyarta allah yadora ta a Kansa ya kirata,kar ya zamo ya manta ma da ita da kuma haduwar da sukayi na mintuna.
Dan gabadaya ya tafi da imanin ta cikin kankanin lokaci batareda yasani ba.
Fasa zuwa gidan su maryam tayi,dan yanda taji zuciyarta tana tsuma bazata iya kallon wata maryam ba a lokacin.
Juyawa tayi ita kadai tana murmushi tareda saka wakar soyayya tanaji,ita a dole sai sannan ta fada soyayya taji mai akeji.
Mamaki hajiya mama tayi da taga sumayyah ta dawo da wuri,gashi sai waka take kaman zaucacciya,sakin baki tayi tana kallonta,ita kuwa ko a jikinta,dan inka tambayeta ma inaga bata san da wanzuwar hajiya mama ba a wajen.
Fadawa tayi kan gado tareda birgima tana dariya,Ita kadai tana sumbatun maganar yazeed,
"Ka hadu my yazeed,wlh karyar mace ta kusheka,irin wannan kyau da kudi haka,ai kawai nayi miji na nuwa sa'a,soon class din zai kara hawa,duk garinnan kowa zai yayi zancen aurena,mutu ka raba nidakai my yazeed"
Kwankwasa kofar dakinta taji anayi hakanne yasata tashi domin taga waye,farouq ta gani dan yah Naseer da kwalakwalan idonsa yana kallonta,daga masa kira tayi tareda tambayar menene,
"Cizoci aji mama ajiya,tana kilanki"
"To naji bagware kace ina zuwa"
Komawa yayi da gudu dan dama ita bakowa ne yake marmarin san rabarta ba saboda hantararta.
Sakkowa tayi tareda zama tana facing hajiya maman,
"Gani mamancy akwai wani abune?"
"U hmm wato saida wani abu kike sakkowa koh,to kije kitchen ki hadawa Ahmad wani abun kin manta ya zaizo wajenki ne?"
Zabura tayi ta tashi tareda buga tsalle tana tura baki,
"Tabdi hajiyah mama,dole saini zan hada masa wani abu,to kar yaci mana,dama nasan kwadayine zai kawoshi ai,maye kawai"
Sauri buge mata baki hajiya mama tayi tareda cewa,
"Ni kike fadawa haka dan bakida kunya,ai kece mayya kam,kuma abune dole saikinyi koda snack neh"
Muhibba ce tayi saurin yin magana wanda shigowarta kenan ta dawo daga gidan Anty Lailah matar Yah Naseer.
"Hajiyah mama kyaleta zanyi kawai,koba komai ni ai kanwarsa ce,allah ya kawoshi da la'asar din"
Harara hajiya mama ta gallah mata tareda cewa,
"Allah ya taimakeki yar iya shege kawai"
Ba kunya kuwa sumayyah ta koma sama dakinta,hannunta rike da bakinta inda hajiya mama ta bugeta,wayar ta dauka da sauri ganin missed call na wata number,saurin bin baya tayi dan zuciyarta yabata yazeed ne,saidai me?.....
Muryar Ahmad taji yana gaisheta cikin nutsuwa,zancen zuwansa yake kara sanar mata,tun kafin yagama yi mata bayani ta katse kiran tareda zefa wayar kan gado ta shige bandaki ita kadai tana tsuka.
Da yamma saida ran hajiya mama ya baci kafin sumayyah ta zumbula riga babu ko powder tayi hanyar guest room inda Muhibba ta sauki Ahmad.
Akan kujera ta ganshi yasha farar shadda wacce takara fito da ainihin bakinsa mai kyau,saidai ga sumayyah wannan yafi komai bata mata rai dashi,zama tayi a can nesa tareda fara danna wayarta.
Ganin bata yimasa sallama bane yasa shi yimata sallamar amma bata amsa ba,kaman bata ganshi a wajen bama,snack din ya dau guda daya tareda kaiwa bakinsa yana cewa,
"Snack dinki yayi dadi sosai,naji Muhibba tace ke kikayimin"
"Hmm tayi maka dai,to karya tayimaka bani nayi ba ita tayi,allah ya sawwake nayi maka girki,tirr har abada hakan bazata faruba,idan kana da abin fada ka fadamin,idan babu kuma zan shiga ciki,ni inada abinyi kaji"
Maganar ta gasa masa rai haka yayi mata murmushi tareda yi mata sallama ya fita batareda yace komai ba.
Harara tabishi dashi tareda komawa cikin gida,
"Narasa yaushe zaka bar rayuwata,ana so dolene,ko jaraba kai haba ni........"
Katsewa tayi ganin bakuwar number tana kiranta,har bazata daga ba sai kuma ta daga,.....muryar da tajine yasata cire duk wani bakin cikin Ahmad a ranta tareda maye gurbinsa da farincikin yazeed.
Dakinta ta koma da sauri tareda bin lafiyar gado tana amsar lallausar muryar yazeed da take kashe mata duk wani bangare na jikinta.
Sun dad'e suna waya har bayan sallahr magariba amma basu katse kiran ba,sunaji ana sallah har aka idar amma hakan bai damesu ba ,dan ji suke kaman rabuwa da juna zai musu wuyah.
A karshen wayarne sumayyah tayiwa yazeed magana akan yaushe zaizo gidansu,shiru yayi daga baya yace,
"Baby karki damu,kinsan ai dole zanzo gidanku,kawai dai komai akwai lokaci ne koh"
"To shikenan habeebee allah ya kaimu"
Kwanci tashi asarar mai rai,lokacin da aka daukarwa sumayyah na ta fito da miji yazo,dan yau kwananta uku kenan da cika wata amma bata cewa abbansu komai ba,shima kuwa zuba mata ido yayi yaga iya gudun ruwanta,dan yau ya shirya tambayarta mijin da ta fitar,in babu kuwa yah bata duk wanda yaga shi yayi masa.

      .........to fah....

🏵🏵*sadi-sakhna*🏵🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now