Page....39...

183 20 9
                                    

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...39....






Tunda akayi auren salma ta tafi garin aurenta kadaici yasake lullube sumayyah fiyeda nada,dan ma busy din karatunta yakaru musamman da suka kusa fara jarrabawa yanzu.
Har yanzu tsakaninta da mai gidan dai jiya iyau,dan gwanda ma yanzu idan ta gaisheshi yana amsawa.
Wani lokacin ma takan zama su zauna suyi hira da maryam,sa9 Ahmad ya dawo tukunna ta tafi dakinta,dan har yanxu ta kula ba sosai yake son ya ganta a inda yakeba,ita kuma tana kokarim kiyaye hakan,dan dama tun kafin ta shigo gidan tayi alkawarin bazata takuwara zamansu ba,saidai idan kokarin shiga nata rayuwar sukayi.
Har yanxu dai bata shiga shirgin abincin gidan saidai wanke wanke wani lokacin idan tana gida takanyi mata.
In kuma karatu ya riketa a dakinta take wuni idan ba makaranta,dan yanzu bakaramin effort tasaka akan karatun ba,bata wada daahi ko kadan.
Shikansa prof saminu yanzu yasan sumayyah ta yunkuro danyin abin katan sosai,shiyasa shima baya gazawa wajen taimaka mata.
Duk da cewa takanyi baya naya dasu saboda mu'amalarta a da dakuma yanxu ba daya bane.
Koda aurene gashinnan kaman ba aureba amma duk da haka hukuncin sa yana kanta,shiyasa takanyi kokarim wajen yin harkarta da mata indai ba waijen bada assignment ba

Koda a bayama tana tantirancinta kam na girman kai sa kuma san sani,sannan ga masifa da raini amma kuma sam kazamar mu'amala da maza ba acikin schedule dinta yakeba,a cewar ta koba hukuncin Allah hakan zubda class ne ba kadan.
Ita kanta idan ta zauna tana tuna yanda mutari ya juyata kaman masa tasan Allah ne kawai yabashi dama saboda abinda ta aikata,dan a nuna mata iyakarta,amma ina mutari ina ita a wajen matsayin yanda take a baya.
Tashi tayi daga kan gadonta ta ajiye wayar ta datake duba wani abu a web,wajen drawer ta taduba inda take ajiye kudi.
Ajiyar zuciya tayi ganin kudin da take takama tana dauka tayi dan lalurinta duk sun kare sauran kadam,da kyar idan ba tayi manage ba sukaita karshen semester.
Lallai hakane da ake zara bata barin dami,tuk tulun dami sai ya kare koda da daddaya ake dauka matukar ba wani ake sakawa ba.
Hannunta tasaka ta murza a cikin kalabar din kanta tareda furzar da iska,zama fah bai kamata ba,musamman da batada abinyi.
A yanda takeji bazata iya tambayar yayunta kudiba dan duk yan rainin hankaline miji kuwa koda ta tambayeshi tozarci zata sha kawai,duk da bazata tabbatar ba,dan kwannan baya daure fuska dan yaganta kaman da.
Amma duk da haka batada karfin halim tunkararsa tambayar kudin,salma kuwa idan sunyi wayah komai normal take cemata,dan bazayyi yiyu ta dunga fada matsalar ta bayan ita ma yanzu da nata gidan.
Zama tayi akan gadon tana karewa jakar kudin kallo.
"Kai ninake damun kaina,tunda bai
Gama karewa ba nasaka dakuwa a raina,idan ya karedin saina san yadda zanyi kawai.
Allah bazai hanani mafita ba ai"
Daga haka ta zefa jakar cikin drawer ta cigaba da abinda takeyi.
Exam dinsu ya matso sosai,sannan kuma ga bikin Muhibba wanda zata auri yayansu Nazeef dan gidan baffah Usman,abin a bazata ya bugi sumayyah dan bata san wainar da ake toyawa ba sai auren kawai taji.
Damuwa ce ta taru tayi mata yawa,ga auren muhibban ga kuma exams sannan gashi dole saita shiga cikin dangi,musamman su anty Maimuna da kowa idan an hadu tasan chapter rayuwarta za'a saka a gaba.mamimakon taje biki taji dadi saidai ta jawa kanta kayan bakin ciki.
Duk da tsakaninta da maryam babu wani tashin hankali amma ama haduwa za'a karawa abin tsanani har sai yafi nada,idan ita bata wargaza auren maryam da Ahmad ba ai masu zugo zasu wargaza a banza.
Lissafi tafara na zuwa bikin da kuma na exams,rashin sa'a sai yazo mata a ranar daurim auren dana wuni dukka tana da paper dazatayi,gaskiya kuma yanda takejin karatunta bazata je wajen bikiba tabar karatun dayake gabanta.
Tasan dole Muhibba tayi fishi da ita amma dole saida tayi hakur,idan tagama jarabawar saitaje har gidanta su sasanta.
Ta wani wajen ma ta huta da zuwa wajen bikin ma,dama ba wani fitaccen kayane da ita yanxu ba,kayan da Ahmad yayi mata na akwati ba a dinke suke ba,kayanta kuwa datake sakawa sun sha jiki,in tace zata cire kudin tayi dinkin sannnan tayi zirga zirgar biki kaff karewa zasuyi tasara yanda zatayi.
Gudun karkowa yagano halin datake yayi mata surutu dole zata bada uzurin makaranta kawai.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now