Page....6...

166 13 2
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

🏵🏵🏵
...6....

Kowa jikinsa yayi sanyi dajin furucin da abbah yayi akan sumayyah,amma haka babu ruwanta kaman an (mintsini kakkausa),saima kade rigarta da tayi tareda wucewa dakinta danyiwa yazeed albishir din abinda abba yace.
Kwata kwata abinda abba yace bai dameta ba,dan ita a wajenta hakanma ya fimata,idan tayu aurenta shikenan ta fita daga rayuwarsu,kowa yaje yayi harkar gabansa kawai.
"Hello baby ina kake ne ina ta kiranka baka dauka ba?"
"Sorry beb ina wani solving business ne,ya akayine naji muryarki kamar mai murna,kaddai kin daina sona kin fara son mijin daxaki aura?"
"Kai habadai,a duniyarnan akwai ranar dazan daina sonka ne,saidai idan bana numfashi,anyway albishirinka...."
"Uhm goro.....amma mai ya farune beb ki fadamin mana"
"Abba ya yadda da auremu dakai,abinda nake fadamaka ma gobe yace kazo a daura mana aure dakai,ai ina fadamaka shawarar daka bani tayi aiki,yanxu haka abinda nake fadamaka gobe i yanzu ina gidanka a matsayin mallakinka"
Wata y'ar kara yazeed yayi a daya bangaren tareda cewa,
"Yessss kai gaskiya naji dadi sosai beb,ashe kedin jaruma ce,dole nayi miki jinjina ashe,finally zamu cika burinmu ashe,duk masu bakinciki saidai su mutu.
"Ai baby inaga nafika jin dadi a yanzu,ni da da'ake shirin yimin aurem dole"
"Hmm mm bakisan yanda nake jinki bane,yanzudai barina je nafadawa abbana halin da ake ciki,gobe inshaallah zamu zo daurin aure"
Da murna da farinciki sumayyah tayi bacci,ganin burinta yana shirin cika a goben.
Da safe kuwa aka fara shirin daurin auren babu abinda ya sanja,saidai zukatan mutanen gida duk babu dadi,kowa yana jimamin irin furucin da abbah yayi,yayinda wasu kuma ta wani bangaren suke tausaya wa sumayyah,ganin yanda sosayya ta makance mata ido bata ganin fari da baki.
Da misalin karfe biyu na ranar juma'a Bayan an idar da sallahr aka daura auren sumayyah Abudulkadir gobir da angonta Yazeed Alh Sulaiman,sannan kuma aka daura auren Maryam Abubakar da kuma Ahmad Muhammad Ahmad.
Haka biki ya juya ba yanda aka faroshiba,inda zukata dama abinda bai zo musu yanda suke so ba,musamman ma Ahmad,dan tun sake yake kwance a daki rike da kirjinsa wanda yake masa barazanar fashewa.
Yayinda sumayyah kuwa zuciyarta cikeda farinciki,harta kagu a zo a kaita dakin mijinnata,dan tasan yana can Yana jiranta.
Har can wajen goman dare amma yan daukar amarya basu zoba,gashi gidan kowa ya watse,dan abban kasawa yayi ya tsare akan babu wanda zai zauna masa a gida,bikin gidansa an gamashi haka,mai son yacigaba da biki to ya tafi can gidan su Ahmad.
Motoci guda biyune sukazo daukar sumayyah domin rakata gidanta,daga wacce Abdurrahim yake ciki sai kuma driver daya tuko hajiya Saratu mamar Yazeed.
Abin yabawa kowa mamaki ganin daga abokinsa said mamarsa,sa'ar su ma daya mutane kowa ya watse,dan haka abin maganar kadan akayi.
Kayan dakinta akaje dauka a shashen abbah,dan dama acan aka sakashi lokacin da'aka yi oder su daga Dubai.
Tarar da kofar akayi a rufe gamm da dan makulli.
Ta shi d'aya hajiya mama ta gano aikin abbane,maganarsa na cewa bashi ba sumayyah ne ta fara aiki,dayake ance uwa uwace,duk da abinda sumayyah tayi na allah wadaine amma saida tausayinta ya darsu a zuciyarta,a ranta tana tausaya mata sosai,duk da kuwa wani bangaren laifinsu ne dasuka nuna mata komai take bukata zata samu tun tana karama.
Dawowa hajiya mama tayi cikin sanyin jiki tareda nufar dakin da sumayyah take ciki.
Samunta tayi harta shirya tasaka kayan daza'a kaita dashi,jijjiga kai tayi kawai tareda zan hannunta zuwa waje inda mahaifiyar yazeed take.
Tafiya suke kaman kurame har suka iso falon kasan,damka hannun sumayyah tayi a cikin na hajiya saratu tareda cewa,
"Allah yabaku zaman lafiya,ina miki fatan alkhairi"
Daga haka ta juya dakin ta da sauri tana boye kokarin boye hawayen dayake shirin jubowa a kan fuskarta,duk kuwa da yanda muryarta ta karye.
Hajiya saratuce tasaka sumayyah a gaba suka fita.
Hanyar wata anguwa suka nufa,wanda akwai dan nisa da gidannasu ganin yanda suka dan dade suna tafiya,ba laifi anguwar tana da kyau sosai,haka ma gidannanta shima yana nasa kyan,gashi ya sha fenti sai kamshin dakin amare yakeyi.
Shigewa sukayi da ita zuwa cikin dakin,wanda babu komai a ciki sai tabarma a shimfide.
Akan tabarmar hajiyah saratu ta zaunar da sumayyah tareda bude mata gyalen dayake kanta.
Kallon dakin sumayyah tafarayi tana kare masa kallo,ran ta yadan baci kadan ganin irin gidan da yazeed ya kawota,a kallon da tayi masa dakuma yanayinsa batayi tsammanin irin wanna karamin gidan zayyi mata ba,amma saboda son da take masa tuni ta ture komai a cikin ranta.
Shiru dukkansu sukayi tsakanin hajiya saratun da sumayyah babu mai cewa komai,dan kwata kwata sumayyah tsintar kanta tayi da kasa sakewa da matar.
Ganin sha daya tana shirin wucewa ne yasa hajiya saratu yiwa sumayyah sallama suka kama hanyar gida ita da Abdurrahim.
Shirun gidan da sanyinsa ne ya sakawa sumayyah wani kadaici a cikin zuciyarta,dunkulewa tayi a waje daya ita kadai,tun tana gyangyadi har takai ga ta mike akan tabarmar bacci yayi awun gaba da ita na gajiya.
****      *****      ****
Tun abinda sumayyah ta fadawa Ahmad a jiya da daddare ya dawo ya shiga dakinsa,babu abinda yake tunawa sai amon muryarta looacin da take zayyano masa maganganu marasa dadi.
Kunnuwansa sun gagara tsyawa da tariyo masa abinda take fada,gashi duk sanda abin yasake maimaituwa sai yaji bugun zuciyarsa ya karu fiyeda yanda bugun zuciya yake a jikin kowanne dan adam mai lafiya.
A cikin wanna halin yakasance har dare ya lullube gari ya kuma sake wayewa wata ranar tasake fitowa.
Duk wainar da aka toya a ranar juma'a Ahmad bashida masaniyar hakan.
Hatta daurin auren sumayyah daya yazeed ma bai saniba,bare kuma amaryar da aka daura masa aure da ita,wato abokiyar masoyiyar tasa.
Kokarin bawa zuciyar sa training yake akan ta rabu da sosayyar sumayyah haka,lokaci yayi dazai fara bawa zuciyarsa hakuri da dangana akan soyayyar sumayyah indai har ya cika cikakken namiji wanda uwarsa ta haifa da jini.
Yana cikin wasiwasinne yaji sallamar Inna a bakin kofar dakinsa,yunkurawa yayi dakyar cikin karfin hali ya bude kofar,sai a sannan ya kulada da duhun da garin yayi,dan tun la'asar yake zaune ko motsin kirki bayayi kaman mutum mutumi.
Kallon dannta take cike da tausayawa kafin tace,
"Babangida yanzu abinda kake kana ganin shine mafita,tun jiya fah da ka dawo naga yanayinka ya sanja,kyaleka kawai nayi domin kasamu lokaci.
Yakamata ka shirya kazo ka tafi gidanka,zaman ka a dakin ya isa haka,dan babu abinda kake karawa kanka sai damuwa dakuma tashin hankali"
"Gidana kuma inna,mai zanje na iyo a can din?"
"Wajen amaryarka zakaje wacce abban mu'azzam ya daura maka aure da ita,dan sumayyah tayi aure bashi yake nufin kai baxakayi ba,dan haka inaso kabawa zuciyarka hakuri,sannan ka rike wacce ya aura maka cikin aminci da amana,ta hakanne zaka godemasa da karamcinsa a gareka.
Ka shirya kazo ka tafi,allah yabaku xaman lafiya da zuri'ah dayyaba"
Daga haka innah ta juya tabar bakin kofar dakinnasa domin bashi damar shiryawar kamar yanda ta umarceshi.
Jikin sanyin jiki tareda bin umarnin mahaifiyartasa yafara shirin tafiya gidannasa,duk da bai so hakan ba amma bashida ikon fadan hakan,dan abinda baya tsallakewa a rayuwarsa shine umarnin innar tasa,abin gudunsa kuwa shine fushinta,zai iya aikata komai matukar zai kasance abinda take some kenan.
Motarsa ya tayar a hankali kafin kama hnayar gidannasa,anguwar tsitt babu kowa saboda dare daya dan fara,ga kuma yanayi na sanyi daya fara shiga.
Har ya wuce kuma ya dawo ya tsaya a bakin wani mai nama ya siya kafin ya wuce dashi.
Sallama yayi a kofar falon amma shiru babu wanda ya amsa,dakin daya hango da wuta a kunne ya nufah tareda turawa a hankali,a zaune yasamu mace ta juya gabanta tana kallon daya bangaren a lullube da hijabi.
Sallama yayi cikin sanyin murya,yayinda maryam itama ta amsa masa a taikace.
Juyowa tayi tareda yaye mayafin dayake kanta tana kallon idon Ahmad din.
Dan razana yayi tareda ja baya kadan,dan daga gani baiyyi tunanin ganinta a matsayin wacce aka aura masa ba.
Murmushi maryam tayi da ganin yanayinnasa,dan tasan dama dole hakan ta faru.
Ajiye mata ledar yayi tareda yi mata sai da safe ya wuce dakinsa,a bangarenta itama bata damu da tafiyarsa ba,tan tasan daga ita har shi suna bukatar lokaci,wanda zasu samu damar amincewa da junansu tukunna.
Kashe wutar dakin tayi itama ta kwanta bayan ta saka naman daya kawo a fridge,da niyyar gobe sai ta sake dumama shi.

***  ***     ***

Cikin dare sumayyah taji kaman ana rabata da kayan dayake jikinta,bata kawo komai a ranta ba,dan a ganinta kaman mafarki nw kawai da mace ko namiji sukeyi idan sun mallaki hankalin kansu matukar suna da lafiya.
Sanyine taji yana ratsa jikinta sakamakon rabata da kayanta da akayi.
Kokarin mannewa take wake daya saboda sanyi,amma saikuma taji an maye sanyin da jiki mai dumi.
Sakin jikinta tayi tana karbar bakon sakon dayake jiyartar ta dukkuwa da cewa tana kokarin tashi,amma zuciyarta takasa fada mata cewa abinda takeji da gaske ne ba mafarki ba.
Zafin daya jiyarci kasanta ne sakamakon shigarta da yazeed yayi cikin karfi yasakata farkawa a gigice tareda kokarin kwace jikinta daga nasa.
Riketa yayi da karfi a waje daya tareda saka mata hannu a baki alamar tayi shiru,daina ihun tayi amma bata daina jan zuciyaba da kuma bada sautin karamar kara akai akai saboda zafin dayake cigaba da shigarta sakamakon aikin da yazeed yakeyi akanta,wanda yi yake da karfi kaman ya samu tsohuwar hannu,ko tausayin bata saba ba bayayi.
Haka sumayyah ta cigaba da shan azaba har baccin wuya ya dauketa lokacin da ta samu yazeed ya sauka akanta.

Shikuwa gogan yana gama karbar abinda yake bukata ya bingire bacci ya debeshi,babu zancen tsarki bare kuma wanka........

*wannan shine abinda muke fama dashi musamman ma ga matasanmu hausawa,zaku ga suna burin aure aure dai,amma burinsu shine karbar budurcin matar a daren farko.
Basa tunanin wane hakkine akansu nata,shin wane irin zama zasuyi,sannan menene ilimi da kuma hakuncen hukuncen zaman aure,duk bashine a gaban su ba,bukatarsu shine su biya bukatarsu.
Sannan uwa uba kwanciya babu tsarki bayan angama ibadar aure,wannan shima abune daya kamata a duba,domin yanada matsaloli dayawa,musamman ma ga lafiyar jiki.
Sannan yana jawo aljanu su shiga jikin mutum,saboda mutum ya kwanta babu kariya a jikinsa sam.
Allah ubangiji yabamu ikon kiyayewa ameen*

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHWhere stories live. Discover now